← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 108

Sashe 85

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Babu imani matayen suka haura zasu kamata jud ta sake tsala ihu tana kai masu hannu ta ko ina tana kiran aliyu kamar ranta zai fice

Arikice ya shigo gidan dan tun daga falon farko yakejin ihun ta da surutun su..

ma'aikatan gidan kowa ya futo yayi tsege tsege cikin damuwa,aliyu yana banke kofar ya same su sun kamo ta sun mata muguwar kamun ina za'a saka ga ramat da dorina a hannu tana huci,a firgice cikin tsawa yace what? subahanallah,mena ke gani anan,sunajin muryan sa suka sake ta,a firgice ta wawuso gudu cikin ihu ta fada jikin sa ta tsala masa ihun dayaji har tsakar kansa

A mugun fusace Yace get out..ku bace min agida na nace..marasa kunyar banza..yan iska,sum sum suka fara fita ji yake kamar zai yi amon wuta tsabar zafin da kirjin sa ta keyi

Tattaba jud yake a birkice yana tanbayarta tana ta rusa kuka duk jikin ta na kyarma

Ramat dake jin kanta kamar zata mutu tayi saurin tare kofa tace ina zakuce,ai bamu gama yau sai na kashe yar munafuka a gida na,a hatsale aliyu ya ture jud ajikin sa tun kafun ya waigo matayen suka ture ramat a tsorace sukayi waje,a mugun zafafe muryan sa har na rawa yace security,security,ganin ransa yayi mugun baci yasa bilkisu ma ta bi bayan su ta fice,security suna isowa ya hausu da dirin masifa yace in aka bar matayen nan suka kwana lapya bai yafe ba,cikin su yana rawa suka fuce sukayi arresting din su kaf aka fita da su

Ramat tasa mai ihu ta daka tsallen mahaukata tace macuci azallumi mayaudari, waima me xakayi?akan wannan karuwar zaka walakanta min kawaye na, tace tabbb bura uban can aliyu kawaye na zaka daure?.. aliyu,ko kulata baiyi ba,ya nufi inda jud take xai riko ta ya rarrashe ta a haukace ramat ta raruko aguje ta sha gaban sa,baka isa ba,ai abunda kanema kenan kuma yanzu ka soma gani maci amana mayaudari kawai,me zakaji ajikin wannan yar cikin kan in ba dan kaso ka wulakan ta ni ba

Se na kashe ta da azaba wallhy,sena kashe ki ta juya a haukace zata dungure jud shikann sa aliu baisan yadda akayi ya kifa mata wani zindikin mari ba,ta dago jajayen idanun ta zata yi masa magana ya sake daura mata wani kakkakrfan marin dayayi karar tassss saida waje ya dau wani shiru

Ramat ta dauke ji sakamakon toshewar da kunnen ta yayi kwakwalta ne ya dakata daga aikin sa na kai sako wani dishi dishi take kallon sa, ransa a matukar bace ya bankade ta ya dauko jud ya maidata kan gadon ya rungumota jikin sa sosai yanaji kamar ransa aka taba

Da wata kakkaurar tsaki ramat ta dauke kanta akan su Cikin wata iriyar slow motion me fallasa zafi da kunan rai ta ce Aliyu ka mare ni?

Bai amsa ba ta dada harzuka Xata sa masa ihu,dan har tayi tsallen bori da alaman zata hau fashe fashe da sauri ya sake jud ya damko hannun ta a walakance sukayi waje tare da ita,ihu takeyi tana zage zage sena kashe ki da azaba,na rantse da Allah gawarki za afutar agidan nan
Munafuka yar munafukai damgun karuwai makwadaita

Wani shiru gidan ya dauka tsaban tashin hankali

Aliyu Yana shiga site din ya ya wurga ta a floor a tsakiyar dakin ta yana me fetsar da numfashin sa ,da gudu ta taso a haukace ta shake gaban rigar sa,tasa ihun bala'u tana zage zage,inka isa kafita a dakin nan shegiya aka haifeni
Macuci marar adalci Allah ya isa tsakanina dakai aliyu,sai naci bura uban yar makwaidata se ta gwammaci mutuwar ta da zama dani,ransa yay koluluwar baci huci yake yana kallon ta da mahaukatan jajenyen idannun sa

Kamu daya yay ma hannun nata a wuyar sa ya watsar
Xata sake kamasa ya kifa mata mari

A matukar tsawace yace
"Keeee...ki nitsu

"Baki da hankali ne?are u mad..wani rawa takeyi karkar hawayen zafin kishi sun gama wanke idanun ta,ta kalle sa tace aliy..u yace dont u dare call my name,ashe ke mahauckaciyace ban sani,whats all these zaki tara mun mata yan iska kina mun zage xage a gida na, kashe ta zakuyi?yarki ce ko baiwa na kawo maki

Tace bansani ba,aikai zakayi bayanin wacce ka kawo min dan ni bansan ta,kuma wallhy da bakar azaba xata bar gidan ka.

Yace ohhh baki san ta bako?to jud abbakar ce yar gidan hamida aminiyarki,frm now on kisa cewa she is ma wife kishiyar ki...

Yanke kukan tayi cak,wani Dariyar mahaukata ta fashe masa da shi tace" Aliyu yar cikin hamida yanzu bakaji kunyar furta wannan kalaman ba?

aliyu ka cuce ni,se ta fashe da kuka me tsananin kara..Allah ya isa mun,dama tuntini nasan ka tsane ni ba zaman Allah kakeyi da ni ba baka daukeni komai ba In ba dan ka shirya kuntatamin ba ai baxaka saye kan hamida da kudi dan ta juya mun baya ba

Yace whaeva,naga zan iya ne..kudi ina dasu abanza,auren yarinyar ba haramun bane,koda dukan dukiyata nasa na siya kan uwarta da shi babu ruwanki, so nake in mallake ta kuma soyayya kadai ke kawo hakan..and dont push me to d wall

Ta rarumo aljihun rigar sa muryan ta ns rawa tace ehh lallai ma butulu,katon banza kawai..yoo nawa ka bada hamidar kafadamin mana inba tsoro ba,ni zan ruba mata a kunce auren nan dan wallahy bazan zauna da yar ciki na agidan nan
Ba xaka kwanta dani ka kwanta da yar ciki na,kai waye haka da zaka walakanta ni,wato dangin ka da suke kankartar dani bai isheka ba shine kaima xaka goya musu baya ko

To wallhy Dakai da hamida sekunyi dana sanin auren nan,baka dauremun kawaye na ba?sai ka shirya daureni nima,wallahy duka kam yanzu ta fara shan shi a hannu na...sena karya mata kafa da hannu sena makantar da ita

bata hankara ba taji an finciko ta an mata wani irin matsa wani wawan hadiyar yawu tayi,yace inkika sake dukan ta abakin auren ki ramla,tace what?a tsawace yace u heard me.. ko bakin gyalen ta kika taba ban yafe miki ba duk ranan da kika sake dukan ta wallhy sena sakeki,and u better relax now or park ur things and leave..

" cikin muguwar raxana da kaduwa Tace what?a daskare take kallon sa se taga kamar ba shi ba,he sound damn serious ransa a matukar bace yayi maganan

A...aaliyu..kace mene?ni ramla in barmaka gidan ka.
Aliyu walakanta ni zakayi,duk akan auren?..oh na manta ka hade kai da makirai munafukai wanda basa son ganin cigaba na,no wonder dan na zauna a estate dinka a saudia kasa aka kwace,Baka ga rashn adalcin da kake min ba ko?koni ba mutum bace,amanata kaci,ka siya kan kawata da kudi, ka raba ni da hamida,aliyu yar cikin ka auro min,auren ma baka sanar dani ba.wayannan duk ba zalunci bane aliyu

Yace eh in hakane zalunci awajen ki save it..
Ramla ni bansan me zan miki ba
Tun kan kibar gidan nan nake shan axaba wajen ki
Kin tafi harkan ki watannin ki fiye da biyar,... five gud months ramla,what do u xpect?na zauna maki...koni ba namiji bane,ce miki akayi babu jini ajiki na?

Azafafe Tace amma aiba yar hamida ce maganin matsalr ka ba...ai Ba yar cikin ka zaka auromin ba,in abbakar ne ya haife jud, ai kai sa'ar abbakr ne,mesa zaka tozarta ni haka aliyu meyasa..

Yace bcos ure not sorry for what u put me tru,tunda kina iko dakanki,nima ina da iko da kaina,kuma ita nagani nake so,in kece kika haifeta nagani ina so,in Allah bai haramta min ba sena aureta, am not a fool.. dont u dare take me as one..kibar haukan nan naki ku zauna lpya ko wallahy kiyi dana sanin sanina a rayuwaki,in har zan bada kudi in mallaketa to kisani babu abunda bazan iya yi in kika bata min raina ba..

Zatayi magana
Bai jira ba ya fizge jikin sa yayi waje

A guje ta biyo bayan sa,tana xage zage tana cewa seta rama,seta walakan ta shi,baxai taba samun kwanciyar hankali ba seta kashe jud,yaki ya kulata ta gama haukar ta ta fada kasa a falon gidan tana rusa kuka

Kukan takaicin kanta,tace kash kaico ai da ta san akan gindi ne kawai zesa aliyu ya kara mata aure wallahy da ta biye ma hamida tana dawowa time to time tana bashi

Duk a tunanin ta shege na nan,ai zaina taimaka mata akan asirin data mammasa

Little did she knw that,mu'amalar sa da inna yana daya daga cikun abunda ya sakwarkwata karfin sihirin ta ajikin sa,dan sosai ake sadaka da saukar qu'ani da al'qunut a sabun masallacin almajirn daya gina musu kafin ya aure jud, to shikan sa baima san ana wani abu makamancin haka domin sa ba.

Shidai kawai ya bari a auren jud ne ya sauya masa komai
Dakin sa ya nufa ya calming kansa dan yana da zuciya sosai Kafin ya fito yaga shol babu jud agidan yana kira layin ta ya tsinci wayar akasa shikadai yana kara

Wani sabon tashin hnkali da tsoro ne suka rufe sa nan da nan ya bude bathrum ya duba shiru yana bude wadrobe yaga kayanta cif cif,yace to ina take?atake kansa ya soma bugawa kirjin sa ta hau barin wuta tana masa wani irin zafi

Tuno da fatima yayi kawai yaji kamar kafafun sa baxasu dauke sa ba,a daddafe ya sulale kasa, sanda yay tsugunon minti talati sannan ya fice ya same ramat tana kan bori,yace mata ina jud take?ta masa shiru tana watsa masa harara ya daka mata tsawa a birkice itama a tsawace ta mike tace ban sani ba,ni banganta ba kuma kar ka sake tambayana ita,...kamar xai fashe ya kalle ta baice uffan ba ya shiga xaga gidan yana kiran sunan ta
Kowa yace bai ganta ba,kansa ya rike cikin tsananin fargaba yana furta innaliahi wa inna ilaihi rajiun,..

Ramat tana lura da hakan tayi sauri ta haura site din ta,tana ta zagaye ita days ta rasa waxata kira suyi murnan batan tan tare,duk dama bata san ina jud din take ba.

Ta sa key ta kulle kofarta bata fito ba sai can karfe uku na dare ta samu wai aliyu baya nan,tun daxun ya wuce neman jud acikin dare.
Chapter 85 · 0% Book details