← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 108

Sashe 76

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da mamakin da su safiya suka sha na yiyuwar auren amma Kowa ya kasance cikin murna da farinciki ne aganin su tunda jud ta zamo matar gida aisukam kakan su ta yanke saka an dau hanyar kubutar da su daga xaluncin ramat

Safiyace take ta lissafi da mamakin yadda abun zai kwashe tsakanin ramat da hamida dan tafi kowa sanin sirrin kawancen su But is still same dan harga Allah tana son jud aranta kuma bata damu ba koda zata juya ma ramat baya ne amma dai setayi shiru bata nuna hakan ma kowa ba sabida jiran ganin abunda zai afku nan gaba

Tun asabahin fari bilkisu ta kasa hakuri ta zaunar da ramat ta sanar da ramat komai,..as expected bata yarda ba,duk iya bayani da shedu ta nuna mata amma ramat sanda taji kamar karya ake mata ta dinga dariyar hauka tana cewa ai mafarki takeyi kuma zata farka..

Sunfi awa biyu suna maganan da kyar ramat ta dawo hayyacin ta ta amince da cewa aliyun ta aure yayi ajiyan kuma yar hamidan ta ya aura

Babu wanka bare parking haka ta nufo aiport hawaye sharbe sharbe tana magnganu zak irin na mahaukata,haka ta shiga jirgin nigeria after 3hrs bilkisu ta biyo bayan ta da kayan su da suka bari har da na can saudi...

Ramat Allah Allah take ta iso abuja dan kanta a kunce yake har yanzu kwakwalta da zuciarta bai ma gama daukar maganan ya amince ba
"tace hamida baxataci amana na wallhy wannan karya ne..aliyu baxai taba auran wancan yarinyn ba wallahy karya ne..haka ta dingayi har sanda aka iso.

Su jud kuwa tun da yamma nasu jirgn ya isa a babban luxury international hotel din SA suka sauka amma ba acikin cape town ba acikin babban birnin dubai shima state ne a SA tsarin sa kamar abuja a nigeria yake...

Babban suite me kayan ababen more rayuwa da mini beach da duk wani kayan jin dadi aka kaisu daga shi sai ita babu wulgawar kowa se masu aiki

Tsintar kansu anan ya sa jud ta soma nuna alamar tsoron ta a bayyane,in yana dakin sam bata iya sakewa da shi hakama zata kulle kanta a bayi wani bin seyayi lallabin gaske sannan ta bude mashi ko ta fito,ganin duk ta firgita ya sa ya kwantar da hankalin sa ya danne kwadayin sa ya shiga janta jikin sa yana lallabrta yana kwantar mata da hankli batare da ya mata komai ba.

Isar ramat abuja ko gidan ta bataje ba ta fige mota fiii ta nufi gidan hamida
A Dede lokacin hamdiya ta sa hamida agaba sunfito a shirye zasu je gidan inna yin mata godiya

rututu ta ga masu aiki suna darewa dan da bala'in guguwar masifa ramat ta shigo ababbankade tana kukan hauka tana kwala kiran hamida

"Hamida..hamida..yar fullo..hamida ina kike kifito

Ras ras gaban hamida yayi dukan uku uku da kyar ta samar ma kanta nitsuwa anty hamdiya kuwa dama lokacin datake jira kenan

Tuni ta kama hannun hamida ta ce muje,aikuwa suka sauko tare hamdiya ta hade rai tace waye kemana ihu a gida haka?

Haduwar kicibis sukayi da ramat wacce daga ganin ta kasan agalabaice ta iso,a mugun zafafe suka banka ma juna kallon kallo me wuyar fassara

cike da jan aji da karfin hali hamida ta dube ramat tace lpyarki kuwa ramla me haka?cikin wata irin dakakkiya kuma gigitacciyar murya ramat tace hamida kiyi gaggayawar karyata min zancen dana keji na cewa yarki ta auremin miji,kiyi saurin cemin karya ne ko duniyan nan gaba daya ta san da zaman haukacewa ta.

Tsaki me sa bacin rai hamida taja,tace akan wannan maganan shine ya sa xaki taramin jamaa? kiga yadda kike birkitamin gida da ihu,to mukoma falo mu zauna dan bazan iya tsayawa ina magana ba..

Ramat tace bura uba...an tada miki gida anyi ihun..bana matsawa anan sekin mun bayani ashe ke babbar munafuka ta ce hamida?kiyi gaggawar sanar dani kullin da kika hada tsakanin miji na da yarki..or else..

Nan anty hamdiya ta sa baki azafafe tace or else what?...

wani muguwar harara suka watsa ma juna idanun su kamar zai fado kasa se yanzu ma ramat ta lura da kamannin su..

tace ke malama banyi dake ba da wannan dakikiyar mata marar mutuncin nakeyi ...
hamida kin ban mamaki,hamida tace dakata min ramat..ni ban fahimce kiba yaushe kika dawo?sannan menene kike son sani wanda ban gaya maki ba ya dawo munafurci,a zafafe cikin kuna da bacin rai ramat tace kinfi ni sanin koma minene,ina dai miji na aliyun kike so ki raba ni dashi?

Hamida tace dama kinban ajiyarsa ne dazaki na tambaya na akan sa tace
Inban baki ajiyar sa ba amma ai naga kin sace shi kin ba yarki,koba haka bane hamida?mena ke gani a social media hotunan ki da uwar miji na mena keji?

Hamida tayi rau da idanu tace auren jud akayi,aliyun ki ne ya aureta.. an bashi yata sai yaya?

Wani Ihu ramat ta tsala tace,hamida kika ba aliyu yarki?hamida kincika babban munafuka azzaluman mace bakar muguwa anannmiya makwaidaciya na rantse miki da Allah sai kinyi nadamar cin amana ta da kikayi Nan hamida tayi jefa da jakarta a xafafe tace ramla karki sake ki zage ni,ni banci amanar ki kije ki tanbaye mijin ki shiya gani ya kyasa sannan ya nema ya samu

A haukace ramat ta haura xata watsa mata mari hamdiya ta sha gaban ta..

Cikin ihu da hatsala da bakin ciki me zafi Tace hamida kinci bura ubanki kinci waye waye.. sena kashe ki na kashe munafukan yarki u derseve to die macuciyar banza axxaluma kawai,hamida tace sai kiyi ai..ni meye laifi na in aliyu yace yata zai aura?akan me zan hanasa ni na haife jud amma ai bani bace uban ta da dangin ta ni uwace kawai...

ramat tace uwa me son abun duniya ba hamida kiyiwa Allah ki warware auren nan ko nawa aliyu ya baki zan ruba muku wallahy bazan zauna da kishiya ba kishiyar ma yar cikin ki wallahy sena kashe ta..

A hatsale Hamdiya tace ki kigama rantsuwar ki kece farkon mutuwa dan wallahy sai na yi raga raga da rayuwarki ramat ta juyo Tace ke din wa?in ina magana kina samun baki saina ci kutuman ubanki..

Hamida tace sede muci kutuman ubanki karki sake kizagar min yar uwa aure aliyu ya nema kuma an bashi,..ni ba dan naci amanan ki nayi ba in kin yarda can miki in baki yarda ba kije kiyi duk abunda zakiyi amma kisani dede da tuntuben numfashi yata tayi sena ga abunda yayi bayanki ramla wallh wallah wallh kinji na rantse miki sai na juya miki rayuwarki tun anan duniya,anan duniya zaki dandani azaban dayafi wanda yake jiranki a wutar jahannama

Ramat tana kuka
tace jahannama ai tare dake xamuje na baki xuwa gobe ki san yadda zakiyi da auren nan in ba haka ba duk abunda xai faru da yarki laifin kine

Cikin wata busashiyar darriyar me sa karayar xuciya da cusa bakinciki anty hamdiya tace ga fili game doki saura sukuwa....wacece na sunanki?

Hamida tace barta hamdiya karma ki kulata ta dauka ita wata abunce,nice kike durawa ashar ko ramla?nice xaki cemun zaki kashe yata?yo tunda bazaki nitsu ki saurarani ba bakar kishin ki ya rufe miki ido da kunne sai kije din nikuma na baki kwana daya tal ki kasheni,ki kashe jud nikuma awa uku zan baki ko ki sauraramin muyi magana ko in fede asirin ki ta inda bazaki taba jin dadin sa ba,ramt sena miki abunda sekin gwammaci zama a wutar jahannama da zamanki a duniyar nan sena tona asirin ki,saina sa kotun sharia sun jefeki duk duniya se sun san kinyi cikin shege da aurenki

Ihun bala'i da zaucewa ramat ta fasa muryan ta har na dishewa tace
Wayyoy Allah na Allah ya tsine miki Allah ya tsine miki hamida Allah ya tsine ma xuriar ki sai tasss anty hamdiya ta dauke ta da mari wani hamshakin dambe ne ya kaure tsakanin su kowa tana yagar kowa da zagi

Da kyar hamida ta raba su,ke har kin isa ki tsine mana jaka kaxama karuwa kafurar banza dangin karuwai matsafiya

Tace eh ku kirani koma miye kuma na yarda ni kafurace zakuga aikin kafurci kuwa,tace ma hamdiya ai karuwanci a gindin yar uwarki hamida aka fara tunda ta tura yarta gaban mijina tallan gindi sabida ya gani ya aura,kinyi asara hamida...ai dama seda aka gaya min ke makiyata ce naki amiincewa ashe ma yarki kike tanadawa miji na?..To wallahy kinci karya ki dau buhun kaya akanki

Hamida Tace sede in banso inyi dauriya ba,amma ki tambaya kiji babu me daukar buhun wuta se dan wuta bakince xaki kashemu ba?..Go on..hamida ta fada da tsananin bacin rai..

Cikin wani irin fixga da bakinciki ramat ta juya a haukace ta bar gidan tana rusa kuka sosai

Tafiyar gidan innan da ba'ayi ba kenan
Su ka koma daki suna rarrashin juna kwata kwata hamida ta kasa zama atake atake ta kira shege tace maza tana son ganin sa acikin daren basai safiya yayi ba.

Tsaban bakinciki ramat bata je gidan ta ba hotel ta kama ta kulle kanta a ciki ta dinga kurma ihu tana maganganu dan a duniya bata taba samun abunda ya girgiza ta kamar wannan lamarin ba

in hamida ta juya mata baya ta san ta kade ta riga ta gama yawo dan duk duniya ita tasan ta ciki da bai babu sirrin ta da hamida bata sani ba..kudi ta zuba ajaka tana Allah Allah washe gari yayi taje gaban shege dan ko waya bata iya amsawa tsaban kuka da gushewar hankali

Isowar bilkisu ma bai kara mata komai ba sai tsaban bakinciki dan kuwa babu irin zugin da bata yi ba tanacewa ai dama nagaya maki munafukarki tana tare dake

Tace ma ramat ai nayi bincike sosai kuma an gayamin Da kudi aka sayi kan hamida ta juya miki baya kuma yanzu haka mijin kin ma baya nan kuma tare da yartan suke.
Bawanda yasan inda sukaje

Ramat Tace wai nawa ne aka bata?zan ruba mata shi sau goma in bata ta sakar min miji na dan wallhy bazan iya sa'insa da hamida ba hamida tasan sirrikana masu ban tsoro..
Chapter 76 · 0% Book details