Sashe 45
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ina nufin bari tayi wanda har mahaifarta ta fara fitowa saboda rashin kwarinta. Shiyasa muka ga dole muyi mata virginal hysterectomy saboda ceto rayuwarta.
Kokari Hamza yake kada ya rasa nutsuwarsa yace kayi min bayani a yaren da zan gane. A wane hali Izzatu take?
Likita yace yanzu tana bacci saboda anyi mata allurar anasiziya. In sha Allah nan da kamar awa daya zata farfado. Abinda nake nufi da hysterectomy shine mun cire mata mahaifa saboda ba karamin lalacewa tayi ba.
Wata muguwar faduwar gaba Hamza yaji wanda hakan yasa shima ya zauna. Zuhra ta sake kankame hannunsa saboda firgici. Yace doctor kana nufin yanzu bazata sake haihuwa ba.
Haka nake nufi amma don Allah kayi hakuri bamu fara sanar da kai ba kafin mu aiwatar da nufinmu. Yanayin da take ciki ne baya bukatar bata lokaci. Idan ta tashi ita tafi cancanta da ta fadi maganin da tasha ya illata mahaifar haka. Bazamu iya yanke komai ba sai munji daga gareta. Tashi likitan yayi ya barsu a office din bayan ya gama yi musu bayani.
Yana fita Zuhra ta rungume Hamza tana kuka. Kayi hakuri Ya Hamza duk laifina ne. Ganina ne ya bata mata rai har hakan ta faru. Da hannunsa ya share mata hawaye...ki dena fadin haka Cutie kaddara ce da bata wuce kowa. Amma shima a kasan zuciyarsa gani yake kamar laifinsa ne tunda Izzatu ta fada masa ranar zata dawo, sai abin ya zama kamar cin fuska ma.
Sabon dakin da aka kai Izzatu suka je. A nan ya bar Zuhra yace zaije gida ya fada musu tunda baizo da waya ba.
******
Daga Hajiya har Mama babu wanda labarin yayi masa dadi. Duk sun tausayawa Izzatu. Mama tace watan cikin nawa? Ni ban san dashi ba Hamza ya bata amsa. Sai a lokacin ta kula da rigarsa tace ya gyara ta. Kunu da kayan tea suka hada ya daukesu ita da Hajiya da Adabiyya ya kaisu asibitin sannan ya dauko Zuhra suka tafi gida. Har lokacin Izzatu bata farfado ba.
Saboda yanayin da suka fita maigadi da Tala suna ganinsu suka fara tambayar ya mai jiki. Zuhra ce take iya basu amsa tana cewa da sauki. Wanka duk suka yi sannan Zuhra ta sauko ta hada masa abinci. Da kyar ta samu yasha tea yace zai koma asibitin. Damuwa ce tayi masa yawa yana tambayar kansa ta ina zai samo kudin asibitin Izzatu? Bashi da sauran kadarar da zai sayar sai wani fili da ya siya a Kumo wanda yanzu kafin a samu mai siya ma aikine guda. Shi ko irin budewa yara account dinnan bai taba tunanin yi ba saboda basu hango rana irin wannan da zasu fuskanci matsin rayuwa ba.
Zuhra na kallon yadda ya zurfafa a tunani ta dan dafa kafadarsa. Ya Hamza kaine fa kake cewa kaddara ce abinda ya faru. Don Allah kayi hakuri. Idan ka bari damuwa tayi maka yawa waye zai rarrasheta idan ta farfado? Murya a sanyaye yace babbar damuwata yanzu inda zan samo kudin asibitin Izzy. Kinsan halin da nake ciki bansan inda zan samo kudin ba indai ba kudin kamfani zan dauka ba. Zuhra tace idan ka dauka aikinku zai sami rauni. Kuma kace har kun kusa kammala daya. Ta mike tsaye ina zuwa....
Bata dade ba ta dawo da wata karamar leda mai kyau a hannunta. A tafin hannun Hamza ta ajiye ledar yace koma meye ki rike kayanki zansan yadda nayi na sami kudin. Ko bashi ne sai na nema. Idonta fal hawaye tace yanzu ka gwammace ka nemi bashi akan ka karbi abinda kake da iko dashi? Wannan abin da na baka kai ka siya fa? Idan ka karba ai ba yana nuna gazawarka a matsayin namiji bane. Jarabawace Allah Ya dora maka.
A hankali ya bude ledar ya ciro wata yar roba mai murfi. Sarka ce da dankunne da zobe na gwal a ciki. Saurin rufewa yayi ya dora mata a cinyarta. Cutie ki dauke kayanki bazan sayar miki da sarkarki ba....abinda ya kasa fada shine ko pant bai siya mata ba a lefenta. Komai Alhaji ne yayi. Hannuwanta biyu tasa ta rike kumatunsa tana kallon fuskarsa mai dauke da tsantsar rashin kwanciyar hankali. Tunda nake ban taba saka gwal ba a rayuwata don an sayar da wanan bazanji komai ba. Duk irin wadannan abubuwan dama ai saboda rana irin yau ake tanadin su. Ni a abinda su Baba suka koya min wannan shine aure. Taimakon juna a lokacin bukata batare da mun fita waje mun tonawa kanmu asiri ba. Su Alhaji ne baka son sanarwa halin da kake ciki to ni din da na sani ka bani damar taimakonka mana. Sarkar da hannunta ya hada ya rike sosai sai kawai taga hawaye ya fito daga idonsa. Lallai rayuwa bata da tabbas, babu wani yanayi da bawa zai tsinci kansa yace wannan yanayin zai tabbata a ciki har ranar busa kaho. Yau kana da arziki gobe waninka ne. Wa zai taba tunanin akwai ranar da Architect Hamza Nasir Hamza zai karbi taimako a hannun Fatima Bashir? Yarinyar da ko certificate din shaidar tayi secondary school bata dashi,ga kazanta ga rashin wayewa. Ikon Allah kenan, kada ka taba raina bawa domin baka san abinda Allah yayi masa na arziki ba. Arziki kuwa ko da ba na kudi bane. Hawayen da Hamza yake yi ya karyar mata da zuciya ta soma kuka. Haka suka rungume juna na tsawon lokaci. Daga baya Hamza yace ta tashi su koma asibiti tace a'a yaje kasuwa ba'a rasa masu bude shago ranar lahadi ya sayar. Ita kuma zata kara yin saka zuwa la'asar ko bai dawo ba zata yi girki ta tafi asibitin da kanta. Sai da ya kwashe kusan minti biyar yana kissing dinta sannan ya fita. Bai san da yaya zai gode mata ba. Tunda ya shiga mota har ya isa kasuwar ALHAMDULILLAH yake ta nanatawa saboda godiya ga Allah da Ya azurta shi da mace tagari a lokacin da rayuwarsa take tsaka da rushewa.
A dalilin mugun tashin da dollar tayi wanda muke ta addu'a Allah Ya yafe mana Ya kawo mana sassauci sai da Hamza ya sami dubu dari uku da tamanin da hudu a matsayin kudin sarka, dankunne da zobe. A haka ma don mutanen sun kula kamar a matse yake da ya sayar.
A hanyarsa ta tsallaka titi ya koma motarsa yaga wata tsohuwa tukuf itama ta rasa yadda zatayi ta tsallaka. Da a lokacin da yake Hamzansa ne mijin Izzatu ita kadai baya jin zai iya yadda hannunsa ya taba matar. Amma yanzu ya koyi darasin zaman duniya. Hannun matar ya riko tana tafiya da kyar har ya tsallakar da ita titi. Godiya ta rinka yi masa tare da addua. Harda dan kukanta tace ba don kai ba sai nayi kusan minti shabiyar ina kokarin tsallaka titin nan. Magani na karbowa dana yana fama da lalurar asma. Ta dauki wata leda da magani ta nuna masa. Hamza ya tausaya mata yace baki da wasu yaran ko jikoki da zasu je miki? Tayi murmushi, shi kadai ne dani. Bayan shekaru shabakwai sai yanzu matarsa take da tsohon ciki. Idan abin ya tashi ita take zuwa amma yanzu bazata iya doguwar tafiya ba. Yana ganin kansa a wani yanayi ga wadanda suka fishi. Kudin aljihunsa ya shafa ya sa hannu ya kirga dubu goma ya bawa matar. Hannu na rawa ta karba tana ta kuka...Allah Ya albarkaci rayuwarka data iyalinka, Allah Ya rabaka da masifun zamani, Allah Ya baka arziki na halali daga inda baka taba tsammani ba. Yaro nagode, nagode. Hamza na tsaye har ta shiga adaidaita sahu sannan shima ya tafi zuciyarsa kamar an cire masa wani nauyi. Hakika sadaka maganin masifa ce kuma waraka daga bacin rai.
Asibitin ya koma ya tarar Izzatu ta farfado. Raliya ya kira a waya ya sanar da ita halin da Izzatu ke ciki. Cikin kidima tace gobe zata taho in sha Allah. Tana ajiye wayar ta kira kanwarta Larai ta fada mata asibitin da suke.
Tsananin bacin rai da kishi yasa Izzatu kuka tunda ta farfado. Yanayin da taga Zuhra da Hamzanta shi kadai yake mata yawo a ka tunda ta bude ido. Su Mama kuwa sai tausayinta suke yi a nasu tunanin bakincikin bari da cire mata mahaifa da akayi take yi. Cike da tausayi Hamza yake mata sannu amma ko kallonsa taki yi. Su Mama sai suka dauke kai kamar basu kula da abinda suke yi ba. Adabiyya tace Yaya ina Anti Zuhra? Yace zata taho girki yasa bamu fito tare ba.
Basu dade ba kuwa sai gata da kwandon abinci. Bata tashi daga kan sakarta ba sai da tayi mai yawa ta yadda abin da ya rage mata saura kadan. Itama ko kallo bata ishe Izzatu ba duk da halin ciwon da take ciki. Sauran 'yan uwan Hamza suma duk sun zo. Zuhra ma ta kira Baba ta fada masa Izzatu na asibiti yace zasu zo washegari tare da Umma.
Anti Larai kanwar Raliya tazo tare suka karasa yinin sai dai ta baro maigidanta babu lafiya saboda haka bazata iya kwana a asibitin ba. Dole aka yanke shawarar Adabiyya da Zuhra su kwana da Izzatu. Ranta inyayi dubu ya baci amma ko tashi bazata iya yi ba shiyasa dole ta hakura. Shabiyu saura na dare su Zuhra suka fita suka bashi wuri ya dan zauna wurinta. Sai lallabata yake tana kuka ita bazata zauna da wadda tayi sanadiyar zubar mata da ciki ba. Da kyar ya lallabata yace gobe shi zai kwana. Haka suka rabu ranta a bace. Itama Zuhra yayi mata sallama sannan ya tafi gida.