← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 108

Sashe 13

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana daya daga cikin al'adan ta kowani dawowarta daga tafiya se tayi inspecting ko ina a gidan tanayi tana debar musu albarka cikin kaskantrwa

"Safiya ce trusted maid dinta agidan amma hakan be hana ta zagin ta tass ba

"Karshe ma tace duk sunyi kiiba abincin gidan ta suka sa agaba suna ci,anan ma yau cikin daren sanda ta kore me wanke wanke da zubda sharan kitchen..fata fata tayi musu batare da sun mata lefin komi ba

Ramat tamkar bakar guguwace wacce in bata dauke ka ta wulla ka ba to dolene ta shige ma ido kayi hawaye yauma da kyar ta kyale su...

Late nite alhj aliu ya dawo gidan tana sane anma shima haka ta share shi duk dama tana cikin bukatar sa,washe gari da safiyar Allah bata nemesa ba ta dau wanka ubansu ta nufi gidan kawarta hamida..

Tsege tsage alhj abbakr yayi yana ziriya duk ya kasa samun sukuni kallo daya zaka mar kasan ya damu sosai akan lamarin daya afku da shi jiya..

'Yayi bayani yayi korafi amma hamida tana shiru bata tanka shi ba aranta sai yau ta dada tabbatarwa da cewa lallai abbakr yasa abun nan aransa bana wasa ba.

Ita de bata damu da duk abunda xai biyo baya ba,muddin zata amshe yarta shikenan,itama kwalliyar takeyi dan sun yi waya da ramat din akan tana hanya har wani Allah take ramat din ta iso su tattauna,aikuwa ko minti sha biyar batayi ba saiga aikan ramat ta iso a gurguje ta barsa a dakin ta sauko

Wani irin sautin shewar Ahayyye suka buga suna me sauya sanyin iskan gidan da surutayyar me sauti, ko kula kujera basuyi ba bare su zauna

"ramat tace hamida na sami duniya kuma na samo mana wani babban harka wannan karon dole ne kema kije ki wanye..

Hamida tace Allah ko,harkan kudi ne?kamar nawa zan samu?Kawata shafamin mana yaushe zamuje?niko yaune ma na shirya,wani daria ramat tayi tace kai hamida mayyar kudi,to bayanzu bane se abun ya kankama amma na saka sunanki in abun ya kankama ki zamto cikin shiri zamu tafi saudiya tare..,hamida tace oj a saudi ne?wow masha Allah uwargidan kuma amaryan,shegiya buhun kaya majina ahauki a zame ki hau mutum kizauna dede.."na gaban shege uwar gidan kamili,nan ma wani dariyar fitsara suka sake atare suna me tafawa...
Waje suka samu suka zauna inda ramat ta bata labarin komai fa ya wakana a tafiyartan,

evrything seems normal,gwanin ban sha'awa maganan karbo jud ne kawai ya rage musu ayanzu

Sanda Hamida ta danyi leke leken ta ta jawo ramat suna me rage sautin muryan su..'tace ke kawata an fa bugo shi kin min dede,ramat tayi dariar mugubta tace hamida shiyasa nake sonki babu daga kafa harkan cin uban namiji..,hamida tace ina kika ga batun daga kafa bayan an kwace min yata..

So whats next?aliu yasani?

Ramat Tace noo,ai in suka kuskura suka gaya masa ni nasasu aiki wallahy kashin su ya bushe..
Ke?inada makamai na fa in abun yafi karfin mu ai shege yana raye se mukai masa aiki..daga mazajen har macen da aka turo ni nasan sirrin su"..kuma sun tabbatar min cewa bazasu bashi aikin ba sai mun cimma burin mu

Hamida Tace good,
Naga yana ta damuwa ai nide bance dashi komai ba amma tunda kinzo pls lets do shap shap ko jibi haka inje in kwaco yata..

Ramat tace hmm ok
Amma kiban kwana biyu"zokiji wata magana matsowa hamida tayi ayayin da ramat din ta fada mata wani magana akunne atare suka ranbatsa wata shewa suna kyakyatwa kamar zasu shake.

Har alhj abbakr ya fito suna kai,tuni hamida ta dauke idanun ta akansa ta hade rai itakuwa ramat da kyar ta gaishe sa dan kuwa ita mace ce meji da girman kai da iya raina kurwan dan Adam

Ko awaje ne ta hada da mutune In ance hajy ramat ina kwana..,to baxata amsa ba seta wani kankance idanun ta cikin yatsinawa ta dube gefe da gefe sannan ta amsa can kasar makoshin ta,shikuwa alhj abbkar ko ajikin sa be sake kulasu ba ya saka kai yay waje dan babu abunda ke damun sa ayanzu illa ya samu me shiga masa gaba wajen maganan contrct aproval.

For sure ya san matsalan badaga shi ko aikin sa bane,aransa ya dauka kawai dab anga baida arziki ne ake neman abama masu ido da kwalli

This time har gida ya biyo ma aliu sede baici sa'a ba ashe ma aliun ya riga ramat fita agidan da safen nan ma ce masa akayi yabi jirgin dubai a gaggauce.

Haka yy tagumi Daga ya kira wannan sai ya kira wannan Yayi iya kokarin sa
har yasoma jin kamar baida mafita face ya nemi taimakon alfarma wajen contrctors din kai tsaye inyaso kota nan xaisan asalin bukatarsu, he really need the job yasa abun aransa sosai,kuma yasan irin wannan kudine kawai ze samu martaban sa ya dawo a idanun jama'a harma da matarsa hamida

Zuwan sa ofishin su sai yanemi waje yay zaman dirshan yana jira amma haka suk dau lokaci basu bashi izinin ya shigo ba,wani bawan Allah ne dai yaja sa gefe ya temaka masa da bayanai yana me warware masa kan labarin

nan ne ya fahimce cewa da saka hannun ramat acikin zancen..ai a saba'in ya tarkata takardun sa ya dawo gida da niyyar yima hamida magana akai amma sai yaga ta bore tana fixga kamar bazata taba sauraran sa ba.

Duk zumudin sa haka ya daure,sai washe gari dayaga bazai iyaba sai ya daure ya sake zuwa dakin ta ya same ta da maganan,.
"yace hamida naji ance kawarki ramat tana da ikon fada a ji a harkan kwanglar nan why not ki shige min gaba a wajen ta sai ke kiyi mata magana pls i really need this job,.'da wutsiyar ido ta wani kalle sa "Hmm kawai tace fuskn ta ba asake ba,shikuwa be gasa ba roko akn roko da taga ya matsa akab maganan ma sai taja tsaki ta hau fada "nifa bansan komai ba aise kayi hkri in naje gidan ta
Zan tambayo ta..

Daganan Baice komi ba har tagama shirin ta ta fice wajen ramat din

Da alama wani wajen zasuje yauma dan bakaramin wankan gwalagwalai da manyan leshona sukayi ba

Ramat luxurious Quest house suka dosa,inda suka hafe da sauran manyan mata sukayi harkokin su na siyasa da kudi

To bayan duk anwatse ne suka fara nasu maganan
Kaf yadda hamida suke ciki da abbakr sanda ta bayyana ma ramat

Ramat Tace hamida kije yau in ya sake kawo miki
Magana kice masa eh nine me hanyar shiga wajen contractors amma daga yau nabaki ragamar komai a madadi dina ke kyasan yadda zaki langwasa sa

Hamida ta amsa da toh suka rabu،to koda abbakr ya zo neman jin kan maganar Sanda tamai rigima taja masa rai sannan ta fada masa ai ramat din ma ta bata ragamar komai,yace alhamdullhi yana me jin sauki aransa aganin sa basae ya roki hamida ba zata taimaka masa

Sede ba haka ya gani ba,tsabanin abunda yake tunani aransa yau hamida ta bayyana akan fuskan ta afili ta fito tana me nuna masa cewa gaskiya bazata taimaka masan ba

Farko Abbakr ya dauka wasa take mashi dan taga ya matsu da abun amma da yaga ta mike dagske tana fetsa masa maganganu masu zafi se yayi shiru ya zuba mata ruwan idanun sa cikin mamakin ta

Abun yana matukar damun sa in hamida tana duban tsabar idanun sa tana ci masa mutunci akan abun dunia,zuciarsa na yawan karyewa baiso ace ma se ya tambaye Alfarman taimako wajen kowa ba,yasan yau da'ace aliu yana nan duk haka baxai faru ba...wato a dunia in kai bakomai bane ka shiga uku,..da jimami ya fice ya barta a dakin bai iya yin musu da ita ba dan sosai yasa aransa koma yaya ne zaiyi kkri ya amsa duk wani walakanci dan ya samo wannan kwangilar.

Samun Kwangilar nan dede take da samun wani baban sauyi a rayuwar sa
Musamman akan auren sa,abokan sa, da sauran yan uwan sa da sukayi nesa dashi dan anga baida komi yanzu

Yasan dai kwangilar billions ake magana amma be san nawa bane asalin nashi kason aciki ba,harkan hulda da uban kudi wani abune mai dauke da protocols duk dama yasan badan damar ta hannun aliu ya fito ba da har abada
Bazaiji qamshin wannan arzikin ba.

A Fannin ramat tana iya bakin kkrin ta dan kar aliu yaji zancen wasan da suke shirin bugawa akan abbkar

hasalima babu abunda ya hada ta da kwangilar dan samun irin wannan damar yafi karfin ta

Kawai dai tsaban makirci da iya yin ma mutane talala yasa ta kalmashe bakunan aproving supervisors wanda dama sune zasu danka masa kwangilar da kudin aikin duka a hannun sa

Ta gargade sune ta hanyar musu barazana da boyayyun laifukan su data sani

Ramat zata iya yin komai akan kawarta hamida

Shiyasa tun bata dawo nigeria ba ta miko bukatun ta wajen wakilan kwangilar,ita ta gaya musu yadda zasuyi su walaknta abbakr ta inda zai karaya ya amsa musu bukatun su batare da kowa ya sani ba.

Hanklin Abbakar bakaramin tashi yyi ba,musamman dayake shirin ganin babban daman kwato yancin sa kenan kuma gashi zata kubuce masa

Duk ydda ya sauke kansa hamida taki ta duba,nuna masa takeyi bata yarda da shi ba...

Da shike ma ramat tasan abbkar me adalcine da son gaskiya sai bata
Damu da sanin adadin yawan kudaden da zai samu ba so hamida ma batada masaniya akan amount din albashin sa.

Burin ta kawai ta kwaco jud,dan ta bala'in yarda da kanta inde akan shawo kan namiji dan samun wani abun dunia tasan ita shedan ce.

After 2 days ana washe gari deal din zai yi expire akan sa

To in har ba'a kirasa yau din ba to tabbas yasan an bada wani
Nadaban kenan

To ko bacci baiyi ba bare yaci abinci gashi har yau babu aliu babu labarin sa ba,anan ne kuma su ramat suka hada takardan Deal me zafi akan jud yana kwance a dakn sa
Saiga aika.

Tsaf ya bude ya karanta..ya gane daga ofishin hamida rubutun ya fito

"Tace in ya amince da dokokin ta bama sai ya sake zuwa gaban kowa ba za a damka masa komai
Chapter 13 · 0% Book details