← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 60 OF 108

Sashe 60

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daurewa yyi ya zauna da kyau,kamar me shirin tono asirin kansa yace umma umma dama,ina so ne in sanar dake wani abu game da yarinyar,cikin dakewa da nuna kamar bata san waye ba tace wace yarinya kuma?yace jud..tace oh what abt her now?yace mama dama na dade ina son muyi maganar bansan ya zaki dauke sa ba,shiyasaa nace tunda tazo nan har kinganta da idonki ko zan iya neman shawaranki akanta?..

Tace shawara akan me fa?

Yace uhmmm mumma dama aure nake so..Kuma... kuma..nace jud din nake so in aura,.me kikace?

Tace aure aliyu?da yar abokin ka?yaushe wannan yafara?Tun kan ya amsa tace
Ohh wow finally

Se ta maida bayan ta tana me jingineshi da kujera cikin sauraran sa sanda shirun kusan 10ya gifta tace
and isshe aware?ko kai kake so ka cusa mata kaga yarinya karama?u want to kill this beutiful angel like ur other wifes ko,zaka kaita ma wancan mayyar matarkan ta cinye ta?

"Yace i swear not,baxan tabayin haka ba..mama jud tana so and i feel the same.kawai banfada miki bane savida kinga yanayin abun,her dad is ma friend kuma mahaifiyarta aminiyar ramla ce

Jin an ambato ramla hjy ta fusata tace and so what?ai sai suyita kawancen su,in har anbaka yarinya babu abunda zai hanamu daura aure...ko haramun ne?.ya.girgixai yace ah'a..im just nevours bana son hakan ya zo ya tada fitinan da zai daga mata hankli,so mumy ina fatan zaku bani goyon baya na aure ta,tace why not?
Yace but this time arnd inada abunda nake shiryawa zanso ne ayi auren cikin sirri pls

Cikiin zaro ido Hjy tace mene?sabida kai kaci zamanin ka xakace ayi mata auren sirri?Ka kawo maganan arziki but Dont u dare anoy me aliyu.

Ai da ubanka ne baka tsayawa kana kwana haka da har yar hirarku ta masoya sai ka bashi labari ..

But i still wanna be sure nima se na bincika naga intana sonka,then i wll tell u my plans ai nima inada plan din

Yy murmushi Yace hmmm mama na kenan ok but u just have to support
Me,be by ma side
Mama,kince da abba ne zan gaya masa kema gashi nafada miki,i really like the girl,zanso ta kasance matata ta

"Hjy binta tace
Pls it shud be In few weeks time,i beg u,dadin karin Zimman dawowata gida i cant wait to see that day,

Ta mike tsaye cikin zakuwa..zanje ciki in sameta,tura ma kawunnan ka sako ka fada musu nanda sati biyu zanxo musu da magananr auren ka

Baiyi mata musu ba yace yes ma.

Nan ta wuce ta barshi anan ta nufi cikin gida,wani sauri me tafe da murna take kamar wacce aka ma albishir da aljanna?,tana bude kofar dakin ta ta maida kofa ta rufe lumshe ido tayi cikin jan numfashi tana tanbayar kanta how cud i hv not see
Ya akayi bata dago abun da wuri?

Wow wow wow,masha Allah tubarkalla,ta dage hannun ta bibiyu sama da seriuos emotional tune tace ya Allah na gode maka,adede lokacin dana karaya game da aure a rayuwan dana,kanunamin lokaci bai kare min ba,ka dada nunamin da cewa albarkan ka tabbataciya ne,sannan kowani tsanani na tare da warawaka.

Nasan ba karfi na ba da dubara na ba,ya ubngiji na,"cikin sarkafewar murya ta rusuna kasa,da cikakken ihsni tamkar agaban sa take,tace ka sa wannan neman aure ya bambanta da kowanne samun aure arayuwan dana aliyu,ka dabbaka alherin dake ciki ka kore sharrin dake ciki,Allah,kasa yarinyar nan ta xamto sanadiyyar dabbaka zuria dayyaba arayuwar dana.

Hakan ta cigabafa adua cikin yaqini dan tun bayan mutuwar fatima ta cire abun aranta shuyasa all this while bata masa maganan kowa ba,amma tunda yau shiyaje ya kyallaro yace gashi,gani take me hana yuwar auren nan se lillahi dakansa,ko in ita yarinyar tace bata so! ..

Tuno da hakan yasa ta fada cikin tunanin yadda zata gane gaskiyar maganan ta fannin jud,dan ta lura yarinyar akwai kunya,gata dai yar zamani cas cas amma she daubt ko in taje nata da maganan auren nasu zata ita bata cikakkun amsa

Duk da tunanin hakan datayi bata fasa ba,sede ba atake taje ba sanda ta nitsu ta dada yin tunani sannan bayan awa uku ta futo direct ta nufi dakin jud.

Tayi sallama sau uku ba a ansa ba,a hankli ta turo kofar tana leke,wanda yayi dede da budewar kofar bayi ta ciki,jud din ne ta fito daga wanka bata ma lura da mutum abakin kofa ba sanda ta yakice head wrap din ta da alamar zata bushar da gashi,wani ruff suka sulale suka zube agadon bayan ta,inda aka bar hjy binta da dada kare ma halittar jikin ta kallo,ko inan ta nads haske da kyaun gani har wani shegen kyalli fatar kafarta keyi yan dede ne yatsun ta dogaye kuma tsirara ajere bisa layi kamar ita dakan ta ta zana su,abu daya ne suka
Rasa kuma shine lalle,hjy tuni ta mule duniyar tunani dan har wani gani amarya amarya take yi ma jud,jud tana shirin gyara daurin towel zata kunne handrier sai taji uhmmmmm uhmmm abayan taa
A mugun firgice ta waigo,wani instant hade ido sukayi tayi saurin maida nata kasa cikin jin kunya

Hjy tayi murmushi
Har yanzu bata dena sama kyaun ta albarka axciyarta ba,kamar wata balaribiya haka nan jikakken suman sukayi da fuskan ta
Hjy ta matso bayabo ba fallasa tanacewa ashe wanka kike?ai nata sallama banjiki ba,jud ta sauke ido kasa Tace eh,bata san ya akayi ba taji hannun hjy akafadunta,"no need to be shy of me dear
Zauna anan in tayaki,ba musu jud ta zauna akan stool,da mamakin ta taga hjya ta yalyali suman kayin ta ta kunne hair dryr tana busar mata da shi,time to time tana mata oiling da deep moisturers,kuma
A hanlki take bi da ita kamat yar kwai tanayi suna dan hira kadan kadan,tun jud taba matsewa har ta dan sake jiki
tsaban dadin gentle touches din har wani lummushe idanu take tana jin layi

Can bayan ta gyara tayi mata parking tsaf tace me zakiy?
Tace kayana zansa in shirya,hjy tace ok sai ta kyketa ta futa,

Turaren dumama jikin ta ta bula tana meyi makanta sirace aftrr some minutes ta shirya Sai a Wajen cin lunch suka hadu tana zama ba a wani dade ba aliyu ya basu waje kuma dama tunda ta zauna kallon shi take yi asace har ya mike ta bi bayan shi da leke hjya nata kallon ta tana murmushi,"juice me sanyi ta zuba a cup ta kurba cikin gyaran muryan ta da saida jud ta waigo suka hade ido,faffadan murmushi ta sakar mata ayayin da jikin ta ke amsar sakonnin data keso ta isar,gaban ta ne ya fadi ras ta rasa nayi sai juya fork take tana rau rau da idanu,"cikin dada so ta bayyana mata cewa ta sani hjya tace ci abincinki mana aliyu kam yaci nashi..karki damu da shi,jud ta danyi murmushi Dan Shiru ne y gifta kafin hjya tace gobe zaku tfi ko!tace eh mumy,aje fork din dake hannun ta tyi ta kalle jud din tace ok,yau she ne hutun schl zai kare?Tace kwana biyar masu zuwa zamu koma..
Naji ance iyayen ki ma zasu dwo abuja ko?tun kan jud ta amsa tace my dear u see i wll like to meet ur parent ina dai zasu bani ke?jud ta bata shiru. Tace nima nan da satikai biyu zanzo jud tayi shiru bata ce komai ba can tace Allah ya kawo ki lpy mumy,jin hannun hjy tayi akan nata tana me wani irin tsare ta da sigar kallo wanda ya furta thousands words but yet its silence,kallo ne na nuna so,nuna yarda, da gode mata da amincewa da su tayi,kallo ne na she is welcome to thy family wanda ya saka jud jin ta kara birkicewa da frgaba a hankli ta sulale hannun ta kamar wacce zata tashi ta bar wajen,gently speaking hjy tace yata?cikin sanyin murya Jud tace naam,akwai maganan da nake so muyi dake ba a matsayin komai ba sede a matsayin mu na yaya mata,..so do sit down ki bani hankln ki
Ba musu jud ta gyara zaman ta cikin bada nitsuwar ta me gaba daya hjy tace toh Alhamdullh ala kulli haalin duk dama Zama cikin zuriar bulama ba aba bace me sauki ba amma ki dauka inkin same ni kamar kina magana da yawun kowa ne a family na,duk wani hukunci da zan yanke shi zasu yanke, hakama duk wani abun karuwa da zan kawo babu shakka awajen su duk nasu ne..ko kin fahimceni?jud tyi shiru cikin rudani hjy tce,...ok Aliyu ne yazo min da magana akanki dazu..maganan aure...kina sane ko?
Jud ta dada sunkuyar da kai mayafin abayar ta take dan wasa da shi batace komai ba...,"ajiyan zciya hjy tayi tace in har kina son shi babu me hanaku aure yata,ni dama damuwata kece,bana so kiyi abunda baki da tabbacin su,nasan aliyu ya gaya miki yana da mata ko?ai kinsan ta ma naji ance sunayi da mahaifiyar ki...

Ahnkli Jud tace eh

Hj tace,to karki sa komai aranki addua zaki tayi Allah ya tabbatar, nikuma namiki alkwarin Muddin da yardanki aciki To kisa aranki ni me baki goyon baya ne nothing to fear kinji?.

Jud ta dada dauke idanun ta kasa cikin tsananin jin kunya

Ina so kiyi tunani ne sosai sabida ke yarinyace kuma har yanzu baki san me duniyar take ciki ba..daga yau Ki dauke ni kamar uwa,kuma zanso ace na samu hakan awajenki har karshen rayuwar mu...be free with me karki damu duk matsalarki d damuwar ki ni me dauka ce,u just need to calm urself nd trust us ko jud?jud bata san sanda ta gyada kai ba,Allah ya miki albarka..tace ameen cikin jin kunya ta tashi ta bar wajen
Dakin ta tanufa ta fada kan gado wani dadi da karfin gwiwa na mamaye ta,tunda maman sa ta nuna ta karbeta hannu biyu wani karin son shi ya shiga huruwa a zuciyarta

Haka ranan suka dinga wasan boye har dare yayi inda suka shiga shirin tafiyar su,nan ma aliyu ne yace ta tabbata tayi godiya ma mama in sunje sallama bcos she packed alot of suprises for her sai sunje gida zai bata.
Chapter 60 · 0% Book details