← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 67

Sashe 10

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hankalinsa a tashe ya gyara parking din motarsa saboda yaga alamun Alhaji na gida. Yana shiga falo Adabiyya da Hamida ya gani suna kuka. Gabansa ya fadi yace ku meye haka? Adabiyya ta taso ta rungumeshi tana cigaba da kukan. Dama duk ta fisu raguwar zuciya. Hamida tace Mama akeyiwa gyaran kafa. Me kika ce??? A razane yake maganar tace gocewar kashi ta samu. Matsar da Adabiyya yayi daga jikinsa ya shiga falon Alhaji. Mama ya gani zaune a kasa tayi gumi sosai Hajiya na rike da hannunta. Kafarta ta hagu daure da wani farin yadi. Gefe kuma mai dori ne durkushe gaban Alhaji zai karbi kudinsa. Mai dorin yace in Allah Ya yarda gobe da safe zan dawo na duba. Allah Ya kiyaye gaba.

Tamkar wanda kwai ya fashewa a ciki haka Hamza ya karaso cikin falon. Mama ce kawai ke kallonsa, ita Hajiya kawar da kai tayi gefe. Alhaji Nasiru ya hade fuska kana ganinsa kasan yana cike da bacin rai. Kusa da Mama Hamza yaje ya zauna ta riko hannunsa kawai sai ta soma kuka. Hajiya ta tashi zata bar falon Alhaji ya dakatar da ita. Hamza yace Alhaji barka da rana. Muryarsa har rawa take bata fita sosai. Alhaji yace Hamza.....toh fa yau duk su biyun sun kira shi da sunansa. Allah gani gareKa yace a zuci. Naam Alhaji. Alhaji yace dago kanka ka kalleni.

Kasawa Hamza yayi. Alhaji yace ashe kana da sauran kunya. Dubi yadda iyayenka suke kuka saboda bacin ran da suka kwaso a gidanka. Yau Mamanka ce a zaune ana mata gyaran gocewar da tayi a gidanka matarka tayi mata dariya. Wace irin rayuwar aure kuke yi kai da iyalinka? Me kake son nunawa duniya game da tarbiyar da muka baka? Ba don tsarewa ta Allah bace duk kannenka koyi zasuyi da irin dabiun da ka kwaso a turai. Alhaji ya cigaba da cewa duk irin abinda kuke yi babu wanda ban sani ba amma na kawar da kai saboda iyayenka basu tunkareni da maganar ba. Na basu damar su ta iyaye mata su saita ka a hanya kuma nasan sunyi iya kokarinsu. Amma yau saboda abin yayi yawa Halimatu da kanta ta sanar dani abinda yarinyar nan tayi musu. Wulakanci na karshe Izzatu tayiwa iyalina amma bazan umarceka da rabuwa da ita ba. Sai dai ka sani wallahi nayi maka rantsuwa ranar da duk kuka sake aro daga munanan al'adun wasu har kunnena ya jiye min ko ido ya gani zanyi maka hukuncin da baka taba tsammani ba.

Da sauri Hamza ya kalli mahaifinsa don Allah kuyi hakuri Alhaji. Nasan nayi kuskure tunda da goyon bayana komai ke faruwa. Amma in Sha Allah zan gyara kuma yanzu zan daukota tazo ta bada hakuri. Hajiya tayi saurin cewa ban yafe maka ba muddin kace mata tazo bada hakuri. Indai hankalinta da tarbiyarta basu nuna mata abinda ya kamata ba shikenan. Alhaji yace ina zaune kike irin wannan zancen Halimatu? Tace ayi hakuri. Hamza ya dubi Mama wadda kanta yake a kasa ki yafe min Mama don Allah. Abinda ya faru yau ko kadan bani da masaniya a kai. Alhaji yace halo me ma kuka ce sunan abin? Hajiya tace yo ni ina zan rike. Kamar ba kalmar turanci ba, yau na fara jinta ma. Hamza ya sake dukar da kai ko a da bama yin wannan ranar bansan dalilinta na yi ba yau. Alhaji yace dalilinta ya wuce ta tozarta min iyali ne? Ka tashi ka tafi Allah Ya kyauta.

Hamza dai kin tashi yayi ya kara matsawa jikin Mama yana rokon ta yafe masa. Murmushi kawai tayi tace masa ka tashi ka tafi ba komai. Duk yadda yaso Mama taki tsawaita magana. Hajiya tace ka tashi ka bamu waje magana ta kare. Idan ka fita ka turo min Adabiyya da Hamida. Jiki ba kwari ya fita ya turo su. Hajiya tasa Adabiyya sake gyara gadon Mama , ita da Hamida suka kamata suka kaita daki.

Zuwa dare su Ibrahim duk sun zo gidan da iyalansu. Kowa yayi bakin cikin jin abinda Izzatu tayi musamman dariyar. Ummahani matar Ibrahim tace ni Yaya tausayi yake bani. Jidda tace tausayin me? Ba fa auren hadi bane da kansa yaje ya kwaso mana ita. Mariya tace kuma dashi suke komai ba. Dama matsalar ka fara abu kenan. Sai kaso denawa mabiyanka suce basu san zance ba. Motoci hudu ne a gidan Yaya amma ko keke bai siyawa ko da Nura ba da yake karatu. Irin abinnan ka daukewa iyaye wani nauyi ko a jikinsa. Daga shi sai iyalinsa. 'Yan kwanakin baya ne ma naga abin ya dan canja. Mama dai tana daga kwance tace ku bar zancen nan haka.

A haka sai da Mama tayi sati uku a kwance saboda banda gocewar tayi ta fama da zazzabi. Kullum safe, rana da dare Hamza sai yazo. Da daddaren ma da su Khalifa yake zuwa. Izzatu kuwa tunda baice tazo suje dubiya ba itama ta share. A ganinta yan uwansa ne bazata masa shisshigi ba. Wani lokacin ya hadu da kannensa wadanda suka hade masa kai. Daga gaisuwa basa kara yi masa wata maganar. Su Hajiya suna amsa masa gaisuwa amma suma daga nan magana ta kare. Rashin kula shi da Mama keyi duk yafi komai tada masa hankali. Bashi da aiki sai bada hakuri sai dai tace masa babu komai.

A haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya har suka dan daidaita. Mama ce dai har yanzu bata yi masa kamar da. Shi kuwa bai kosa da yi mata siyayya ba kullum. Domin yanzu ya dauki irin abinda Ibrahim yake yi tun bayan yayi aure. Kullum sai yazo gidan ya gaishe da iyayensa ko da safe kafin yaje aiki ko bayan magariba.
[9/25, 3:34 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿16

Batul Mamman(Mrs)💖

Wata asabar da safe Izzatu ta nemi izinin Hamza tana son zuwa Abuja tunda su Junior na hutun makaranta wurin iyayenta. Ya amince har ya bata dubu hamsin ko zata yi siyayya sannan ya cika mota da mai yasa dreba ya kaisu. Ashe new year celebration taje gani. Sauran shekarun duk tare suke yi da Hamza, ganin yadda lokaci guda ya canja mata yasa bata sanar dashi gaskiya ba. Da yaran ta tafi suka je kallo tare da kannenta. Bayan sati daya suka dawo gida.

Zuhra ce take tafe da katuwar ghana must go shake da kayan sanyin da ta saka. Yanzu ta kware sosai don sanyin da ya wuce tayi ciniki sosai. Da yake farkon March ake gari ya soma zafi. Sai dai mijin Anti Faiza ya samar mata wata makarantar primary sun bata kwangilar sakar rigunan sanyin dalibai. Murna sosai su Baba suka yi. Ta gama na farko shine zata kai musu. A daidai wani lungu zata wuce bakin titi ta hango Anas da abokinsa Sani suna busa wiwi. Idonunta kyam a kansu, Anas ne ya fara hangota yayi saurin taba sani. Dukkansu kashe tabar suka yi suna murmushin yake. Fitowa suka yi daga lungun Sani yace kaga manyan yan mata. Zuhra ina zuwa haka da rana? Ta karkace kai tana kallonsu wai nan bagarar dani zakuyi. To nagani kuma sai na fada. Anas yace don Allah kada ki fadawa Baban yara. Kinga muje mu rakaki inda zakije ma. Sani ya karbi jakar zai daukar mata. Da sauri ya mayar ya ajiye...ke yanzu tun daga gida kika dauko jakar nan. Zuhra tace eh menene? Sani yace Anas dauki ka ji. Anas ma dagawa yayi ya mayar Zuhra haka kike da karfi. Wani murmushi ta saki da yasa duk munin kwalliyarta tayi kyau. Au ku da rainani kuke yi? Ai kada ku taba bari dambe ya hada mu don kasa zan kaiku. Sani yace ke dalla can wa ya fada miki maza na son mata karfafa. Ko ni naji nauyin jakar bare ke. Wallahi ina baki shawara idan kika yi aure ki nunawa mijinki ke raguwace. Sai yafi sonki. Amma yana ganin kin fara aje kwanji wata zai dauko a mayar dake maigadi. Zuhra ta sha kunu amma ka zage ni Sani, kai Anas kayi wa abokinka magana wallahi. Anas yayi dariya ai gaskiya ya fada miki. Daukar abu mai nauyi ai ba na yanmata bane. Fizgar jakar tayi ku bani kayana yan wulakanci. Kun tsayar dani kuna ci min fuska..kuma sai na fadi abinda naga kuna yi. Anas yace to yi hakuri. Yanzu ina kika nufa mu daukar miki kayan. Dayake dama ta gaji sosai tace bakin titi. Gidan yayar Hajara zani. Sani ne ya dauko jakar Anas yace yaushe ne bikin Hajara. Nan da sati biyu Zuhra ta bashi amsa.

A bakin titin suka tarar mata adaidaita sahu. Anas ya mika masa dari biyu yace ya kaita har kofar gidan da zata je. Tayi musu godiya suka juya. A hanya Sani yace Baabaa yaushe zaka fadawa yarinyar nan kana sonta ne? Anas yace haba Sani. Zuhra tafi karfina. Sani yace Zuhran?yarinyar da ko kwalliya bata iya ba. Ko sakandare bata gama ba fa. Anas yace amma ai tana da tarbiya. Kuma sau nawa Baban yara na kama mu a wurin nan. Ai da kunya nace ina son yarsa. Sani ya bigi kafadar Anas to tun wuri gara ka sani ni zan mata magana. Dama don naga kamar ka rigani fara sonta shiyasa na kyale. Anas ya daure fuska kasan Allah bazan bari ka aureta ba. Zuhra sai mutumin kirki mai rufin asiri. Sani ya soma gudu bari kaga har gida zan sami mahaifinta. Da haka suka tafi suna dariya.
Chapter 10 · 0% Book details