Sashe 52
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amin Hamza yace sannan ya ajiye wayar. Addu'ar tsohuwar nan da suka hadu a kasuwa ya tuna yayi murmushi. Lallai Allah shine mai bayarwa ga wanda Yaso a lokacin da Yaso. Duk wannan abu a dalilin canjin ra'ayi da ya samu ne ya kyautatawa Zuhra. Hakika Allah Yayi gaskiya da Yace a suratul Rahman " Hal Jaza'ul Ihsani Illal Ihsan"...babu wani sakamako ga kyautatawa sai kyautatawa.
Hamza ya gyara alakarsa da matarsa wadda ya aura domin ya wulakanta. Ya bata damar zama wata jigo a rayuwarsa gashi tun ba'aje ko'ina ba yaga sakamako mai kyau a lokacin da yake cikin halin matsi da takura. Sai gashi komai yazo masa da sauki tunda ba'a taba rasa abinci a gidansa ba. Da duka mutane zasu zama masu kokarin kyautata alaka da sauran mutane da hakika zamu ga taimakon Allah a cikin dukkan al'amuranmu. Ya Allah Ka taimaki Nigeria da shuwagabaninta da dukkan kasashen da musulmi ke ciki. Amin
Sallah Hamza yayi raka'a biyu yayi godiya ga Allah SWT sannan yayi addu'ar samun nasara. Baiyi saurin fadawa kowa ba yana jira sai dare ya fara sanar da Zuhra amma kafin nan ya fita zuwa gidansu. A nan ya fadawa su Alhaji wayar da ya samu. Alh Nasiru yayi murna sosai tare da yi masa fatan alkhairi. Su Hajiya ma duk sunyi farinciki suka yi masa addua. Yana fitowa bai biya ko'ina ba sai gida.
*****
Izzatu ta sauko falo tana tafiya tana rangwada jiki. Tun daga sama take jin hirar Zuhra dasu Khalifa. Tana saukowa ta zauna daga can gefe ta fara kiran yaranta daya bayan daya. Abinka da da da uwa duk sai suka koma wurinta suna bata labaran abubuwan da suka yi lokacin da bata nan. Ko kadan Zuhra bata nuna damuwa ko bacin rai ba sai da ta tashi suka hada ido da Izzatu ta jefa mata muguwar harara. Bata tanka mata ba ta tashi ta shige kitchen zuciyarta babu dadi. Ita dai tana tsoron zaman da zatayi da Izzatu.
Da ta gama abinci ta zubawa su Junior a plates daban daban yadda taga Izzatu tana so sai dai bata same su a falo ba. Tala ta tura ta kirasu suzo suci abinci. Ko da taje dakin Izzatu ta fadi sakon Izzatu cewa tayi taje ta dafa musu indomie guda uku ita da yaran. Khalifa ya tashi Mummy ni dai abincin Maama zanci. Indomie uku bazamu koshi ba. Junior ya tashi nima haka Mummy kizo muje tare akwai dadi ya fada yana jan hannunta. Izzatu ta fizge hannu tace Zuhra ba mamanku bace nice mamanku. Ita bata sonku, so take Daddy ya koremu mu bar mata gidan ita kadai. Khalifa yayi shiru alamar tunani...ni dai Maama tana sona da gaske. Amma bari naje na tambayeta dama tace duk wanda yake fadar abu ba mai kyau ba akan wani idan baya nan jirgin aljannah a Kano zai barshi. Ran Izzatu ya baci tace idan ka sake min zancen jirgin aljannah sai jikinka ya gaya maka. Kuma duk ku sami wuri ku zauna ko na zane ku. Babu musu suka zauna suna mata kuka. Juyawa tayi taga me Nana take yi a gaban dressing mirror taga bata nan. Da sauri ta tashi ta fita, ta sama ta hangota Zuhra na bata abinci. Ta girgiza kai wannan yarinya da shegen cin abinci take, bata san lokacin da ta fice daga dakin ba. Dole ta kula da abinda Nanan take ci saboda kada tayi kiba sosai.
Tala ta kawo indomie haka su Khalifa suka ci ba don rai yana so ba. A dakin nata suka yi bacci Izzatu tasa Tala ta kaisu dakinsu.
Zuhra dai tasan duk neman rigima ne yasa Izzatu ta hana su Khalifa cin abincinta. Babu ruwanta tunda 'ya'yanta ne fatanta Allah Yasa sun koshi da indomie din da aka dafa musu. Wurin karfe tara ta tashi daga falon ta koma dakinta. Dama bata yi gangancin zuwa dakin Hamza ba don tasan ko ba'a fada ba Izzatu ya kamata taje ta kwana dashi. Abincinsa ta ajiye a dinning table sannan ta tafi.
****
Da murnarsa ya shigo gidan yau zaiyiwa Zuhra kyakkyawan albishir. Ganin bata falo yasa ya zauna ya ci abincinsa sannan ya tafi yayi wanka. Idan yayi tunanin Cutie dinsa sai yayi wani shu'umin murmushi. Yasan tana daki ana gyara jiki bata yarda tazo dakinsa ba wanka saboda sai ya yi mata fin karfi yayi mata da kansa. Air freshner ya fesa a dakin yana mamakin yadda akayi yau har ya dawo bata fesa ba. Shi da kullum idan ya dawo dakin sai sanyi da kamshi.
Wata hadaddiyar rigar bacci Izzatu ta saka mai kyau. Ta gyara jikinta tana zuba kamshi ta fito ta rufe daki. A ranta ta kudurce idan har Zuhra na dakin to sai dai su kwana su uku don bazata fita ba.
Duk abubuwan da yake kafin ya kwanta ya gama ya koma falonsa yana duba karin bayani game da workshop din da aka gayyace shi. Ba karamin project gwamnatin tarayya zata bawa wadanda suka yi nasara ba. Hankalinsa na kan aikinsa yaji an rufe masa idanu ta baya. Shiru yayi ya shaki kamshin wanda a take ya gane mai shi. Da sauri ya cire hannuwanta daga idonsa ya kalleta fuskarsa babu fara'a. Lafiya, kika shigo min daki a daren nan?
Murmushi tayi don tasan har yanzu Hamza na fushi da ita. A hankali zata karkato da hankalinsa gareta har ya gane abinda tayi domin inganta rayuwarsu ne ba don ta kuntata masa ba.
Ta sunkuyo zata yi kissing dinsa yayi saurin kawar da kansa gefe. Yanzu Izzatu bata burgeshi ko me zata yi abubuwan da tayi masa kawai yake tunawa.
Fuskarta kamar zata yi kuka tace Sweety ya kamata ka manta da dukkan abinda ya faru mu sake gina rayuwarmu kamar da. Nasan nayi maka laifi ina rokonka ka yafe min.
Wani irin kallo yake mata na rashin gamsuwa da abinda take fada....zancen na yafe miki kema kinsan ba abu bane da zai iya faruwa lokaci daya. Mu bar wannan zancen ma, na fada miki duk irin asarar da kika janyo min amma baki ce komai ba. Duk wata kadara da kika san ina da ita na sayar. Motata ce kawai ta rage da taki. Wace gudummawa zaki iya bani domin ganin mun cigaba da running din gidan nan kamar yadda muka saba?
Izzatu tayi saroro tana kallonsa. Ita bata dauki abin serious ba lokacin da ya fada mata. Tayi ajiyar zuciya...nima bani da wani kudi yanzu duk nayi amfani dasu a wurin biki. Amma zanyi kokarin taimaka maka da gyaran tawa motar. Sun kira maigyara yace zata ci kamar sixty thousand.
Hamza yayi murmushi tare da girgiza kai. Izzatu kenan, ita nata taimakon a kanta zai kare kenan. Yace to babu komai a hakan ma nagode.
Taji dadi ta sami wuri kusa dashi ta zauna...nasan wannan problem din is not permanent amma zanyi kokarin ganin mun rage kashe kudi sosai. Abinci da kake siyo mana every thursday sai ka rinka siyowa a wurin da bai kai na da tsada ba, sannan...
Bai bari ta karasa magana ba ya tashi..bari naje na rufe gidan ina zuwa. Ko sake kallonta baiyi ba ya fice ya barta zaune. Gani yayi idan ya cigaba da zama ransa ne zaiyi ta kuna a banza. Ita a irin nata hankalin duk abinda ta lissafa gani take yi ba karamin taimako tayi masa ba kenan.
Babu wani rufe gida da zaiyi domin ya rufe tunda ya dawo. Dakin Zuhra ya nufa yaji dalilinta na kin zuwa dakinsa yau.
*****
Kwance take a kan gado amma sam bacci yaki zuwa. Tunanin Ya Hamza take yi, yana can yau tare da Izzatu. Hawaye taji ya cika mata ido zuciyarta na zafi. Yanzu duk irin yadda yake bata kulawa haka zaiyiwa Izzatu? Gaskiya taga kokarin Izzatu sosai da ta bari Hamza ya aurota. Bata fatan ranar da Hamza zai nemi karin aure, gani take ciwon zuciya ne kawai zai kamata. Da wannan tunanin Zuhra ta rinka kuka wanda ta kasa gane dalilin yinsa.
A hankali Hamza ya bude kofar dakin ya shigo. Fitilar a kashe take amma yana iya jin sautin kukanta a hankali. Cikin sauri ya kunna fitilar ya karasa gefen gadon ya zauna. Zuhra na jinsa taki kulawa sai wani hawayen da yafi na da. Muryarsa a sanyaye yace to bari na tafi tunda baki so zuwan nawa ba.
Yana rufe baki ta tashi zumbur ta rungume kam tana kuka mai sauti. Shima rungumetan yayi tare da sauke ajiyar zuciya. Ashe dai ba shi kadai yake sonta sosai ba. Sun jima yana rarrashinta har ya samu tayi shiru tana mayar da numfashi. Dago kanta tayi ya shafa fuskar yana goge mata hawaye...Cutie haka kike da kishi? Ina da aiki a gabana kenan. Ni da nake so idan an tashi rabon kwana ya zama sati bibbiyu. Kyakkyawan mintsini yaji a hannunsa sakamakon maganar da yayi ya daga hannun yana yarfewa....banda kishi harda mugunta a lamarinki.
Zuhra ta harare shi...ni ka tashi ka tafi tunda abinda kazo fada min kenan. Dan bakin da take turowa ya kama da nashi yana kissing. Bata dade ba ta manta ta fushin ta biye masa. Bayan dan lokaci ta ture shi ya tambayeta dalili...ance babu kyau satar kwana.
Dariya yayi kafin yace wa ya fada miki satar kwana nazo yi? Sai gobe ya kamata muyi maganar rabon kwanan amma kawai sai naji ki shiru.
Zuhra tace naga ta dade bata gida ita ya kamata ta kwana. Nima bazan so ayi min haka ba. Ka tashi ka tafi.
Ya shafa lips dinta...sai da kika gama cinye min baki zaki ce na tafi.
Sunkuyar da kanta tayi tana murmushi. Ya dago fuskata suka hada ido tayi saurin kawar da kanta....gobe akwai albishir da zanyi miki maidadi Cutie. Ki tanadi tukwicin da zaki bani. Ba a son ransa ya tashi zai barta ba.
Yana cikin tafiya yaji Zuhra tace..Ya Hamza I love you.
Iyakar karfin zuciyarsa ya tattaro ya fasa komawa wurinta. I love you more Cutie. Goodnight.