← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 108

Sashe 55

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Jud,nasan zakisha mamakin yadda rayuwa tayi dani a matsayi na na wanda yaci ace ya kasance miki uba me kare mutunciki da nemo miki farinciki a duk inda yake, shi kansa kunci wani abu ne wanda yake da matukar azabtarwa ba kamar damuwa bane da zai iya nunawa akan fuskan dan adam anjima kadan ya washe.

" ki yafe ni...kiyi hakuri...nayi wasa da wannan darajar dakika ban na matsayin uba me kare ki,na bada shedan kofa ya sa nayita aikata abubuwa dake which im sure i did it with good intention

.so nake na samar maki lpy But to tell you the truth inaji ajiki na cewa na sa sonkai aciki wajen samar makaina sauki game da matsalolin dake cikin aure na

Kuma Ke Baki da laifin komai dan na dade da lura kin biye min ne sabida baki da wanda zai taimaka miki akan abunda ya dade yana gurbata rayuwanki ne

..i swear to you wani lokacin nima bana sanin mena ke aitakawa but one thing im very sure of now is i love you.

Kuma bana so in ci gaba da lalata rayuwarki,bana son incigaba da cin amanan iyayen ki,tunda har kin same lpya ina ganin babu amfanin boye miki sirrin zuciyata i want yoy to forgive me pls..Jud Kina da matukar kyau amma ba zallan shi yau nake nema ba, Ba sha'awar ki kawai nake kwadayin ji ba
Ina so ne nakasance dake a rayuwata ta har abada cikin aminci da mutunta juna da karemin dukiyata kamar yadda kika fara nunamin cewa zaki iya ayanzu

Dada sunkuyar da kansa yayi ya sauke nannauyan ajiyan numfashi yace jud,banso na gaya maki sirrin aure na ba but im despretly in need of ur help today,kuma dukkan kulawar ki yardan ki da soyayyar ki kawai nake so ata wannan fannin.

"Dada suke idanun shi yayi kamar wanda baison furtawa yace asalin sunan matata ramlat david matori,a gombe dai na auro ta amma bazan iya ce miki nasan ta ko bansan ta ba, kawai tsintar kaina nayi da qaddarar zaman aure da ita,kuma tana so na nima hakan nakeji akan ta,ajiyan zuciya yasauke again,daga nan bit by bit ya shiga bata labarin rayuwar auren sa da ramat duk dama ba duka ba amma fannin rikicin hanasa aure har mutuwar fatima da duk abunda ramat din tayi na kaucar da samun kwanciyar hankli arayuwar sa akan aure duk ya fayyace mata bai boye mata komai ba

Yace u see My wife,has not been there for me kuma taki jinin nayi mata kishiya,kuma ayau ko naje mata bama yawan karewa ta dadi.

She feel like ni nayi arzki ne bana son itama tayi,but u know kowani namiji yana bukatar matar sa ne dn tana kulawa da shi sosai,and i despretly need that kulawa too gaba daya hakuri na ya kare..ina cikin matukar bukatar kulawar mace arayuwata..not just for my sexual urges but for my marital responsiblity inaso in same me tallafamin,me ban shawara ina son wacce zata kasance agefe na

Ki dauka kamar yadda ciwon ki ya dade yake damunki tsawon lokkaci baki da mafita kuma babu wanda ya nuna ya fahimce hakan nima nake zaune da matata cikin matsi da rashin son in jefa kaina hanyar da baidace ba,but i dont know what happen with you and me.

Jud Naga mata kala kala arayuwata
,amma bantaba aikata irin abunda na aikata dake ba
Daddys princess Zaki yi hakuri kibani dama in gyara kuskure na?

kekam nasan zaiyi miki matukar wuyar amincewa da hakan kar ki damu da komai basai kin amsani yanzu ba take ur time nd think,nine na dade ina tunani akan hakan kuma ina me tabbatar miki da cewa zan iya yin komai dan na mallake ki arayuwata shiyasa dole ne ya zame mun in bayyana miki yau,jud Nasa kaina cikin kunci da bakin ciki a lokuta dayawa kuma nasan hakan ma ya cutar da ke,i just hope zaki mance shi ki yafe ni?

"Wani jan numfashi jud tayi har makogworon ta Bayan tulin hawayen datayi tayi tana sharewa wani Murmushi ne ya kufcee mata sannan wasu Hawaye masu zafi suka sake tuttulowa ayayin datake girgixa masa kai batare da ma ta sani ba, a sanyaye ta shiga tarewa tana kallon hannun shi daya dada rike ta warware diamond band din ta makala a hannun ta me nuni da alamar amincewarta akan soyayyar shi,kuka takeyi da alaman ta rasa me zata furta ne one time taji kirjin ta yana kuma bugawa Ta dage idanu tana ta kallon hannun ta tin kafin ta gama concluding abunda ke ranta...aliyu ya kalle ta Gwanin ban tausayi yace jud kin yarda da ni?kin amince da soyayyata kenan ko?...ban miki alkwarin komai zai tafi mana dede ba ina fata kin fahimce matsala ta?Fatar gobe inna aikata wani abun kece ta farko da zaki fahince ni ki kuma bani uzuri?
Gyada masa kai ta takeyi tana tarar hawayen ta yace
I really cant thnk straight wallhy ba haka nake ba nakanji bana son abu ba daidai bane amma sai naga inayin shi...

Kuma Bayan mahaifiyata kece kawai nasan zaki taya rayuwata da addua kece zaki dawo min da haske
,da neman sauki

when m with u i feel happy,inajin sauki akaina inna zauna nakanyi tunanin kasancewa dake a matsayin matata..

Jud Ina son ki sauya min rayuwata
Ki kawo min sauki me dorewa axiciyata kinji?
...dan na lura dukkan dukiyata da tarin sanayya ta bazai samar mun da komai ba face rudin duniya da cigaba da aikata abun kunya.

Hawaye take mashi kamar wacce ake dukan ta arude ta sulale gaban shi tasa knee din ta ta sunkuyar da kanta at sanyaye tana mashi wani irin kukan tausayi da nuna tsantsar kaduwarta akan labarin rayuwar auren sa

Ji yayi hawayen ta na tsokalo masa nashi kamota yayi tareda daura kanshi akan kirji ta ya rungumeta a hankali tace
"thank you hamma aliyu.."tayi kissing dinshi muryan ta adishe ta kuma kankame shi ta sake cewa
"thank you for sharing ur burden with me"..wallhy basai ka tsanan ta min bayani ba,nikam na fahince ka,na dade da sanin kai mutumin kirki ne...ni banda karfin ikon hanaka zuciyata dan Allah ya riga ya mallaka maka shi tun ranan dana fara saka idanuna akanka

Dukkan abunda kayi min arayuwata,mai kyau da marar kyau dukkan su na karbe su hannu bibbiyu kuma Allah shikadai zai saka maka..

And..and i promise to do anything for you daga yau..nama alkwari

Kadauka ni yarka ce dan bazan fasa baka girman da ka cancanta ba,haka ma ni budurwankan ce dan bazan fasa baka dukkan soyayyar da ka rasasu abaya ba,zan tsaya maka duk rintsi duk wuya,in har addua ns sauya qaddara sai ya sauya mana namu har na kasance matsayi na matarka na har abada,i love you too daddy..im ready to take any risk dan in faranta maka. .i promise you

Bai amsa ba yabi dukan hawayen nata da kiss kafin chan ya saketa ya mike yana kallon fuskar ta me cike da tsananin nuna yarda da so, maida masa mumurshi tayi duk idanun ta sun haura sunyi ja tsabar kuka"ya tallafo ta ajikin shi yana me fadada murmushi yace its ok
" Allah ya maki albarka babyn d...a matukar kunyace tace Ameen sai kuma ta fada jikinshi da kyau ta rungume sa sosai tana mai sauke nannuyan ajiyan xuciya mai nauyi

Ahankali ya cirota daga jikinshin wani abu ya danna kalan wutan dakin ya komayin hske sosai,batare dayayi nesa da jikin ta ba ba ya mike tsaye tare da ita a hannun sa,sama ta daga ido ta kalla tana kallon wutar dake neman kashe mata ido a hankali ya daura hannunshi kan fuskntar ta ya shiga goge mata sauran ragowar hawayen

Kamo hannayen ta yayi suka zauna abakin gadon suna me sauke idanun su akan inda kalman i love you din ta fito
Cikin fargaba da damuwar shiga sabon taku a rayuwar su kowa yake ta sakawa da warwarewa.

Dan Matsalan jud baifi yadda zata fuskance iyayen ta da mutanen duniya ba.

Me zatace da abban ta da ya kasance abokin aliyu,uwa uba amynta data kasance aminiyar matar sa?

Tasan hala duniya zatace tazo har gida tayi kwace ma mijin mahaifiyarta,tunda dai da hamida da ramat kowa yasan ba wani bambaci suke da shi atsakanin su ba

Shin Me zai faru in har tace yau aliyu zata aura?me wannan maganan zai jawo ma iyayern ta,inde kishi da qwabzawa da ramat ne ita tasan ta inda zata bijiro mata da wayo, amma zumuncin su na iyaye dake zagaye da al'amarin shine yake matukar bata tsoron fara tunkarar sa a ziciyarta

Anata fannin ita kadai tasan cewa bazata iya kufce soyayyar aliyu data dade tanaji aranta ba

Kuma aliyu ya zame mata tamkar katanga alokacin da bata da rufi,ya kare sirrin ta ta hanya mafi wuya ya dora jin dadin rayuwar ta fiye da nashi ya bata dukkan so da yarda,ayanzu haka bata da wani uzuri ko dalilin da zata bayar nakin kasancewa da shi

Tasan labarin qaddarar auren sa na baya akwai sa tausayi da abun al'ajabi amma haka kawai taji labarin be kara mata tsoron komai ba face karfin zazzafar soyayya da tsananin tausawarta akan shi.

She feel like she can
Pull Throu the worst akan shi,ayau ne ranar da ta dau alwashin samar masa farinciki da kwanciyar hankli tanajin aranta koda jikin ta ya nema bazata taba iya hana sa ba.

But she like it this way dayace bazasu sake irin waccan rayuwar ba,rayuwar rashin da'a da rashin kiyaye dokokin ubangiji wanda suka daukar shi hanyar samun sauki Inde za'abi gaskiya takance laifin duk nata ne,ko game da labarin dayagama bata na yadda yake ji arayuwan sa na rashin gane daidai da aikata sabanin tarbiya hala zai iya zamtowa matsalar auren sa ne ya jefa sa aciki,koko rashin samun kwanciyar hankli koko damuwa da yawan tunani,

Amma itafa? Bayan matsalar ciwon sha'awar nan bata da wani damuwa acikin hanklin ta take kasancewa fiye da shi..
Chapter 55 · 0% Book details