← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 108

Sashe 63

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Turo kofar dakin ta tayi a hankli ta dube agogo tana ne sake wata ajyar zuciya,can ta cire kayan ta ta daura towel ta nufo bathrum warm bath tayi ta tsane jikin ta da mayukan qamshi agurguje ta gama ta fito tayi yan shafe shafen ta sannan ta bude wardrobe ta dauko sabuwar rigar bacci red colour na kamfanin wengers wanda tsaban rashin nauyin sa gaba dayan ta bata fi a dunkula a tafin hannun ba guntun gown ne iya cinya da brexia hand wajen cup din nonowarta an tula masa foam wanda suka dada bulloko da girman nonowarta suka cicciko suka tsaya awaje daga tayi motsi suma se suna motsawa,duka ta mayar da suman ta baya ta kama da yar clip shima ja,feshe ko inan ta tayi sannan ta dale saman gado ta mike kafarta tana me lumshe ido sosai tana sake ajiyan zuciya,
mirginawa tayi ta dauko wayarta sannan ta bude ta shiga tura tex bata jira reply ba,after 5 min ta kira shi ta compterr ta,ya dauka atake hoton fuskn sa ya nuna da alama ya fito daga wanka kenan dan tiwel ne a kugun sa yana goge kanshi da karamin dake yake hannun sa,
murmushi me sanyi suka sakar ma juna
Ayayin da dressing din ta da yanayin yadda kimtsatsun nonowar ta suke masa welcome sukasa ya taho gaban screen ya xauna batare da ya sani ba,sautin kiss muaammmh ya turo ma kirjin ta nata ta gaban screen,cikin jin kunya ta jawo pillw ta rufe tana sake dariya,yace baby bakiji ko,yanzu fa nayi wanka ko so ake nakarayi a shagwabe tace am sorry..i just forgot..yace mmm ist ok ai dole na ai na koyo control ko?a hankli tace eh..yace till when?next week in kin xamo matata?injira samun hakan ko,yar dariya kawai tayi..u knw i cant resist u ure so beuriful ya fada yana dada leko fressh cinyoyin ta da suke fallasa hasken su,cikin shagwabbaben yanayi tace i miss u,dama na kirane inganka kafin nayi bacci,yace thats sweet of u baby..mekike dazu dabaki son ki dau wayata,tace ai na nafada maka ina gaban inna ne itace fa wai sai munyi karatu,yace good wani irin karatu knan?ai baku koma schl ba,tace yah islmiya..yace ohh..
Yawwa baby we have sumting to talk abt,tace ok inajinka.
Yace to bari in saka kawai,kema ja bargi ki rufe jikin ki ina ganinki hakan bazan iya komai ba,tayi smirks a sanyaye ta jawo barkon ta kawo shi har wuya tayi shiru tana kallon sa yana sa jallabiyar sa har ya gama ya dawo sannan suka fara tadawa...

Nan ya shiga tambayarta abubuwa masu muhimmaci wanda bata tsammanin samari da yan matan yanzu suna tsayawa suyi shi a tsakanin su,she just tot ko dan shi ya manyan tane ko dan yana da kudi sosai amma wani abun ba haka bane kawai sanin kai ne,sabida karara yake nuna mata abunda yake so yake kuma expcting ya samo wajen ta inta kasance matar sa

Tunda yasan in yayi maganan sexual life da soyayya zai iya jangwalo musu jin wani abu, se kawai yayi skipping part din ya soma nagana akan dangin sa da addinin sa,musamman dangi wanda ramat ta kore su ajikin sa da duk wani aikin addinin data haramta ayi acikin gidan sa yace xai bata kudi duk iya yawan datake so shide burin sa befi ta basu kulawarta fiye da shi da girmamawan ta ba...yace bby kiyi kokari kixamto me daurewa wajen muamala da mutane kinsan nayi siyasa ko?jud dake jin kamar kanta na mata nauyi tace eh.

Yace to u hve to be honourable with urself kisa aranki zaki tsaya agefe na ne so karki yadda ana ce miki karaman yarinya bcos once ure my wife ure no longer a child,saida ta dan ja kafin tace ok..yace good nasan mumy zata gaggaya miki yadda akeyi amma nafiso kifara jin su abaki na..ina fatar kin fahimce ni ta turo baki tayimishi pauts a sangarce tace eh dady,yayi yar murmushi,yce what?nide dan Allah asauya min suna in na angwance aka kirani wannan sunan ai sai asani jin kunya,dariya me yar sauti tayi tace au ba dadyn bane,hmn ai na nema maka daddan suna kawai bayau ne ranan fadar sa ba,yace hmmmm nima bansonji yau,nafiso inji shi acan cikin kunne na
Ranar ne zaki san ina asalin sonki,wani rau tayi da idanu sannan ta rufe idanun ta da tafukan hannyan ta
Ta barsa yanata murmushi,haka suka dinga hira marar gajiyarwa yana dan bata shawarwari kafin ta ankara karfe uku na dare yayi,tace wayyo Allah inna yanzu zata zo tashi na,yace 3 din?tace ai nan gidan da asuba ake tashi,kuma anty hamidya xata zo yawwa daddy wazai kwashe min kaya na acan,this week xamu koma gida wai..yace uhmmmm
Yanzu de kiyi baccinki gobe zan sa safiya ta tattara seta ba driver ya kawo miki,tace ok kai baxaka yi baccin bane yace zanyi,let me have my gudnit kisss,ya matso scren yana turo mata baki ta taho ta masa muaaaah,yace i love you..tace love you.
Nan suka katse,futsari taje bathrum tayi ta dada kulle dakin da keys ta ciki bata wani jima ba bacci me nauyi ya kwashe ta.

Da asubah inna ta zo za'ayi karatun qur'ani to babu irin masifa da bambamin da inna batayi a kofar dakin ta ba anma haka taki fir ta bude,wani nauyi idanun ta suke bacci duk ya kashe mata jiki,se wajrn bakwai saura ma ta mike tayi sallah,wanka tayi a hanzarce ta saka riga da skirt na kampala green colour sannan ta nufi site din innna
Innan ne zauna akan kujera hannun ta dauke da littafin dake warware matsalan mata akan al'adar su Suna hade ta watsa mata kallon lallai ma,kamar wanda ruwa ya kawso ta rusuna"inna ina kwana?inna tace kinyi wa kanki..Tace inna wallhy bacc,inna tace kimin shiru shasha bccin lapya?aikin surfe kikayi agidan nan ko nika 10 fa mukayi sallama dake,jud ashe bazaki aje lalaci ba,tace inna kiyi hkri an dan kirani ne,masifa inna take ta inda take shiga bana take fita ba tace"ga abun karin ki nan agabana ki zauna ki cinye ki wuce kije kichen yau ke zakiyi komai agidan nan na fada miki,ko karban haddan su hamza bazanyi ba ke zakiyi nagama magana...jud ta runste ido tana mutsuka fuska banda toh bata sake cewa komai ba ta jawo abincin ta soma ci still tana yi tana latsa waya,hadadden spagheti ne wanda yaji kifi da kayan lambu tun kan gamawar ta inna ta fauce wayar ta korata ta wuce kitchen,godiyan Allah da ta samu me aiki ta gama wanke wanke da shara tayi moping da alama abinci kawai zatayi

Jingina bayan ta tayi da Wani nannuayan ajiyan zuxiya,me aikin su tace lpya?jud ta labgwabe murya tace inna tace wai ni zanyi duka girkin yau dan Allah kitayani munayi tare anjima sai inje in fara karban haddan su hamza,me aiki tace babu matsala tace amma bazaki fada ma inna bako tace mata a a

wake suka fitar suka wanke suka jikasa da kayan miya dede nayin moi moi sede dayawa dan yakusa cin mudu goma,duk jud adar take tana leken hanya karma innna ta shigo me aiki ce ta bayar wa yusuf suka kai aka markado sunfi awa biyu suna zuzzubawa a leda gaba daya sanda jud taji ba dadi yau gashi ko daukar wayarta ta duba innna batayi ba

..tana gamawa still inna ta sata agaba tayi tuwon masara da miyar kuka wanda yay fresh yaji daddawa da tulin kashin miya..

Qamshin miyar yasa Yara zagaye,ita kuwa wannan duk be dameta ba Kewar aliyu da tsumayin sake jin muryan sa duk suka cike mata zuciya da kwakwalwa,ko se yaushe zaidawo din oho,lokacin karfe 1 saura na rana komai yana kan wuta taje tayi sallahn zuhr ta dawo still inna bata barta ta dau wayar ba,tana kada miyar se famar tura baki takeyi ita kadai tana sose sose,bayan an sauke abincin kusan wani awa suka shafa wajen kasawa akalla yau dai gaba daya a kitchen tayi rayuwarta fita waje tayi ta tara yan hadda tace duk me bukatar cin abincin sa yazo ya bada haddan sa,kowa ya tsaya kallon ta dab ba a saba musu hakan ba,ita kuwa so take tayi komai a gurguje dan ta karbe wayarta taje daki "one by one suka fara xuwa in kayi karatu seta mika maka abinci..

Yusubu ne yace yakai gulman wa inna inna batace uffan ba sanda jud ta gama ta kwaso nasu ta kawo mata
Gaban ta ta jajjera,wanka taje tayi a tsaye ta dawo tana ta satar klllon inna hoping ace mata taxo ta dau wayar ts inna kuwa tana sane tayi banxa da ita,to zauna mana kici abincin,tace toh inna wayar fa?
Inna tace ai baki gama ba,waccan haddar da kika karba beyi min ba nan da bayan ishai in kun sake yin wani kya karbe wayarki jud tayi shiru cike da saibi da jan kafa ta zo ta zauna suka fara ci ahankli tana turawa kamar wata mecin madaci,inna ta matse ko ajikin ta
Diff se wayar ta fara ringing cikin sauri jud ta aje spoon kamar zata miko hannu ta dauka inna ta watsa mata harara,tanaji tana gani yayi ta ringing har inna ta dauuka ta kalla sunan taja tsaki ta maida gaban ta da kyau ta aje " bakince bakiji ba,yau zanga in baki rike wayar ba ko mutuwa zakiyi dum wani me saka ki awannan damuwar sede ya jira dan wallhy baki isa ina sakaki aiki kina labewa kina amsa waya ba,hawaye ne fall idanun jud ta turo abincin abaki kamar wanda zata amar tana tunowa da aliyu kawai ta fasheda kuka,tace inna kaya na fa za'a kawomin..

Cikin kyabe baki Inna tace ai sai suyi sallama..jud tace to ya za'ayi susan inanan bayan kin kwace wayar

Inna Tace ba kuka kukeyi ba ki kara sautin kukan in sunji xasu sani,sake cokalin ta tayi ta kwanta aksa ta cigaba da rusa kuka,sallamar da sukaji ne ya sa duka suka dago kai.
Chapter 63 · 0% Book details