← Book details Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 108

Sashe 74

Kudi Kumbar Susa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ana saura kwana uku aje sokoto anan ne hamida ta hada wata arniyan liyafa a wata boyayyan hotel inda ba kowa zai iya yazo ba sede special iv,A hakan ma zokaga mutane anyi wankan gadara da nuna arxiki
...daidaiku daga dangi da yan uwan aliyu duk sun halatta

Amarya tayi kyau duk dama arabian gown kawai aka saka mata taji kwalliya da red lips stick da gwala gwalai gwn dinta black colour da transparent alkyabber silver colour me kyalli

tsaban ana kakafa da bikin se ba a amince da kawaye ba mariya ce kawai take wajen a gefen ta

Haka akayi kawataccen liyafa me cike da dumbin tarihi,mother and doughter moment da sukayi gwanin ban tausayi wasu har hawaye sun taya su zubdawa.

Anci an sha ansha shagali sourvenires din da aka bayar ma kansu abun kallo ne
Dan bakaramin xuba kudi akayi ma hidiman ba.

Aliyu tun ba ayi rabi ba aka kusan cika masa hotonan amarya awayar sa dan acikin dangin sa da sukaje babu wanda bai dau hoto da amarya ba

Shigowar sa site din matayen sarki ya samu duk maganan walimar akeyi,shidai he cant wait ayi auren nan gani yake kamar gobe bazaiyi akawo jud sokoto ba

Anan gidan sarki Hatta side din da su hamida zasu zauna an tsara sa anyi masa wani irin ado na sarauta,komai red and golden an dake wajen da amarya zatayi sakun lalle da kawatatun royal sitting carpets da kujeru da labulayen zamani

Duk wayanda zasu rufa musu baya hamida ce ta biya musu kudin jirgi,manyan
Kawayen anty ham diya,da itama nata kawayen gudu uku se inna danata ayarin su bakwai ne tsoffi.

mariya ce kawai tare da jud,dan anty maryam dama tace ita zata zabo kawayen haya guda biyar kowacce za'a mata anko da komai da komai acikin kudin ta wanda sune zasu zo su rufa mata baya ranan royal night daga an gama sai a sallame su

Ana Washe gari zasu tafi hamida da hamdiya suka fara kimtsa kayayyakin fitar amarya da suka siyo wanda zata sa ata nasu fannin,sun barar da kudi ne sosai dan sam basu so azo araina musu wayo So all kinds of matrials da laces sun hada su ne filtered by 11 colours kowanne da kalan ababen wuya da hannu da jaka da takalmin sa
black,grey,purple,cyan,blue,red,green,brown silver gold yellow se white da off white

Acan kuma sokoto kayan dubar da hjy binta da matayen sarki suka cire ma jud shine wata _metal chantilly embroided lace_ me kimanin 169us dollers per running metre

Na royal nite aka cire acikin wata
_Silk jacquard fabric_ me kimanin 305euros per runing metr

Ranar da zasu taho da amarya sokoto make up arttist biyu ne suke kula da jud,
Wani iriyar perfect nude make up aka mata sabida yaune zata fara ganin sauran dangin sa hamida tace kar acika ma fuskn ta kwalliyar shirme,sosai jud tayi kyau aka mata dressing da wata A line gown wanda akayi scattering ko inan sa da sequins.
Aka sambada mata babban mayafi me shegen tsada

Ranan gidan sarki sultan babu masaka tsinke dan tun kafin jirgin su ya sauka aka aika convoys na subaru da alfa romerio domin a debo su duka

Babban jeep din GTR dake wajen shi daya tal ashi aka dauko amarya ita dayan ta a baya se security agaba da driver su.

Side din da aka tsara domin su baida nisa da asalin side din matayen sarki,so kafin abasu masauki sanda aka kaisu fada sukayi gaisuwa ma sarki da sauran manyan wakilai dake zagaye da su,idanun aliyu kar yake akan jud dan duk wani motsawarta yana lura duk dama mata ne fall zagaye da ita

jakadai masana kirari yan san ayi kwakwafi ga iyaye da yan uwa kusan kowa yana son yaga fuskarta akaro na farko,haka anty hamdiya taki sam ta basu wannan damar har sanda suka gama gaishe gaishe da manyan mata aka kaisu site din su suka nitsu ababen tabawa da akayi ziryan sa barama su iya kirgawa ba,da yanma bayan asar
Masu sakun lalle suka fara shiryawa

Asalin atamfar holland ja me diso dison ruwan toka aka sa ma jud tayi kyau dinki na Ajin farko ce..

Hamida da kawayen ta da inna suna can ciki suna jan girman su,anty hamdiya ce aka barta da sa ido akan duk wani hidima,part din da aka shirya domin sakun lallen babba ne sosai dan haka mata da yan mata kowa ya halarta
anata hira ana raha ana annashuwa.

akan wata kayataccen dadduma kowa ya zazzauna makadan kwarya da masu turaren wuta sun ruda wajen da salon su na raye raye

،..jud tana zaune a tsakiyar su a lullube da babban mayafi tun kan afara mata lallan ake ta daukar hotona su anty hamdiya da su anty maryam duk anan suka hade anata ban dariya ana zana ma kowa zanen lalle a hannun sa.

"Babbar jakadiya ce tayi jagora akai kai jud cikin wani killataccen daki inda aka sa ta canza kaya aka bata wani kyalle ta daura a kirjin ta,shima half ba har sama ba wani abu me sanyin qamshi suka goge mata jikin ta da shi sannan matar ta kwaba wani iriyar lalle me kamar dyes me shegen qamshi,".. Suka sa ta juya musu baya inda suka sauko da kyallen gaba daya ta inda gadon bayan ta ne kawai zai haska,"

a fresh and smooth sexy back dun ta matar ta nemi spot me dauke idanu ta zana wata shegiyar flower me dan tsayi a kallon bugu daya zakace tatto ne...
zanen yayi matukar haskawa sabida fatar jikin ta ya gogu yaji gyara yana fidda wani irin kyalli,sanda aka barsa ya sha sannan ta umarce ta data ja kyalle saman kirjin ta,jud taki sam a mata kwalliyar a kusa da saman nono inda aka mai dashi gefen wuyan ta bakaramin kyau yayi mata ba

Gefen wuyarta da bayan tan gaba daya suka sauya mata kammani suka kara mata kyau

Seda aka bari suka bushe aka wanke sannan aka barta ta maida kayan ta sannan ta fito wajen taron mata,guda ne sauti aka cika wajen da shi kowa yana so ya daukar gefen wuyartan daya haska sosai dan basuga na bayan ba

Nan aka xaunar da ita a tsakiyan su,wani irin waketa makada sukeyi mata na amsawa anty hamdiya tana dauka a video kamar zatayi hawaye tsaban dadin datakeji aranta,"anan aka fara mata zane a hannu da kafa aka bita da qamshi ita kanta jud bazata iya kirga sau nawa aka dauke lallen nata a hoto ba,she wishe ita zata fara tura ma husband to be din ta amma ta riga ta san su anty maryam zasu rigata dan tun xuwar su suke ta neman su sata dariya
..su Ahmad da ashna duk sunzo wajen ta..sai can da yanma lis wajen bayan ishai aka watse bayan ancicci abinci an shagultu,

At arnd 10 na dare aka kira su family dinner a 45 inches babban royal dinnig table maxa da mata da yaran gidan kaf suka fito Xallan familyn aliyu ne dana sarki sokoto

Yan matan ne Suka shirya cin abincin Nan ne ake shirin nuna ma amarya duk wani muhimmiyar mutum acikin dangi

Wani sabon wanka akayi ma jud aka shiryata tsaf cikin wata kafurar Flowing chiffon gown with long sleeves and voluminous bow at the neck

Dake kawaye are not allowd se awajen program Mariya ce kadai ta saka yellowish colour Straight dress with ruffles ta tsaya agefen amarya Su inna kam suna site din su sam basu xo wajen ba

White Coctail dress made of lame hamida ta saka sukuma su anty hamdiya da kawayen ta suka sa asalin short evening purple gown paired with orgendy skirt

No one can deny that sunyi matukar haduwa,musamman uwa da yarta da babu wani maraban haduwar su dan hamida tana da asalin kyau ne me dauke hankali

Gashi komin su a nitse cikin jan aji
Hakan ya dada kara masu kwarjini na musamman a idanun familyn sarki dana aliyu

Kowa aransa yanajin son ya hada zuria da wayannan yan gayun anyi gulman iya wankan su da qamshin su har sau ba adadi.

Burin hamida ta nuna musu itama tana da shi,kuma zata iya kashe shi abanza dan koda wasa bata so aje araina mata yarta.

Aikuwa hakan yayi matukar tasiri dan bakaramin darajar su da kimar su aka gani a gidan ba

A tsakiyar hajy binta da matayen sarki aka saka jud ana nuna mata kowa da kowa suna gaisawa including su rukayya kanwar amarya fatima ex wife din aliyu data rasu a hannun ramat,duk sanda rukayya ta kalle jud hawaye take saukewa masu rauni amma a boye dan babu tantama hakan yana matukar tuno mata da yar uwanta fatima

Jud kuwa Da kyar tayi loma biyu na abincin,altho seda akayi kusan rabin awa kafin aliyu ya shigo cikin su,aikuwa yana yaba kwaliiyar jud awajen xo kaga murmushi da kwament ta kota ina masu jin kunya suna ta kau da ido suna gyaran murya sede shi bai wani dade anan ba ya fita gashi Yayi matukar kyau duk dama ba manyan kaya ya saka ba sede kalar dark blue ce kuma ta haska shi sosai

Tsaban abun ya kawatar har aka bar wajen ana hira me sa dariya da ban nishadi kowa ya nuna farincikin kasancewa da su hamida acikin zuriar su uwa uba kyakwar amaryan su

Bayan an gama an watse haka hamida tayi babakere wajen hana kowa ya dame jud dan kuwa inna tana gama sata sallahn nafila suka sakata yin bacci da wuri

Hakan ya balain taimaka mata dan bakaramin stress din mutane ke yawo mata akaiba.

Gashi gobe royalty night,tasan hidiman sarauta..

Washe gari sasaafe suka yi salla suka hau kimtsa ta tun kafin ma a fara musu sallama da gaishe gaishe
Ko su inna ma sun lura da cewa kowa xumudin bikin yake a gidan,annashuwa da farinciki gaba daya ya cike fuskan kowa.

Dake hidiman na dare ne sun samu enough time na hutawa kaya daba daban kala takwas aka saka ma jud daga safiyar zuwa bayan ishai da zaaje hotel yin progrme din.

Abbakar yana abuja shirin daurin auren a gobe shi baixo hidiman auren abokin sa surukin san ba sabida nauyi da abun yaxo ya fara masa shima
Chapter 74 · 0% Book details