← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 108

Sashe 47

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sassafiyar Allah ameer yaga aliyu yana ta shiri ya dube sa yace wai saurin me kakeyi ne gida fa zakaje?aliyu be kulasa ba sanda ya kammala tsaf ya dubi tai wang dake hannun shi yana kiyasce lokacin da jirgin sa zai isa abuja yace Ameer
"Bana son nakai karfe 8 anan garin ina da wani abu me muhimmanci wanda dole inje in duba,cikin tabe baki ameer yace to ai shikenan mwayi waya,..ahaka suka rabu 7.56am aliyu ya shigo cikin garin abuja koman sa a tsare as usual
Saidai Drive din da zai kawo sa gida ne yaja lokaci dake few drives ne tsakanin airport da anguwar su..
Safiya da sauran ma'aikatan gidan atsaye suke wajen kikkimtsa komai kowa na miko gaisuwa amma hanklin aliyu baya nan,Daga shigowar sa gidan site din jud ya nufa yana turo kofarta ta sega sautin shigowar kirar mahaifiyarta hamida
7/17/20, 9:17 PM - Ummi Tandama: 35..
wani faduwar gaba ne ya taso masa ayayin da ya kalle sunan hamida akan screen dinsa da kyau jud kuwa tana hangosa ta sauko a guje ta fado jikin sa

hannun sa guda daya yakai kunne dayar kuma ya kankame ta ajikin sa sosai.

"Yace Salam alaikum hajiya hamida!

A hargitse Jud ta dago ta kalle shi,irin wata hamidar?
sai taga kuma yana murmushi yace," lpya lau ya aiki?
Kin dawo ne?to ina matata kuma?

A dayan bangaren hamida tace hmmm ranka shi dade kenan ai nadawo nikam..matar ka ramla ai bata idda ba,fatan komai lpya ya jud take?
ya shafo kan jud datake kallon bakin sa cikin fargaban sanin mahaifiyartan ne yace lapyarta kalau ai suna ma hutu Amma inaga next week zataje excursion"..bude baki jud tayi cike da mamakin abinda yace"nan ya kashe mata ido alaman tayi shiru..,hamida kuwa batare da ta kara masa wani tambayar ba tace Allah ya bada sa'a.."
dama na kira ne in sanar dakai na dawo yanzu haka ina katsina tare da abbakar sai Kayi hkri dan Allah zan dan jira shi ne ya kammala aikin sa inyaso sai muzo abujan tare mu dauki jud, and pls bana son jud taji cewa ina nigeria for now...

Yace ok hajya hamida babu matsala ai..Hala kafin nan ma ta dawo daga excursion din..

Hamida tace wai aina haka?

Yace i think a india ne is a field course

Sake shi jud tayi ta koma gefe da fargaba dan gaba daya ta rude da maganganun dayake furtawar she was like"wani excursion wani india?ko de schl ne suka tura masa hakan ita bata sani ba

Tanaji hamidar tace
To Allah ya taimaka nima zan kirata anjima amma da landline dina yace ok babu matsala.

Hirar saudi kadan sukayi ta katse wayarta..

Nannauyan ajiyan xucia ya sauke yaname cusa wayar sa a aljihu wani waro hannayen sa duka biyu yay yana bin ta da kyakkawar murmushi inviting her for a hug again,sam bata iya daure mayukan idanun shi musamman alokacin dayake kawata shi da murmushin sa me mugun kara ma fuskan sa tsantsar kyau da kwarjini,a dan kunyace ta sake tahowa ta fada jikin sa suka wani kankame juna suna yar lilo.."aranta babu abunda takeji sai kwanciyar hankli,iya sautin numfashin su kawai kakeji yana tashi awajen
,kwanciyar rai da tsananin shaukin kauna shiya buwaye su ahakan sunfi minti 20 kankame da juna..can ya tallafo fuskarta yana me kallon hasken dayayi tayi kyau tana wani kyalli sakamakon yau bata kona shi da kwalliya ba,"slowly tace ure welcome back mama na ne ta kira ko?baice komai ba idonsa kar akan ta cikin yanayin marairecwa
..can yace yes tare da shafa gefen fuskan "so how u babyn d?did u like ma suprise"..kafin ta amsa har ya dago habarta ta yana me dora lips dinsa akai wani lumshe ido tayi ta amsa suka fara aikin shan yawun juna saida yyi me isarsa sannan ya dakata,wani irin kallon juna sukeyi ayayin da zuciyoyin su ta nitse tayi kundun bala wajen warware ma'anonin shakuwar su dake wanzuwa acikin zukatun su

Aliyu tamkar wani jigo ne arayuwan ta wanda bazata taba iya mancewa da shi ba.

Lokaci daya ta kamu da tsantsar kaunar sa a zuciyarta mai gauraye da tsananin yarda da sha'awar sa me tsanantawa.

Shikuwa aliyu ya sha ji arnsa kamar washi kadai akayi jud a duniya,dan a kowanne giftawar dakikan nunfashin sa dayake saukewa tsantsar kaunar ta yake hurowa yana neman hanasa sakat..

Tace dady me kake fada ma ummah na nan? Naji kanacewa..da sauri ya datse lips dinta da yatsun sa yy murmushi yace" zan miki bayani amma se kin cika min alkwari na,bakince zakimin abinci me dadi ba?im soo hungry kuma sabida ke na taso sassafe,fadawa jikin sa ta dadayi ta lumshe idanun ta sosai ta yar murmushi ajiyar zucia ta sauke tace 'nagode..im soo happy ure back,it feels so empty witout you"i miss u,goshin ta kawai ya sumbata..wani tattaro nitsuwarta tayi ta dora masa light kiss agefen kuncin sa kawataccen murmushi me sanyi ya sakar mata me narkarwa,tace dad.."kana jin sha'awar cin wani abu special ne ko inyi nawa kawai?.
Yace ure the boss kizaba tace ok..i will make ur breakfast now..toh kaje ka huta to..kai ya girgiza yana bin ta da ido,har ta kikkimtsa suka fito waje tare.

Sanda ta shige har kitchen sannan shikuma ya nufi fankacecen luxury extrema bedroom din shi mai gwanin ban sha'awar kallo da sa nitsuwa wa xuciya.Yau Shida kansa ya hade ruwan wankanshi acikin full sized jacuzzi nan ya nitse a ciki yana famar sauke numfashi

Bangaren jud kuwa tana isa kitchen ta soma aikin da ya kawo ta,ko safiya yau komaya gefe tayi tana ta famar mamakin ta gaba daya qamshin dadi ya cike musu ciki

Pickles and spicy souces ta shiga harhadawa,yana wuta yana karasa nuna tana hada breadfruit dan kadan agefe,both rice and roshi ta hada su suma awaje guda ta dafasu atare(pply known as"long eat")sai tayi hadadden miyar "garudia"wato irin miyar nan ta zallan smoked and dried fish,me dauke da red chilli da lime to dama da shinkafar long eat din ake ci dan haka tayi komin ta dan dai dai,sai tayi papaya purees a matsayin derset
Ta shisshiryasu a hadaddun food bowls

Wani portable table na serving din abinci ta dauko me suna "dumpwaiter" wanda dama yawanci ba a samun sa a gidaje sai a asalin irin 3star hotels din nan aka fiye amfani da su

To Tsabar yawan kala kalan abincin da jud ta harhado yau A dumpwaiter aka jero su tsaf
amfanin sa shine moving abinci daga inda aka dafa shi zuwa inda za'a ci shi

A kasashen da suka fimu samun ci gaba shi dumpwaiter yakan zo ne kamar karamin lift ko elavator inda zai dinga rarraba abinci daga wannan building din zuwa wani building ko daga saman bene zuwa kasa..

Straight ta nufi hanyar dinning dake side dinsa dan nan yafi privacy sannan tsarin wajen ya dade yana matukar burgeta.

Thy are two colours that speak of luxury nd royalty kuma sune purple and black dan haka wajen a tsime yake da launin labulaye dark masu matukar daukar idanu da tsada,both in purple and black colour..

Manya manyan set din royal cushions din sukuma zallan dark purple ne da trow pillows dinsu same colour amma light.

Crystal chandeliare Airmores,da brass lanterns sukadai ne daban domin shikanshi dining din da dark theme glass aka kawata shi

Akai ta shiga jejjera abincin neatly cikin tsafta da nitsuwa
Tana kammalawa ta nufi dakin ta domin ta sauya dresing ta fito..

Sanye cikin tradional milano gown lilac ta sauko
Qamshin humrar ta wanda ya gaurayu dana turaren oud sharqiya shiya jefa ilahirin gidan a wani sassanyar yanayi

Bataje room dinsan ba tayi xamarta akan dinning,a kasaitance ta tura masa tex dacewar food is ready

Shikam Dama tuntuni ya fito daga wankar dan har ya kawata kansa da kananan kaya cool maroon shirt nd deep matte trouser
Wanda suka mugun amsar ginannen jikin shi,turaren sa na salvatore ferragamo ya yayyaba sama sama dan bakaramin yunwa ne yake kwakumar cikin sa ba..cikin sauri ya zura simple versece half shoe yayo waje inda ya same jud tana tsaye tana shirin jujjuya plate da niyyar fara serving dinsa

Yabon ta yakeyi a zuciyar sa har ya taho ya zauna abban kujeran wani sassanyar murmushi kawai take sakewa batare da ta kalle kwaliyar san sau biyu ba,shikam a zahirance yake yaba irin kyaun datayi yana nuna kulawar sa akan kokarin ta wajen girke girken datake jerowa agaban sa

All his life in aka cire mahaifiyan sa hjy binta da mai aikin su safiya to tabbas bazai iya bada shedar wata tanayi masa wannan dabiar ba

Rabon shi dazama akan dinning shida matar sa ramat da ximman cin abinci baxai iya tuno rana ba bare wata

A hankali ya janye idanuwanshi daga kan bowls din jin qarar yar wayarshi

,nan ya cirota daga aljihun black trouser din dake jikinsa yana duba sunan mai kiran,abun mamaki ramat ce,dan qaramin tsaki yaja dan yau ba matsala yake so ta qara mishi ba,ya riga da ya yanke magana shi ya gaji da masifar ta Allah ya bata sa'ar abunda taje nema.

qwafa jud tayi ganin yadda yake famar katse wayar,yana kokarin maida ta silent dahar ta budi bki kamar zata masa tambaya sai ta tuna yin hakan ba ajin ta bane,nan da nan ta maida komai ba komai ba tayi zamarta,nan suka zauna cin abincin atare yana mata yar hirar santin sa me dadinji da ban daria..

Komai da komai awajen sanda ya taba kuma yaci,cike da neman sakata yin magana mai tsayi ya shiga praising din mahaifiyarta hamida da cewar ta iya tarbiya..jud rasa mema xatace dashi tayi ta dai zuba masa idanunta tana faman murmusawa

Sanda ya gama tsaf,sannan yayi hamdala ya kura mata ido..can Yace jud?Tace naam ddy

ajiyar zuciya sauke ya kamo yar yatsun ta cikin rikitaccen yanayin kallon ta me sanyi

yace nagode.

Rau tayi da idanu alaman bata fahimce sa ba

hannu yasa a dayan pocket dinsa ya xaro wasu formal papers ya mika mata su,..karantawa ta shigayi atake amma Bai bari ta idda ba ma Yace"..please dont say no!..
Chapter 47 · 0% Book details