← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 67

Sashe 8

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da daddare yana bacci yaji kamar ana taba shi. A tsorace ya tashi ya lalubi fitilar gefen gado. Zaune ya ganta ta dora pillow a cinyarta. Sweetheart ka tashi muyi magana game da birhtday din Nana. WHAT??? Shine abinda ya iya fada a hasale. Izzatu tace maganar birthday din Nana nace. Ya nuna mata agogo Izzy kinga time fa, uku saura na dare. Ta dan kwanta a jikinsa kullum ina son mu tsara komai baka dawowa gida da wuri. Jikinsa ya janye sannan yace saboda haka sai ki tasheni da tsakar dare? Haba Izzy! Tashin miji ayi magana a irin wannan lokacin ai sai a film. Indai maganar kirki ce ai ido biyu ake yinta. Ni naga irin haka is normal tsakanin couples. Idan abu na damun daya sai suyi discussing at night. Kasan kuwa na sake ganin yarinyar da kuka yi fada saboda ka watsa mata ruwa. Ashe kanwar Faiza ce. A wannan lokacin Hamza ji yayi tamkar ya saka ihu. Fuskarsa ko kadan babu annuri yace yanzu Izzy ki tasheni a tsohon daren nan saboda zancen birthday sannan ki ce kinga yarinyar nan? Did I ask you? Gobe meeting gareni da sassafe kuma na fada miki. amma sai kika zabi yanzu ki hanani bacci kuma ki bata min rai. Kallonsa kawai take yi....yau me ya sami baby dinta yake irin wannan fadan. Shi kuwa Hamza banda bacin ran gani yayi dama ta samu na bin umarnin Mama a soke maganar party. Yace ki manta da maganar wani party don an dena. Kina iya dafa abinci ki kawo a kai asibiti ko makarantar allo sadaka. Wannan karon ita ce nata ran ya baci. Wace irin magana kake yi ne? Yarinya duk na gama sa mata rai. Har kayan da zata saka ranar duk na gama siya. Hamza yace indai kaya ne ko gobe ma ki saka mata. Izzatu ta soma hawaye kada kayi min haka Hamza please. Yace meye na daga hankali, shekara biyu zata yi ai ba wayo gareta ba. Hawaye take sosai ya rungumeta yana rarrashi. Tace indai don na tasheka ne kayi hakuri amma kada kasa yan gidanmu suyi min dariya ko aga kamar baka da kudin ne. Bai san haka suka daukaki abin ba sai yanzu. Yace na gama magana Izzy no more parties. Ki duba a family dinku mai bukatar taimako sai mu bashi jari. Su Mama basa son abinda muke yi kuma nima na fahimci kuskurenmu. Ai ture shi tayi ta tashi tsaye. Dama nasan zugoka aka yi tunda ka fara magana. Na rasa meyasa 'yan gidanku basa sona. To wallahi sai anyi ko kana so ko baka so. Hamza yace ni kike fadawa haka Izzy? Yau daya don na hanaki abu shine zaki nuna min ban isa ba. Ba tare da ta bashi amsa ba ta fice daga dakin harda buga kofa.

Kansa ya rike ya zauna a bakin gado. Lallai yayi sakaci da har abin ya kai haka. Dole ya nemi yadda zai gyara gidansa don a zauna lafiya. Cikinsa ne ya murda alamun yunwa. Yau kamar sauran alhamis Izzatu batayi girkin dare ba. McDonald's tayi musu order. Soyayyan dankali aka kawo musu da kaza harda Tala da maigadi. Ko kadan Hamza bai koshi ba sai dai an saba irin haka wanda tun kafin suyi aure yayi mata alkawarin ware rana daya a sati kada tayi girkin dare zasu rinka ci a waje ko ayi order a kawo musu gida. Tashi yayi ya bita dakinta sai dai a rufe yaji dole ya koma ya kwanta. Da kyar ya iya bacci saboda yunwa.

Washegari saboda tana fushi bai sami breakfast ba. Da yayi magana tace ta dena girki sai ya janye maganar party. Shi kuma yace ta bashi atm card dinsa na wurinta maganar soke party babu fashi. Baram baram suka rabu. Har mamanta ta kira a waya ta fadawa tace kada ta damu idan bata da kudi ne zata turo kaninta ya kawo mata.

Hamza gani yayi an cigaba da shirye shirye. An siyo katons din lemo da ruwa. Ga gifts duk an gama hadawa a wata jaka mai hoton Nana duk an ajiye a store. Ya sake wa Izzatu magana tace ai ba kudinsa bane. Maganar Mama ya sake bi ya kwashe yaran ya kaisu gidansu.

Su Hajiya sunyi mamaki da farinciki ganin Hamza yaji maganarsu. Aka sa Ibrahim dasu Mariya suka kawo nasu yaran. Tuni su Khalifa suka saki jiki cikin yan uwansu. Idan suna Hausa sai ka rantse daga turai suka dawo. Kwatakwata basu iya sosai ba ,sai turanci. Nana kuwa dama bata iya magana sosai ba. Tunda suka zo ta likewa Adabiyya take kiranta Anti Adab.

Izzatu tayi mamaki da ta dawo daga supermarket ta tarar yaran basa nan. Tala ce ta sanar da ita sun fita da daddynsu. Sai dai tasha takaici da ya dawo shi kadai yace a can zasu kwana. Tasan saboda maganar party ne. Tayi ta rokonsa da koke koke duk a banza. Har zaunar da ita yayi yana mata nasiha amma ta kafe. Shi kuwa yace indai zata iya zuwa gidansu ta dauko yaran shikenan. Bata san gatse ba ta tafi ana sauran kwana biyu sai dai ta tarar duk sun tafi Kumo. Babu kowa a gidan sai maigadi. Kuka kam ranar ba'a magana. Izzatu tayi fushi sosai da Hamza tare da alkawarin sai ta rama duk ranar da dama ta samu.
[9/25, 3:31 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿13

Batul Mamman(Mrs)💖

Fada sosai Hamza da Izzatu suka yi sai da kyar ya samu ya rarrasheta suka daidaita. Amma kudirin ramuwa yana nan a ranta, dama kawai take jira.

Kusan wata biyu suna zamansu lafiya. Architect Hamza na kokari wurin cigaba da kulawa da iyalinsa. Su Hajiya ma yana wadata su da abubuwan bukata. Hatta kawunsa da aka kora aiki sai da ya aika masa da dubu dari. Hajiya taji dadi sosai har waya tayi masa abinda bata yi sai da dalili saboda dan fari ne tayi masa godiya. Wannan wayar tasa shi jindadi mara misaltuwa. Shiyasa ya cigaba da yin abinda zai kyautatawa iyayensa. Itama Mama taji dadi ya dauki shawararta don Izzatu bata nuna musu bacin ranta game da tafiyarsu Kumo da 'ya'yanta ba.

Zuhra an gama koyon saka Baba ya kukuta ya siyo mata injin saka tsoho ne ma amma bai lalace ba. Tayi murna sosai shiyasa sakarta ta farko shi da ummanta ta fara sakawa rigunan sanyi masu kyau da kauri har uku uku. Duk da suna tsokanarta taki karatu amma sakar tayi kyau sosai. Umma ta bata shawarar duk lokacin da aka bata kudi ta sayi kulu tayi sakar ta ajiye kafin lokacin sanyi tunda ya kusa sai tq sayar.

Wata rana Hamza ya fita zuwa gidansa da suke shirin komawa tun safe saboda aikin yazo karshe. Gida ne da ya tsara komai na ginin da kansa sannan kamfaninsa ke ginin. Izzatu tana kitchen yayarta dake aure a Alaska ta kirata a waya. Suna hira ne Izzatu ke tambayarta ina yaranta. Zeenatu tace sun fita da babansu siyan kayan da zasuyi amfani dasu na HALLOWEEN. Izzatu tace kai sis har kin tuna min lokacin da muke siyan namu da Daddy. Gaskiya ba karamin missing America nake yi ba. Zeenatu tace ba kinga dan fillo duk kin rude ba. To amma meyasa bakiyi a nan? Hmmm kinsan yan Nigeria da kauyanci kada ma yan kauye suji labari. Gidadancinsu yayi yawa...ko kin manta yadda muka yi da inlaws dina game da birthday din Nana? Zeenatu tayi dariya haba Juliet din Romeo duk soyayyar taku har zakiyi korafi. Ba haka bane sis, abin ya bani haushi sosai. Amma gaskiya zamuyi halloween this year. Ba don yana wani aiki ba ai da dole mu taho sai muyi celebrating tare. Zeenatu tace muma zamu taho nan da December a gida zamuyi new year.

Bayan kwana biyu da wayarsu zancen halloween ya tsayawa Izzatu a rai. Lokacin da suna Canada da iyayenta suna celebrating tare sa sauran turawa. Nan da nan ta fara shirye shiryen yadda zasuyi nasu a gida. Hamza ta tambaya kudi don ya dena bata atm card dinsa. Tunda tace kaya zata siya bai hanata ba saboda rigimarsu ta party ta wuce. Washegari ta debi yara suka je manyan shopping malls din Kano da kyar ta sami abinda take so ta dawo rai a bace. Me zaayi da Nigeria abinda bai taka kara ya karya ba sai ka nema ka rasa. Washegari Khalifa ya tashi da zazzabi dama mura yake suka fita wannan siyayyar. Abu kamar wasa sai da suka kaishi asibiti da daddare, sai da safe aka sallamesu bayan an gama kara masa ruwa. Da suka dawo ne wurin karfe takwas ya kira Mama ya sanar da ita.

Ranar ta dace da talatin da daya ga watan october wadda a irin wannan ranar ne turawa suke yin halloween. Izzatu bata fadawa Hamza ba domin bata dauki abin a cikin irin wadanda ya hana ba tunda ba gayyato mutane zata yi ba. Ita da 'ya'yanta zasuyi abinsu a gida. Bayan Hamza ya fita tasa Tala tayi musu wanka ta koma kitchen. Ita kuma ta dauko musu kayansu da ta siyo ta saka musu. Harda Khalifa mara lafiya. A ka'idar wannan rana ta halloween wadda take da sunaye da yawa harda Day of the Dead ana yin abubuwa masu yawa. Nasara mabiya addinin kirista suna celebrating wannan rana ne domin tunawa da matattunsu. Kamar waliyai, manyan masu bauta da shahidansu. Ana saka kaya na ban tsoro a ranar kamar riga mai alamun jini, fuskar shaidanu, yin shigar da baza'a gane mutum ba, tsorata mutane a gidajensu ko waje, zuwa wuraren ban tsoro kamar makabarta, tsohon kango ko gidan da babu mutane. Kai hatta horror films(fim na ban tsoro) ana gani a wannan ranar ko ka ziyarci malamin duba da sauran abubuwan firgici dai. Haka halloween yake ko kadan bashi da alaka da musulunci. Amma wani lokacin musulmai yan uwammu idan suka sami kansu cikin yahudu da nasara sai kawai su dauki al'adunsu suna ado dasu ba tare da sunsan ainihin dalilinsu na girmama ranar ba. Zama a kasar waje ba shine dalilin da zaisa mu dauki dabiar nasara wadanda suka bata da yahudu wadanda Allah ke fushi dasu ba. Allah Ya tsare mana imanimmu. Amin
Chapter 8 · 0% Book details