← Book details Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 65

Sashe 40

Masarautar Jordan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tura baki tayi sannan tace. "Plss zan aura akan Dp ina," Hararar ta ya i sannan ya fito daga ciki ta biyo bayanshi, tana murmushi tace. "Abban twins!" Murmushi yayi ya tsaya, "Plss" Mika mata wayarshi yayi ya barta ta koma, wani abinda ummi tayi ya kara ha e kanmu ba kome bane sai cusa mana soyayyar junarmu, idan abu yasamu mutum aya kama ya samu saurane, duk wani dabi'a irinta sako da sako du bamu dashi, sam yadda take da sanyi hali haka muma mu asance dan ita har wasu nace mata baci suna maryam ba, amma ko yayya ne mu dai muna son Uwarmu haka, dan tayi na mijin kokarin ganin mu tashi da tarbiya, akasin kaddara da ya fa a min ne kawai zan iya ce wani abu. D'akin ya dawo yasame Umma tana son komawa gida, Ummi da Sophia tare da Nanah suna nan, Abdul ya dawo da Umma ya kuma kwasosu Batul ya kawosu. Zuba min ido Khalil yayi sannan ya dubi Ummi yace. "Allah yasa karshen matsalarta kenan" "Amin" duk akin suka amsa, "Toh Ummi ina yaran suke?" Inji Khalilah, mika mata wayar Nanah. "Duba gallary," Da sauri ta amsa, har suna rigayen kar a, duba gallaryn tayi sai ga hotunan yaran, "Masha Allah! Haka yaran suke da kyau," Aikuwa Khalil ya amshi wayar ya shiga bin hotunar yaran, sai murmushi yake sakewa. "Ummina Didinmu ce ta haife su, masha Allah bari na aura a Tweet.." "Sai kasan amsar da zaka bawa Babansu dan Dudu ya hanani." Inji Nanah, "Ahtoh na hakura, tunda yace kar asaka." Duk wannan yana cikin tsarin tarbiyan Umminmu domin idan babba yace kar ayi abu toh karami bai isa yayi ba, kuma koda laifi karami yayi bata ta a kallonshi zata barshi da yayunsa su masa fa a, sannan itama ta aura da nasiharta, tunda Ummi ta haifeni har na girma Ummi bata ta a dukana ba, sai tsawa shi yasa lokacin danaje jordan nasha wuyar jibgar sa suka min. Basu bar Asibitin ba sai dare, aka bar Ummi, bayan tafiyarsu Dr HZ. Katagum ya shigo duba ni, sam Ummi bata san shine yayita hidima ba, cikin mutunta juna suka gaisa sannan. Ya kama abinda ya kawo shi yana gamawa yafita, ita kuma ta cigaba da laziminta. *** Washi gari dakin ya kuma cika da yan uwana. Da mutanen arziki tun safe Abdul ya kira Nannah ya gaya mata haihuwar. Tsabar murna kamar tafito ta wayar. Karfe biyar na yammacin ranar na farka, a sannu abubuwan da suka faru ya dawo min, lumshe idanuna nayi tare da fashewa da kuka. Kukan nawa ya sanar musu farkawata, Batul ce ta fita. Taje ta kira likita. Can sai gasu tare da Dr Katagum, yana shiga yace. "Ku ha a min tea! Sannan ku an bamu guri, amma Mama karta fita ta tsaya dan taimaka min." Duk suka fita, shi da Ummi aka bari. Ya auko auduga tare da wani almakashin aukar auduga, ya kar i wani kofi. Da kanshi yakawo kwanon silve ya mikawa Ummi sannan ya umarce ni na bu e bakina, ina ji ina gani ya wanke harshen tass, sannan ya kalle yadda nake kuka sosai,ta e baki ya i cikin gatsali dan matsalarshi bai iya magana ba. Yace "Yanzun an wannan abin kikewa kuka, kika iya haihuwa sai wanke baki ne kike zubda hawayenki, toh ai sai ki aura ammara dan yanzun zaki sha hot tea." D'ago idanu nayi tare da kallonshi. Kar an tea in ya i sannan ya kur a, kana ya mika min. "Ki godewa Allah da yabaki Jarumar Uwa! Inda nine da zafi zakisha, dan haka zuwa an jima zan dawo ki adana hawayenki" Yana gamawa ya juya ga Ummi yace. "Sannu Mama! Zaku iya amso mata yaran ta fara shayar dasu." "Toh mun gode sosai," tace masa, har zai fita tace. "Don Allah kaine Dr Katagum!" Cike da jin kunya ya gya a kanshi. "Mungode sosai, da Hidima Allah yasaka da alkhairi." "Amin, Mama!" yace sannan yabar akin, da kallo nabishi sannan na kalle Ummi ina jiran karin bayani, kar an tea in tayi. Taje ban aki ta ha a min ruwan zafi sannan ta fito ta riko hannuna muka shiga ciki, Lallai na yarda Ummi Jarumar Uwa ce, ita da kanta tamin wanka tass bayan ta gasa min jikina yadda ya dace, sannan ta fito tace. "Ki wanke jikinki kuma kisa ruwan zafi a gurin, banda shirme dan matu ar baki gyara gurin ba kece a ruwa. Babu abinda ya dame ni." Murmushi nayi a raina nace. *Ummi kece kuwa me shiga damuwa* Wanka sosai na i sannan na fito, riga da zani ta bani na saka, bakina ya i nauyi, dan haka bana magana sabida harshena. Zama na i sai gasu da yaran, tea in na kar a ina sha tare da matse kwalla, ina gamawa ta mika min magani nasha, sannan ta shafa mun bonjula, akan harshena, ina gamawa tana samin yarinyar farko a an cinyata, d'ago kaina nayi na kalleta, murmushi tayi sannan tace. "Idan da duniya zasu ha u domin dakatar dake alokacin, tabbas rabonsu zan iya kashe mutumin da ya nemi dakatar dasu, Safinah rabon y'ace nada zafi tafi kowacce halitta zafin, Kuma ki duba da kyau yara biyu, ki godewa Allah da ina raye haka ta faru, da bana raye ko kuma Dudunki ba me kula bane, nayi imani da Allah mutuwa zakiyi, tunda kika ga sunzo toh ke baki isa dakatar dasu ba.Allah ya albarkaci rayuwarku dake dasuma." Kuka nake sosai, ina kallon yaran, nama rasa me zance dan nayi kuskure a rayuwata, nice Babba kuma nice na fara zubda mutuncin gidanmu, ribar taurin kai har da shegu. Dafe goshina na i sakamakon sara min da yake Ummi tayi maza ta riko babyn. Kallon Ummi nayi ina girgiza kaina nace. "Ummina! Ni bazan shayardasu ba, kawai a shayar dasu Madar." Make min bakina ta i cikin wani irin acin rai, wanda ban ta a sanin tana dashi ba, ta kuma aga hannu zata mare ni, haka ta kasa marin, saukewa ta i ranta yana tafasa, ta dire min jaririyar ta auki hijab inta tace. "Nagode." Tasa kai zata fita, Khalil yace. "Ummi! Ke da kika haifemu kikayi fushi da alamarinmu ina kuma wani na daban, Ummi idan kikayi fushi da ita bazata ga daidai ba, don Allah kiyi hakuri Didi bazata kuma ba." Kallona ya i cikin jin haushi amma yayi kokarin haka yace. "Didi baki kyauta ba auketa ki bata abincinta ba a shayarwa ke aka shayardake," "Ibrahim sheg..." "Ke kan wallahi baki da hankali." Inji Umma da tashigo ganin Ummi a tsaye yasa tsayawa a gun, gashi taji abinda Khalil ya fa a min, uwa Uba kato arar da na i. Hmm bakin ciki yasa Ummi barin asibitin, ba ita a ba hatta yan uwana, dan Alakatafur naki bawa yaran nono, har Abdul sai da yaji haushina. Maida yaran akayi ni kuwa na cigaba da kuka na, Umma ka ai aka bari. Muna zaune sai ga Dr Katagum ya shigo da yaran yana auke da daya, nurse tana auke da aya.. Yana zuwa ya ja kujera ya zauna sannan yace min. "Maza basu nono." D'agowa nayi a tsiwa ce, muna ha a ido naga ya cika min ido, dole na sunkuyar da kaina, na bu e rigar na rasa ya zanyi da babyn, nurse yayiwa magana, sannan ya juya gun Umma da take min fa a da harshen shuwa, tana gamawa, ta shiga masa godiya. Nuna min yadda zan bawa babyn nono tayi, sannan ta ajiye min ayar, ta fita. Babyn tana kama nono na lumshe idanu, sabida zafi. Haka mukayita dambe da Babyn sannan ya amsheta ya sakata a kafa arsa, sannan yanuna min ayar. Na auka fita Umma tayi dan ana kiranta a wayarta bata ji. Tana fita sai bumm muka ji kamar an wurgo shi akin, 'ago kaina nayi, bansan lokacin da yawu ya sarke min ba, tari na fara. Dr Katagum ya mike yazo ya amshi yarinyar ya kwantar da ita, sannan ya zuba min ruwa a kofi na zafi sannan ya auki na goran faro ya zuba min, tare da mika min, da sauri na amsa. Takowa Anim yayi yazo ya kalle yaran, cikin mugunta yace. "Sannu uwar yan biyu, riba har da uwar ku i kenan." Rike rigar Dr nayi ina girgiza kaina, kallon Anim yayi ciki mamaki yadda yake murmushi. Gashi yana kokari ta a yaran, cikin kuka nace. "Karka barshi ya ta a min su!" Aikuwa ya rike hannunshi, tare da maidashi baya, dariya Anim yayi.. "Kice anan ma kin kuma samun abo in tayi, toh su yaran ubanansu nawane haka?" Kuka ne ya ci karfina sosai. "Wai Anim me yasa kake son cin mutuncina ne, laifin me na maka ne da zafi,me na tare maka a rayuwar duniya? Nayi danasanin saninka a rayuwata, kuma Ubangiji sai yayo min sakayya." "Dalla rufa min baki, meye kika min, bayan kin lalata min nawa rayuwa, kika je kika kwaso wasu shegu a rayuwarmu." "Yarana ba shegu bane, domin sa Ubansu sai dai kaine dai basu ba." "Keee! Ni kika zaga?" cikin kwarin gwiwa nace. "Eh in na zageka." Dukda ciwon dake harshena bai hanani kare mutuncina ba, kaina yayo zai dake ni, Dr Katagum ya dakatar dashi ta hanyar mai dashi baya. "Dalla malam matsa min, dakai ba kaine aka yaudara ba, ka tmbayeta abinda ta min, da sadakina taje wank katon iska ya lalata min tanadina," Dafe goshina nayi hawaye na zuba wannan na oran wanan. Dr yace. "Shin wani irin tanadi aka lalata maka?" "Bada mutuncinta na ace da tayi shine tanadina." Murmushi Dr yayi sannan yace. "Kenan dama ba ita kake so ba, Budurcinta ake hari, da zaka samu a waje bazaka ta a damuwa da taje gidanka ba, ko kuma kana aurenta kaji yadda take ana kwana biyu zaka saketa ko?" *Wacce amsa Anim zai bada???* Oum Muwaddah...... [2/5, 7:51 PM] +237 6 72 92 59 08: _HAZA A WRITER'S ASSO_ *_MASARAUTAR JORDAN!!!_* _Jordan Historical_ 2020* *BOOK ONE* *_Labarin daban yake da sauran._* Page. Wuri-wuri Anim yayi da idanunshi zuciyarshi tana wani irin buga, kankance idanunshi yayi ranshi na kara aci. A fusace yace. "Kai waye? Da zaka sani a gaba da tambayoyi!
Chapter 40 · 0% Book details