← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 108

Sashe 8

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

06....wajajen 6am na safiya jud ta farka daga bacci,mika tayi ta yaye bed cover a kasalance tana sauke kafafuwan ta kasa adai dai kamar ance alarm din ta da ta saba sawa yay kara"its 6am,daga nan bata yi wata wata ba ta fada bathrum,ruwa mai dumi ta sake ma jikin ta ta lumshe ido sosai tana so ta tuno abunda ya faru jiya tsakanin ta da abban ta,but abun baya zuwa dan sosai qamshin l'orels bath gel datake using ya gama ciki mata kai ya hana ta sakat numfashin tane yake sauyawa a hankali da kyar ta kammala tana fitowa ta shimfida sallaya ta shiga biyan sallolin da ke kanta ko addu'¥ batayi knockin ya fargan da ita da sauri tawaigo"Waye ne?...ta furta a hnkli tana dan dubawa bata gama rufe baki ba sai taga anni mai aikin gidan su ta turo kofar

"hade ido sukayi tai Saurin dauke kanta ahnkli tana kkrin hade rai ko uffan bata ce mata ba

ani kuwa ko ajikin ta dan tasan ba shakka zargin ta jud take akan maganan su na jiya da Abba.

Juda ta bata rai cikin maganan zuci"To dama wa zai san ina fita in ba itan ba,munafuka ai nasan tasha labewa tana jina awaya in muna magana da shi,naga ita kadai tasan ina fita da abdul yarima,
mswwww

'Anni tace jud,Kije mahaifiyar ki na kiran ki"..

Ta dago a hanzarce ta dube ta sama da kasa,ta tabe baki sai dai Ko amsa bata samu damar jin zata bata ba,haka tayi banza da ita har ta gaji ta sa kafa ta bar mata dakin...sai After 3min ta biyo bayan ta,tafiya take tana jan kafarta duk tunanin ta yadda zasu kaya da Ammyn ta ne,cos More than any one tasan akan maganan jiyan mahaifiyr tatake neman ta,"damuwar ta shine tayaya xatayi ma ammyn bayani bayan ta sha mata gargadi akan ta rike mutunci kawai bayanzu zatayi aure ba?

Wani garas kirjin ta yake bada sauti,tuni ta iso bakin metallic door din ta tsaya amma ta kasa ko tabawa Cahn dai ta daddage cikin kwakwalo ma fuskn ta dauriya ta tura a hnkl ta shiga da karamin sallama..

Wani jimm jikin ta ya dauka da sanyi.."Barakallah da sassanyar yanayin dake dulmuye ackin dakin mahagiyartan wanda yake neman saurin sauyawa mata yanayin ta

Tabbas Hjy hamida yar tsaftace uwar ado ga qamshi da aji Bayan wankan tsadaddun kayan shadduna, leshona da atampopi da manyan gwalagwalai da aka san ta da su

A kowani safiya al'adan tane tana tsuma kanta da tsumin qamshi da hayakin itacuwan turaruka musamman na can yankin larabawan sudan da suke yawancin safaran itacuwan su a srilanka ne,hakan ma Bata hakura ba takan hada kaya qamshin ta da asalin baki da fari kai harma da jan humran da ake samowa a hannu shuwa arabs da kanurai a garin maiduguri.

Shiyasa namiji duk inda ka kai ga miskilanci da hjy hamida ta wulga sai ka bita da ido kana mai jinjina ma qamshin jikin ta

Mace ce dake tsaka tsakiyar shekaru talatin itama,sai dai sam hakan bai nuna ko kadan a fuskan ta ba,domin kuwa tana da kyau na fitan hankali yalolon qashi mai tsawo tsiriirin hanci da madaidaicin doguwar fuska
yanayin tsarin ta da komi na fuskn ta ya isar maka sanin cewa naked fullo ce daga gani ba tambaya,dirin jikin ta ma a murmure yake tana da manyan idanu farare kar,tsayayun nonuwa da mazauna manya wanda tsawon suman nata ta yakan zube har kusa da bangon duwaiwakan ta..

"Albarkatun dake jikin ta su suka dada bata karfin gwiwa wajen kurewa wajen iya wanka da kwalisa..yau ma Kwalliya mai dauke hankali take tsalawa dakan ta bata sa kowa daga masu iya kwalliya a tayata ba,tana lura har jud din ta shigo a sulale ta rusuna gefe da ita daidai lokacin tana bada red lipstick akan labban ta dan haka bata kalle ta ba kuma bata ce mata uffan ba

"Mamma...."Jam bamdu na?.

Cike da barin baki mai tafe da bugun zuciya jud ta furta

Wani Shiru ne ya dan ratsa wajen,2scond ta dube ta Ta mirror a cikin ranta tana cewa hmmm..dai tace
"Noi a wani bingel am,noi kugal?

Tace all good alhamdull ...tare da sauke numfashin alaman jin dadin amsar data samu

"Toh tashi ki zauna
..ba musu ta zauna abakin dark brown lush couch tana wasa da yatsun hannun ta kamar mara gaskiya..wani shiru ne ya sake ratsa wajen zuciyan ta cike da fargaba da kuma tsananin shaukin son ta gan ta tana rayuwa kamar mumyn ta Wacce Tsaf ta shirya cikin red voile wanda ya matukar fito da sigar ta na zinariyar mace.

Hjy hamida Wayar ta ta shiga latsawa cike da aji cikin yanga tana tattalin fingers din ta akan screen din kamar wacce take tausayin hannun tan,Few minutes call tayi da babbar aminiyar ta ramat sannan ta juyo ta dube ta tana daga tsaye

Tace...."Jud...?

Cikin sanyin jiki tace Naam mama.

Kinsan abunda yasa na kirawo ki nan?

Ta gyada kai a hankli tace eh...jin hjy hamidan bata yi respondin ba sai ta daure ta fara bayani

mama kiyi hakri nasan nayi kuskure
Amma wallhy kibin cika xaki gane ba soyayya nakeyi da shi ba.

Tace 'To me kenan kikeyi dashi gashi kinaji mahaifin ki ya nace akan maganan auren ki da wancan yaron,ke me xaki tsinta in kika yi auren?gaggawa me kike yi haka

Kasa dago kai tayi dan Allah yasani bata son taga mum
Dinta na fada

"Jud A Kullum nakan ce ki dube ni,ni nazamto miki madubin dubawa amma sam kamar baki ganewa.

Ure just in 100lvl me ma kika sani akan rayuwa bare ki tanada makanki zama inba mu?
To ki shiga taitayin ki,ydda kike tunanin rayuwa a sauki na haka take ba.

ki duba mana ki yi nazari akan rayuwar mu,da dadewa kudin siyasar uban ki ya kare for 8yrs ni nake ci daku nake sha daku,ke wannan gidan ma ta wace bana shi ba,sai ki auna ki gani Da haka na watsar da kaina nayi auren asara da wakenan zai tallafa ma miji na har asirin mu ya rufu haka?

Jud yanzu dan Allah kece kike son ki lalata rayuwar ki?

Muryan ta kamar na mai shirin yin kuka tace Mumy Dan Allah kiy hkr..

Hjy Hamida tace
'Sorry for urself!
Tana bi tana kallon cikin watery eys din nata

Tace Dan gida yarima ko?mmm Soyayya kukeyi da yaron? Jud
Har ta budi baki zatayi magana ta tsare ta da masifa

"ke ki fadamin gaskiya dan in na binciko baxaki ji dadi ba..

Da sauri tace aa mama shidai yace ya na so na wai zai aure ni

Tace Ko? Aure ?Akwai abunda ya taba shiga tsakanin kune?

Nan ma ta girgixa kai da sauri tace ah'aa...nidai ammy ki taimaka kar abba ya min auren nan yanzu wallhy i want to be like u first..

Hakan Da tace ya sa hjy hamida jin ddi aranta tace i dont think so,kedai tashi Ni ina sauri ne zan fita,daga na dawo kizo ki same ni

Jud Guntun Hawayen ta ta share ta mike a sadade tare da mata sallama ta fice.Hade da sauke idanun ta kasa wayarta ta ciro ta dialing number jim kadan aka dauka
Tace ramla?
"Gani nan zuwa...ta fada tana jawo wata munafukar jan mayafi kusan kala daya da takalmin ta kwas kwas tana tahowa Adaidai matakalar saukowa falo suka ci jaro da mijin ta alhj abubakar

" wani hade rai tay batace mishi uffan ba Haka har ta fice yana kallon ta kansa kawai ya girgiza a fili yace Allah ya kyauta

yasani maganan auren bai wani shake mata wuya dan tasan itace mai tacewa agidan tunda itace me kudin yanzu

duk zafin alhaj abubakar sai ga qaddara yasa bai isa ya aikata abun da hamida batayi ra'ayi akai ba

Ita kuwa hjy hamida Ajiyan cikin dare har ta labarta ma babban aminiyar ta kuma shakikiyar ta wato hjiy ramlat matori daga abunda ya wakana na auren yarta jud..dariya kawai ramat tayi dataji baraxanar da alhj abbkar yay akan auren sai tace ma hjy hamida kiyi shiru karma ki sake dago maganan nan ke dai Kija ma yarki kunne ta bar biye ma yaron
Kawai.

****
Duk da haka a iya juya mazan su alhj abubukar yakan tsole musu ido wata rana dan shi dagaskiyar sa ya dogara,baban jud dan siyasa ne amma mai tsananin gaskiya da rikon amana,azamanin sa ya taka rawar gani sosai wajen yaki da cin hanci da rashawa toh a dai dai gabar da zai ji dadin aiyukan sa na alherin ne makiyan sa suka jefe shi da sharrin froud ta hanyar masa mumumm cune akan dukiyar gwamnati kuma ahaka sukayi fafur sanda suka dora shi akan gadar zaren da har yau shine silar sashi ya tsiyan ce ya dawo fakiri baida kowa baida komi karshen ta uwargidan sa hjy hamida ke dawainiya dasu a arxikin ayanzu.

Duk da hakan ya faru fa su shi mutum ne mai tawakkali dan haka bai karaya ba yana nan dai yana malejin rayuwar sa sannan har yau bai dena neman aikin gwamnati akan gaskiyar shi ba

Ummar sa kayal,kyakwan bafulatana itace makasudin hade auren sa da hjy hamida wacce takasance yar riko ce awajen mahaifin su,shi alhaj abubukar asalin fulanin yankin sudan ne amma aynxu su ma suna claimin dukku yankin su matr sa hamida

Auren hadi irin na fulanin asali aka ma Alhj abubukar da hjy hamida daga baya ne suka so juna har aka same yarsu kwara daya wato JUD .

Alokacin dayake tashen arzikin,komi na tafiya masa dai dai,agidan sama shiyake sa doka,sai dai tunda banbancin halayen sa da na matar sa hamida ba abu bane boyayye

Shikansa yasan Hamida tana son duniya,kudi,dukiya arziki..in ba shi babu ita,amma sam bata da wani matsala a fannin tsafta da iya ado

Wannan ra'ayi nata nason kudin sosai ya dada bada guduma wajen halin da mijin ta ya tsinci kansa,tsabagen son kudin ta ne yasa makiyan sa suke yawan samum nasara akan sa
.
Da shike akan komi Kudi kawai idon hjy hamida ke dubawa ita sam bata lura da irin makircin fa ake kullawa akan mijin ta har sanda ya rasa komi nasa
Chapter 8 · 0% Book details