← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 108

Sashe 57

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana saura sati guda thas bayan sati uku cif cif da dawowar su daga dubai,sultan ya yanke hukunci zai mallaka mata rijiya ko da ta duba tagani sai ta lura karami ne sosai aranan ma kusan dambe sukayi da bilkisu amma hakan ba shi ya hana komai wakana ba

Ko da ramat ta nuna rashin amincewar ta sultan sai yace "ya bata maganan shi ta karshe kenan."ko ta samu karamin koko ta same babba amma da sharadin hannun jarin sa 50-50% kan ramat kamar zai kunce tsaban bakin ciki amma dai hakan ta amsa dan tasan inbata amsa ba zata iyajin kan ta agefe.

Wannnan abunda ya farun bakaramin jefa ramat kewar hamida yayi ba

Gashi Ta rasa yadda zatayi da laulayi gashi irin me nunawar nan ne minti daya ta tsit da yawo,bata son kaza bata so warin kaza

" taso ta kira shege yay mata aiki akan sa amma Tayaya ma zata iya gaya ma hamida tayi cikin shege bayan tasan ta hanata tafiyar ma takiji tun farko?

To tunda wautar bilkisu ya jawo mata asarar deal din komai yazo ya kare abaiibai kawai taji bazata iya ba kawai dolenta ne fa ta gaya ma hamida gaskiya dan ta shawo kanta asan nayi

Bangaren hamidar ma hakan rayuwarta yake tafiya duk kamar an saka musu hannu,bakin kishi da damuwa akan maganan business din saudi ya mugun sakota agaba u can imagine tulin zaman ta anan katsuna babu abunda take tsinanawa sai buruntu

Washe gari da safiyar Allah ta fito raka mijin ta ya fice aiki kenan saiga sallamar wata bakuwar daya sa gaban ta yayi mugun dokuwa da faduwa..

Bakuwar ce ta shigo ta dada kafewa agaban hamida tace sallama dai masu gida,ina tambaye ne ko angane mini yar uwata hamida yar fullo...mace me qamshi..?

Wani ihun balai hamida ta fasa ta rikito a gurguje tace "mena ke gani. hande?hande.. Hande.. karkice dani mafarki nakeyi nuna ta da yatsa tayi a firgixe muryan ta na rawa tace "Hande...sai ta fashe da kuka ayayin da bakowar ta taho a disashe ta rungumeta ajikin ta sosai suna me taya juna.

"Asalin sunan Hande,hamdiya muhammad,..duk da kasancewar hamida na marainiya amma hande kamar yar uwace mata na jini,dan itace suka hada uwa da ita ata wani fannin amma uba kowa da nashi

Ma'ana lokacin da mahafiyar hamida tayi aure hande itace yar agwalar data zo da ita tana zama agaban ta har aka haifo hamidar sukayi tashen kuruciya tare..

Sede banda uwa babu abunda ya hada su,kowa da nasa uban kuma kowa da nasa yaren dan baban hande asalin kanuri ne daga jahare maiduguri,bayan mutuwar iyayen hamida na asali duka ahannun inna kainuwa suka rayu
dake inna kusan uwace ga marayu
To da hamida zataje karatu gombe ne mahaifin hande ya zo ya dauke yarsa ya maida ta maiduguri after 20years sai yau Allah ya sakeyin gamowar sa

Waje na musamman suka nema suka zauna yau Sunci kukan kewa da rabuwan bazata da sukayi,labari akan labari game da abubuwan da suka wakana tun ana kuka har aka dawo ana buga shewa ana dariya

"Abu kadan hande zata buga guda tace
Shegiya hamida qamshi ansamu duniya haka kukayi kudi?hamida kuwa sai dai tayi murmushi tana alfaharin d yadda taga yar uwantan
Dan kuwa babu marabar su wajen wayewa iya daukar wanka da kwalisa

Sede ita hamdiya ba zallan dirin manyan mata take da shi ba
Tana da asalin kiba
Da tula tulan maxauna fiye da na hamida

Ita dai hamdiya ba fara bace sosai amma baza ace da ita baka ba kwarariiya ce wajen iya kwalliya da tsara duk wani abun da ya shafi gyaran jiki musamman ma na ya mace..

Takan hada kaya harda kayan mata sannan tsaban ta shahara babu wata jaruma me sana'ar ata yankin sokoto maiduguri niger sudan india da yankin larabawa wanda bata sani ba

Busines din ta kenan kuma Tayi kudi da harkan bana wasa ba,ayanzu haka ta dawo neman yar uwan ta ne sabida mutuwar mahaifin ta wanda dama shi ya mata katangar karfe da hada zumunta da yar cikin mahaifiyarta hamida sannan ya kafe ta ya hanata aure.

Taso ta tsine ma bakar halin sa amma duk cikin halayen hamdiya babu abunda ya fi karfi kamar tausayi da mattukar son neman ilimin addini ta karanta fannin biology education a unimaid amma bazaka wani gane hakan ba sabida ita bokon a ado kawai ta dauke shi

Awajen ta sana'arta ya mata riga da wando,hakan yana daya daga cikin kyakyawar garkuwan da ta samo har Allah ya kawo ta wannan lokacin

Daga yadda suke hirar au zaka san lallai sunyi matukar shakuwa dan babu abunda suke boye ma juna,kaf labarin arzikin hamdiya ta bada hamida hakama hamidar ta shiga zayyana mata dukan abunda ke faruwa da ita game da neman kudi da abunda ya lifta tsakanin ta da kawarta kuma aminiyarta ramat wanda hamdiyar bata taba sani ba sai yau,ita takan ce ma tafi kowa sanin hamida akan maitar son kudi
So xata iya amincewa da Komai daya futo daga bakin hamidar

Sai dai maganan ramat shiyaso ya bata musu komai
Dan Fada hande ta shiga mata tana nuna sam hanlkin ta bai kwance akan ramat din nan ba,tacw ace mace ce da mugun zuciya har haka?tace kedai hamida baki sauya ba inba shegen son kudi ba inake ina hada hanya da muguwar iri
Irin wannan?wanan fa ba kawa bace irin su ne ake cewa da haihuwar su gwara barin su,me zata tsinana maki?zakici aminta ne yanzu keda bakinki kike gaya min yadda kuka rabu a saudi,to in zaki shafama kanki sa'a ki kunce kawance nan

Hamida tace tab a'ha hamdiya,bazaki gane bane,wallahy bazan iya haka nan kawai ba,kin manta nace miki ramat tana auran asalin attajiri ne?wallhy in har ta sami harkan man nan sai nasan yadda zanyi in yanke rabo na haka kawai in kyale kifi inbi gwado?tab

Hamdiya tace hm yi saffa saffa dai nidai na gargade ki
Tace waima kina zagawa wajen inna kuwa?

Hamida tace turrr wata innar datake juya min kan miji da yata?

Hamdiya tace wayyo Allah anyi uwar banza kince min ki haihu da abbakar dan Allah ina yata jud,jud ko?ita take?ke kya rasa suna sai jud?sekace wanda akayi mana gorin baki da ja.
Dariya hamida ta fashe da shi

Jud yar gatan maman ta ina kike kizo kiga asalin mamanki,ina kike farar wata sha kallo
Ta kalle hamidan tace Hamida anya ta gado kyaun mama kuwa?ko de dangin inna ta debo

Hamida ta yanke dariyar tace ai sai kiyi,yata kam ta girma sosai kuma ma dake tayi kama
Allah ya kiyaye ta debo gadon mabarata

Murmushi kawai hamdiya tayi ta cigaba da zaga falon tana nema ganin jud,dan tariga tasan yar tsaman dake tsakanin hamida da inna tun suna kanana wannan tara yaran bara da simple life irin na inna shi sama hamida taki jini sam arayuwarta

Haka suka karashe shirmen su sukayi dakin hamida ta gaya mata ai jud bata nan taje india,nan ma wani sabuwar hirar aka bude,kafin yamma har sun cancnda azabar wanka sun sha kwalliya gidan shikansa ya gumame kamar zai yi magana dan qamshin turare

Dake hamdiyar tace zatayi oder sinadaran kayan hadi kayan mata anan katsina,se hamida tasa aka share mata wani babban site agidan na musamman abun gwanin ban sha'awa yarda suke matukar kaunar juna.

Koda abbakr ya dawo bai same matsala da hande ba,dan ba marabar ta da hamida saidai ita babu wannan tsinannen son kudi aranta kamar na hamida kuma ita tana da sanin ya kamata kodan Albarkacin harkallar cinikayya da gogayya da mata datakeyi awajaje daban daban..

Hakan suka yi zaman suna dan fita,hande tana dawowa karfe hudu na yamma ne inda ta dinga saka hamida agaba tana cusa ta akan hanya musaman rufe idon datayi akan kudin ramat da ceqa kawau tafara tada nata a Kwana biyu kacal hamdiya ta hana hamida zaman sakat

Dadin samun gwarin giwar hamida yazo ne a lokacin da hamdiya tace itama a abuja zata siya gida kuma takafa kamfanin ta
Tasan kenan koba komai dai bazasu sake rabuwa ba dan bakaramin son yar uwantan take ba

Sede tsaban son kudin hamida takejin bazafa ta kyale ramat ba,yau kamar yadda hande ta taso mata da tambayayo akan rayuwan yarta jud haka itama ta bijiro ma zuciyarta tsaban tunanin ramat dan tana da yaqinin awannan satin zasu dawo...

hande ba mace me daukar dumi bace amma sam bata ji dadin yadda hamida ta babbata amsa akan rayuwar jud ba
Da kyar ma ta amince sukayi video call ta waya,Allah ya so jud din ma ita daya ne nan hamida ta hada su da hande
Suka jima suna gaisawa dan hande har hawayen dadi se datayi data kalli jud kuma sukayi magana,tace ma jud nice asalin mamarki karki damu xaki dawo ina nan injiranki ko auta?jud sede tayi murmushi dan ta lura sabuwar antyn ta bata da matsalar saurin sabawa da mutum

To bayan nan kusan kowani rana tana tura mata sakon yaya take?tun abun nama jud wani iri harta zo ta saba tana amsa anty hamdiyar,ita kuwa intaga hakan dadi takeji aranta dan bata tsammanin yar sun ta girma tayi hankali har haka ba
Kuma gani take sune kawai famylin ta na asali a duniyar nan

hakan yasa yau dataje office din ta ta kira inna suka sha hirar dn tuni ta karbe numberta wajen abbakar inna yau harda kuka

Hamdiya tace mudiin suka kammala komai zasu dawo abuja me gaba dayan su
A kiyastawarta baifi nan da kwana 10 zuwa kwanaki sha biyu ba

Hamida ta dawo ita daya by 4 zata shiga gida babban wayarta ne ya hau ruri tana dagawa kuwa taci karo da sunan shakikiyarta wato ramat.
_KKSPls inbaka biya ba karka karanta game bukatar sayan littafin ya turo katin mtn ta 300 ko 450vip ma 08060712446,ko ta acct 0152983148 surayyah muhammad suleh gtb.kuji tsoron Allah kubar masu shi_
7/17/20, 9:18 PM - Ummi Tandama: 42..
_KKSPls inbaka biya ba karka karanta game bukatar sayan littafin ya turo katin mtn ta 300 ko 450vip ma 08060712446,ko ta acct 0152983148 surayyah muhammad suleh gtb.kuji tsoron Allah kubar masu shi_
Chapter 57 · 0% Book details