← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 108

Sashe 15

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sede hamida ta dade tana lura da shige da ficewar jid agidan wani tarin bakin cikin takeji ganin yadda jud gaba daya ta sauya halayen ta babu wani wanka babu isashen qamshi babu aji sai uban doka salla da yawan saka hijabi da shiru shiru

Se Tayi kyam dai batace uffan ba dan tana jira ne taga matsayin cikar alkwarin abbakr na damka mata babban mota da kudi kafin ta fara cika alkwarin ta data dauka

Shikuwa yanasane da duk abunda take ciki,sanda ya karance su tsaf daga ita har jud din sannan ya nemi inna shawara..

washe gari da safe as a suprise jami'an banki suka biyo hamida har gida tayi signing millions da sunan ta kuma amshe kyautar babban motan ta

Tsaban maitar abun duniya hamida murna takeyi tana yi ma abbakr godia kamar bata taba raina masa wayo arayuwarta ba.

Shikam inda sabo ya saba,dan yasan a duniya in har kaime kudi ne to hamida zata kasance mace ce me kyan hali agaban ka harse kasha mamakin ta

Dan haka ya dada jadadda mata sharudan sa musaman akan jud

Washe gari ya wuce lagos can wajen da kamfanonin da zasuyi aiki da su suke don ya fara shiryawa ma gundarin tsarin ayyukan da xai fara in ya dawo abuja.

Da sassafe jud tana idar da sallah,taji ana daka mata knocking fito warta ke da wuya anni mai aikin su tace taje maman ta ne take kiran ta

Batayi wata wata ba ta mike Da hijabin ajikin ta ta fito har zuwa dakin mahaifiyarta hamida,salamu alaikum"ta furta bata saurari amsawar maman tan ba tuni hankalintacyayi saurin komawa kan yanayin yadda aka sake tsara sabbin kayan dakin,komi anan orange nd black ne hakama funitures din gaba daya royal manya manyan wadrobs da fankacecen gadon na alfarma

Ga wani uban qamshin turaren salvatore daya gwamutsu da traditonal scent sun bada kalar me rikitarwa daga ji kasan tsadaddun kayan qamshi aka turara dakin lungu da sako inka juya zaka shako qamshn dadi har kamar bacci ze kwshe ka a tsaye,ko ina neat gado yaji shimgida it feels like a dakin matar sarki kake ko uwar gidan shugaban kasa

Aranta tana ta admiring din komai a dakin,gyaran muryan hamida ne ya fargan da ita suka hade ido nan ne ma ta lura da wayar da ke kunnen ta,"hamida ta watsa ma jud kallon sama da kasa da alama hijabin ne ya bata haushi,seta mugun daure fuska jud kuwa bata ma dago lefin ta ba tukun a tsaye ta jingina da wall tana jira maman nata ta kammala wayar ta gaishe ta..

A kasaitance hamida tamata alaman ta matso tana matsowa ta mika mata wayar
Tace karbi...maman ki ne"da alaman tanbaya akan fuskan jud..seta mata ido akan ta karba da sauri,abata san waya ke magana ba ta sa wayar a kunne"Tace salam ina kwana"wani shiru taji can taji an dan ja tsuka,hakan yasa ta fahince cewa da ramat take magana itama atake ranta ya baci dan gaba daya taki jinin matar..

Haka kike gaida uwarki?jud tana shiru...inade kin dawo?to meda ma uwarki wayar,tun bata gama zancen ba jud ta mika ma hamida wayar ta juya kanta tana dan turo baki,cike da rashin fahimtar tasu hamida tace har kun gaisa?ramat tace to tamun shiru ai yarkin nan ke kadai ke iyawa da ita badole ma akaita gidan bara ba...she is so disrespectful wai wani ina kwana ba sakaya na karya wuya ni sa'arta ne?hamida batace uffan ba ta bi jud da wani irin kallo da harshen yare ta dan daka mata tsawa tace _Asautina?_
_Kina haukane?_
Maza karbe ki haishe da mamanki da kyau kuma kiyi mata godia,ba musu jud ta karbe wayan ta aikata hakan,ramat tana amsawa ciki cikii tana fetsa mata magana,jud tayi shiru ta mika ma hamida wayar bata dena mita aranta ba sanda hamida ta daka mata tsawa

Waike meyasa bakiji ne?ke kenan kullum bazaku nitsu ba,mesa baxaki gaishe ta ba?kin raina ni ko?

Cikin kwabe fuska jud tce Mama nagaishe ta..ai ban san ita bane

Hamida tace yimin shiru,to wallahy gwara ma kisa aranki in bana dunian nan ramat ce uwarki..u better respect her kinaji na?

Jud tace eh

Nan hamida ta shiga kananan surutu tana me tabbatar mata cewa in ba dan ramat ta taimaka ba da har abada agidan inna zata kare

Jud kuwa tuni ta shiga maganan zuci"..haushi takeji dan duk sanda ramat ta shigo tsakiyar su se maman ta tayi ta mata fada

Tun asali jinin ta dana Ramat be hadu Ba sam

Matar ta samata ido wuce misali,tun tana karama take yawan hantaran ta abu ko ba lefin ta bane se tace madallah

Jud Bazata manta ba akwai wata rana lokacin tana ss1 ramat ta taba kawu ziyara zuwa gidan jud din tasama a falo tana karanta littafin hausa

To akan wannan karatun seda ta yi sanadiyar sa abban ta yahana ta walwala kwata kwata agidan na kwana biyu da kyar ya sauko ya dena fushin

Kuma bakomai bane yasa ramat ta dada harzuka sede Wai dan ba a gaishe ta akan lokaci ba,haka ranan ta tuma ta rinka korafi Tanacewa ai tsaban jud tasa karance karancen iskanci da soyayya aranta shiyasa bata daraja babba..

Tace ma abban jud ai jud ta dauko hanyar lalacewa kenan,har ta sa shi yaji wani iri aransa

Jud kuwa tun tana tsoron ramat har abun ya fara bata haushi dan arayuwa bata san me ta taba yi mata ba..

Tsawan da hamida ta daka mata ya fargan da ita ta da dena tunanin

Hamida Ta dubi jud din sama da kasa a hatsale tace waimeye ne kike kumshe jikin ki da kaya,tun kan ta amsa ta shiga kwala kira...Anni Anni ke anni tun kan jud ta cire hijabin jikinta se ga annin ta shigo da sauri tana cewa gani nan hajya, wani wawan fauce hijabin tayi a hannun ta ta wurga ma anni,yimin waje da wannan abun da rawar jiki anni ta dau hijabin tayi waje da shi,dada sauke kai kasa jud tayi tana me jin sauran surutun mahaifiya rtan

"Waime kika dawo ne jud?kazama? Wannan salon kazanta da kauyanci ba anan ba,se naci ubanki inkika sake samin hijabinnan a gidana
Wawiya kawai..jud tana shiru batace uffan ba har hamida ta gama surutun ta.

Wasu abubuwan ma bawai fahimta take ba Ji tayi kawai ance kije kifara kimtsawa ni xan fita
Daga na dawo kizo ki sameni ba.

Da Toh ta amsaa sannan ta wuce site din ta...

Wayarta ne yy kara ta dauka se taga unknown number....
*KUDI..kumbar susa*

_YADDA AKE BIYA,HOW TO SUBSCRIBE,plus payment details_

_FARASHIN SA👇🏿_

#300 naira ne
#450 naira for VIPs

*1- Biya Ta bank acct*

_Use👇🏿_

Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB

*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*

*2.MTN RECHARGE CARD OR VTU TRANSFER👇🏿*
*08060712446*

*Sai ki tura screen shot shedan ki wa 👉🏿08036651119*

*3:yan kasashen da ba nigeria ba masu biya ta PAYPAL,OR*
Use👇🏿

Account name:
Surayyah muhammad suleh
Acct number 0152983148
Bank: GTB
Phone Number :07058797141
CITY:bauchi: _PLS DO NOT READ IF YOU DO NOT PAY......_

*Wanda ya fitar tsakanin sa da wanda suka biya ne domin hakkin su ne*

12..Dakinta ta nufa wayar hannun ta na kan ringing da kamar bazata dauka ba se kawai ta manna a kunne tace salam daga nan Wani kara ta sake ayayin da ta tsinkayo muryan aminiyarta wato mariya..

'"Jud Yan mata ashe kina duniya?

Tace hmmm mariya kenan,aike zan wa wannan tambayar ashe haka kawancen yake se ki share ni?kinyi wa kanki

Dariya mariya tayi tace Hmm kedai bari jud akwai labaraiz albishirin ki?Jud tace goro,...
cikin sauti me nuna murna tace kawata nan da kwana biyar za'amin transfer in dawo abuja,kinsan wani abu?jud ta girgiza kai..tace a makarantan ku aka sani kuma abba na yace course din da aka maidani shi kikeyi kenan. .girl we gon be class mate again...

wani ihun yeeyyyyyy jud ta sake cikin sautin daria me nuna farinciki kamar ba ita ba

Atake fuskan ta ya gume da wani sabon annuri..Tace wow Alhamdullahi dama wallhy nagaji da yawo nikadai..

Mari tace hmm kedai,naki ai kadan ne ni gajiya nayi gaba daya danan garin yarbawan i cant wait yo see u
Friend

Jud tace me too,..daga nan hira kadan sukayi sannan mariya ta katse wayar

Mikewa tayi ta shiga kimtsa dakin ta kamar yadda mahaifiyarta ta umarce ta,tanayi tana murmushi ita kadai,hirar da suka yi da mariya awaya yanxun nan take tunawa musamman abnda suka tofa akan ramat..

Mariya tace kurwan kune kawai bai hadu ba,dan wasu zagin da ramat takan yi ma jud sam baida ma'ana.

In ba haka ba ya'za'ayi kace mutum ya cika kyau?wannan zagi ne?waye baison ya zamto kyakkwa a duniya dama

Itade har ila yau matar mamaki take bata har yau dai batasan meta taba tsare mata a duniya ba

Karfe 4 na yamma hamida ta dawo se can wajen bayan ishai ta sa aka kirawo mata jud

"Shigowar jud ke da wuya ta tura mata manyan ledojin shoping guda uku gaban ta ta kuma umarce ta da bubbudewa,nan jud ta durkusa babu musu ta shiga aikin zaro kayan dake ciki daya bayan daya tana ajewa agefe inda tuni wani fitinannen qamshi ya mamaye su,"

Ledan farko na kayan gyaran jiki ne amma da shike akwai na super markets da aka tula a dakunan su se ta siyo mata xallan traditonal body teasers.

Manya kuma Qasaitattun,sabula da mayukan wanka ne da turaren su na musamman wanda akayo mata oder su tun sati biu daya wuce a kasar madagascar

Sun hada da natural face nd body scrub,gel..body essential oils,exfoliant,moisturizers,spf da skin toners..

Dukan su product din an hada sune da ingredient iri daya imma baka samu anan ba zaka same shi anan,duka duka sun hada ne da Turmeric,licorise nd pormenganate se fannin essential oil aka sa carrot oil lavender and argan oil.

Gasunan de Hilimi guda kamar ba kayan amfanin mutum daya ba

Hamida ta amince cewa itace malamar yarta,dan haka ta shiga mata bayanan yadda zatayi amfani dasu ajikin ta bawani nauyi ko kunya,tace ba siyan kayan gyaran bane sanin amfanin su ajiki shine babban aiki
Chapter 15 · 0% Book details