← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 65

Sashe 45

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

muka fita, Muna barin cikin gidanmu, wata jibgegiyar mota tana rufa mana, kamar zasu bi takanmu Zakari ya matsa musu yana mita, munzo traffic, sai ga wata mota tazo da mugun gudu, zata shege damu. Abin mamaki sai gani mukayi wata babbar tanka tabi ta kanta. Ai ganin haka yasani fasa ihu, tare da kamkame jikina, karan jiniyar yan sanda da fire service, Da sauri nasakai zan fita naga an shigo tare da ture Zakari gefe, akayi baya da motar, zanyi magana dani har zakari aka watsa mana hoda. "Eh kome ya kammala karkashin jagorancin D28 Code 29 grps" Iya abinda na iyaji kenan, sannan wani kafirin barci yayi awon gaba dani. *** Fitowar Dr kenan daga Asibiti, zai shiga motarshi,, sai ji yayi an Duke keyarshi da abu, durkushewa yayi tare da rike keyar, sai ganin mutumin da ya duke shi, ya fa i a kasa, ko shurawa. Sakamakon harbin da aka mishi ta keya har sai da yafito goshinsa, lumshe idanunshi yayi sannnan ya yanki jiki ya fa i a gurin. *** e idanuna nayi a hankali na sauke akan Ummi wacce nake hango acin rai a idanunta, mikewa nayi da hanzari kaina yayi mugun sarawa dole na koma, ina lumshesu nace. "Ummina! Yarana fa?" Wani banzan kallo tayi min cikin matsanancin acinrai tace. "Dk cikin yarana, kece kika fita zakka. Ko yayya na saka doka sai kin rusa min ita, yanzun badan Allah ya kare ba, me kike tunanin zai faru. Wallahi Safinah ki fita a idanuna na rufe." "Don Allah Mariama ki rabu da ita haka, da muka samu duk suna raye barka zamu sannan mu godewa Allah, sai Dr shima ya farfa o Insha Allah, Ubangiji zai shiga tsakaninmu da duk me nufarmu da sharri, yanzun haka munyi magana da Hukumar yan sanda, kuma Allah zai bamu nasara." "Alhaji hankalina bai kwnta ba Ina ganin Safinah ta tattara tabi tafi Oman zatafi samun kariya a can." Shigowar Mataimakin IG, yasata yin shiru, gaisawa sannan yace. "Alhaji Badar! Mun sami labarin kaida iyalinka tare da Dr Katagum ake hari, amma abin mamaki ba maharan bane suka turo mana sakon D28 Code 29Grp" Yacn kaina har ciwo yake, _Domin cancare chakwalkwalin Chakwakiyar zaku iya sheke naira 150 a cikin asusun bankina kaitsaye domin dakon Book 2, idan kuma Katine zaku iya Kumdume katin Mtn na naira 200, Mu kafta saura pages 28 na karkare Book One ga wata Chakwakiyyar ta fashe kune min taku...Karku manta idan transifer in kati Vtu 200 ne idan kuma kaitsaye ne zuwa asusuna na banki 150 ne sayan nagari mai da ku i gida Arashin araha ake barin tayi, koda ku inka sai da rabonka abin dace ne an fari ya mutu idan kun shirya naji motsinku daga marubuciyarku wacce bata san raggonci ko lalace ba ullum suburbu eku take da labarai sinki sinki_ Oum Muwaddah...... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITER'S ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* *_Labarin daban yake da sauran._* _Kun gane Nufina kuwa? Book One free ne daga page 1 to 60, Book 2 zuwa inda zan tsaya na ku ine wai ina gaya muku ne ku shirya tsaf_ Page. Zaro idanu nayi waje, tare da kifkifitawa, nace. "Ummi ina yarana?" Bu e min bakina tayi cike da jin haushi matar da tun da tahaifeni ban ta a jin tayi zagi koda Qaniyarki bata ta a fa a a gabana, sai yau wai itace ke ce min. "Suna gidan Qaniyarki" Zaro idanu mukayi hatta Abba sai da ya kalleta anya ita kuwa. "Ummi zagi kikayi fa!" inji Khalil, juyawa tayi a fusace tace. "Qaniyarka zan fasa muku kai, haba jama'a ke aya kin addabi rayuwar kowa, Haba don Allah Safinah anya kina son ganin dai-dai a rayuwarki kuwa, ke ko damuwa da rayuwar yaranki bakyayi, toh idan Sajidah ta mutu sai ki san yaren da zaki gaya Ubanta da Kakarta, ina ga baki san ina kika saka kanki ba." Mikewa nayi tare da dirowa a gadon, jikina na rawa. Fita nayi da gudu, ni kaina bansan inda zani ba, dan su Abba sun biyo ni da sauri mukayi karo da Dudu, rike hannuna yayi na fashe da kuka, tare da fa awa jikinshi nace. "Dudu! Aanih! zasu kashe min Yarinya bansan me zancewa Abie insu ba." Riko hannun yayi muka nufi akin da aka kwantar dasu, tana kwance tare sa yar uwanta, ita tana barcin wahala. Wani mahaukacin soyayyarsu ce ta daki zuciyata na kura mata ido, sai yanzun na lura da bata kai Aamih haske ba, tana a haske amma me duh. Dan idan ka cika saka ido zaka ga fatarta har wani sheki yake, yayinda Aanih kuma tafita haske sosai dan itace Ashraf a fuska, amma a zahiri Aanih ta fita hakuri. Sumbatar kumatunta nayi ruwan kwalla ya sauka a fuskarta motsi tayi, tare da sake yar kara irinta wahala. Kamar ance d'ago kai, har e hannunshi yayi a kirji. Kanshi yasha bandeji murmushi ya sake min. Na kauda kaina tare da mai dasu kan yaran, haka kawai nake jin wani abu na fisgana, wani irin yanayi nake ji akanshi. A sannu nasake satar kallonshi, gira ya d'age min tare da kashe min ido, kunya ya bani na kauda kaina. Ina murmushi asa asa, Har inda nake ya iso yana kallon yadda nake shafa kan Aanih, ina kuma jin idanunshi na yawo a jikina, lokaci guda ya saukar mun da mugun kunyarshi tare da ganin tulin girmanshi da ya cika min ido. Hannunshi yakai zai auki Aamih, hannunmu ya ha u da juna. D'ago ai mukayi a tare muka kurawa juna ido, janye idanuna nayi daga gare, mai dashi nayi kan Aanih da take barci. "Ina jin bakon yanayi a tsayuwarmu na yau idan kika bani dama." Gyara kwanciyar yarinyar nayi na ra e gefenshi zan bar d'akin, sai ji nayi ya riko hannuna. Tsigar jikina ne ya mike sabida ban ta a shiga irin wannan yanayin ba sai yau. Duk abinda Anim yayi wasu abubuwa a tare dani ban tab'a jin kome a game dasu ba, kai ko Ashraf da shi na fara sani a duniyata ban ji kome ba, ina jin kewarshi na kata'i sabida halayarshi da suka min, ina son halayarshi fiye da kome. Dawo dani yayi gabanshi, ya zuba min ido cikin sanyin murya yace. "Zan iya hakuri har ki yayyesu, amma bazan jure shirunki ba. Am 45 now na rabu da Aieesha, pls ki taimaki gwauro irina ki bashi gurbin." Dakyar na had'iye yawun bakina cikin inda inda nace. "Abban Adil! Ina son fita." "Zama da Sultan ya maida ki miskila irinsa ko? Ga sona a cikin idanunki but kina pretender kamar baki jin kome a kaina, ki bani dama na karshe rayuwata dake." Ga baki aya na gaza furta kome domin bansan wani irin yana i nake ji ba, sake hannuna yayi sannan ya kwantar da jaririyar, addu'a yayi musu. Sannan yasani a gaba har bakin kofar da aka kwantar dani. "Safinatu!!! Zan baki dama daga nan har ki yaye yaranki, don Allah karki cutar da zuciyata." Jikina ne yayi mugun sanyi, sunkuyar da kaina nayi ina wasa da farcena wanda ban jima da musu lalle ba. "Ina son mace me lalle! Haka yana kara mata martaba da kima." Takowa yayi har gabana, dukda mutanen da suke kaiwa da komowa, bai hanashi sauke nauyin dake cikin zuciyarshi ba. "Safinatu! Ki bani amanar kanki da rayuwarki, Insha Allah bazan baki kunya ba." *Wayyo Allah na ashe haka mace take ji idan tasame me sonta ji nake nafi kowacce mace sa'a.* 'agowa na i da niyyar ce wani abu ina ha 'a ido dashi sai naji bazan iya ba, haka nayita motsa bakina. Karshe na juya da sauri na shige akin, na rufe kofar tare da sauke wata ajiyar zuciya. "Wannan mutumin zai kashe ni da salonshi, mutum sai kace majnun" "Didi ke kuma Lailah, eyye Our didi falling in love" Ware idanu nayi dan ban tsamaci yan butan uwa suna cikin akin ba, take na bone fuska. "Toh Didi! Idan babansu Aamih yazo ya zaki yi?" inji Batul, Wani tsuke fuska nayi, cikin acin rai nace. "Kinga nayi miki kalar matar yaro? Ai Ashraf saike Batul ni nafi karfin Yaro karami." Bakinsu a sake suke kallona, cike da mamaki, fahimtar abinda yake yawo a zuciyarsu ya sani fara kame kame, Ummi tana kallonmu bata ce cikanku ba, sai dai da alamu bata ji da in furucina ba. Dukda na jefa musu kokwanto haka suka share batun amma tabbas suna nazartan Alamarin fiye da tunanina, karshe ina zaune bayan tafiyarsu Ummi tare da jagorancin yan sanda. Karshe gidanmu sai da aka saka mana yan sanda. "Didi!" d'ago ido nayi na kalleta, dake ina chatt da Dr. "Dama da naji kince Abie insu Aanih Yarone sai ni! Am sorry da tambayar da zan miki, kuma wallahi ba cin fuska bane, kince yaro taya." Tsuru tsuru tayi tana kallona jikinta na ari. Saukowa nayi daga gadon na mikar da ita, sannan na bata labarin abinda ya faru. Kuka sosai tayu tare da bani hakuri, tace. "Bai kyauta ba"
Chapter 45 · 0% Book details