← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 67

Sashe 63

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Umar Dalha > ZAMA NA AMANA 2 AL'ADUN WASU 77 Batul Mamman(Mrs) Da kuka Izzatu ta fito daga motar Nura. Maigadi ya biyota yana tambayar ko lafiya. Bata bashi amsa ba sai kallon banza. Murya a sama tana kuka ta shige ciki. Nura dai tsaki yayi ya ja motarsa. Tala ma da yaran duka babu wanda ta kula ta wuce ta tafi dakinta. Wai ita Hamza zaiyiwa saki har biyu? Lallai dan Adam ba'a ci masa laya. Irin soyayyar da suka yi tun kafin suyi aure ta zauna tana tunawa. Bakincikinta ya karu ne saboda a ganinta ba karamin kaskanci bane ace an saketa saboda wata Zuhra. Yarinyar da bata jin ko brush din kirki ta iya lokacin da Hamza ya aureta. Rasa mafita tayi ta dauki waya ta kira Raliya. Babu abinda ta ragewa mahaifiyar tata na dangane da abinda tayiwa Zuhra zuwa halin da take ciki yanzu. Raliya ma kukan ta soma yi tace Izzatu kinga abinda nake ta ji miki tsoro sai da ya faru. Ban ga ranar bin al'adun wasu don ka burge wasu tsiraran mutane ba. Kwalin tissue din da ta kusa kararwa daga shigarta daki ta kuma janyo wata ta goge hawaye....Mum ya zaki ce ina bin al'adun wasu. Duk abinda muke yi da ai tare dashi mukeyi. 'Yan wadanda nayi da baya so sosai kadan ne. Kuma naga shima dan zaman da yayi a Canada ya isa ace ya waye da dabi'unsu. Ace mu kullum 'yan Nigeria babu wani canji a rayuwarmu. Ni a ganina kawai gajiya yayi dani amma babu wasu al'adun wasu da nake yi. Ta yaro kyau take Raliya ta fada tana tuna irin sakacin da ya samo asali daga wurin Alh Sunusi a fannin tarbiyar 'ya'yansu. Shine ya dage sai su barsu su sake bayan sun bar kasarsu. Tun Raliya bata jindadin yadda 'ya'yansu ke sajewa da na turawa ta fannin dabi'a har ta fara so musamman idan suka zo gida Nigeria suka shiga cikin 'yan uwa. Dan turancin da sukeyi da 'yar fitsara shi yake burge mutanenmu. Sai kaga kowa na kokarin kyautata musu tamkar anga 'ya'yan wani shugaban kasa. Kuma irin haka dama halinmu ne musamman Hausawa. Da 'yan uwanmu sun tafi kasar waje mun rinka shela kenan sai kowa ya sani. Idan suka zo ganin gida kuwa ba'a magana. Kowa jiki na rawa yana tasa bajintar. Raliya tayi ajiyar zuciya....yanzu duk bazaki gane abinda nake nufi ba kila sai nan gaba. Amma ina so ki sani namiji duk inda yake indai akwai sauran mutumci a tare dashi to yana son a kyautatawa iyayensa. Sai kika yi rashin sa'a gidan Alh Nasiru tsarin rayuwarki bai burgesu ba. A zatonki sonki ne basa yi shiyasa kuka yi ta samun sabani da Hamza da farko har sonki ya rufe masa ido ya koma yana biye miki. To kada ki manta dama tun da fari ga irin tarbiyar da ya tashi da ita yake hakuri da irin taki tunda ke kinki canjawa don ki faranta masa. Sai Allah Ya kawo wadda zata yi masa yadda yake so kafin yace yana so. Ai wallahi dole ra'ayinsa ya juya can. Gashi ke kuma sai shirmenki ya karu ninki akan na baya. Izzatu dai kuka take tana sauraron mahaifiyarta. Raliya tace kina jina kuwa? A hankali tace eh. Duk abinda kika yi masa kinga ai ya hakura musamman cire mahaifa. Amma yau da yarinyar nan ta mutu wallahi banda saki uku nasan sai yasa an kulleki. Kinyi sake tauraronki ya dishe a zuciyarsa. Abinda Larai take ta korafin zai iya faruwa kenan duk muka banzatar da ita. Yanzu ki bari zan kira Ustaz dan gidan Kawu mai zare na tambayeshi game da dalilin cewa sai kinyi idda a gidan. Kafin nan don Allah Izzatu ki kama kanki kinji ko. Zan kiraki idan munyi magana. Yau daya a rayuwarta da take ganin ta rasa abu mai matukar mahimmanci ta nutsu ta saurari mahaifiyarta. Idan har akwai yadda zatayi ta sake mallakar Hamza to zata yi. Abu daya ne bata yarda dashi ba saboda tashin turai da tayi shine bin malaman tsibbu da bokaye. Kyankyaminsu take ji kuma gata da tsoron zuwa irin wuraren nan. Ta taba kawa da ta kaita wai a basu maganin mallaka. Tunda taji ana zancen tayi masa lemo da jinin al'adarta na ranar karshe a wata bata koma ba. Bokan na fada tana amai ma. **** Babu wata hira tsakanin Hamza da Zuhra a motar sai kallon juna da murmushi. Karshe ma hannunta ya hada da giyar motar ya rike. Dukkaninsu farincikin da suke ciki bazai misaltu ba. Maigadi na bude gate da ya hangota kamar yayi tsalle don murna. Tabbas yasan inda take a bakin Tala amma dole yayi kewarta. Abinci da kyautawar da take musu ai bazasu manta ba. Hatta jakar hannunta mika hannu yayi zai karba Hamza ya karbe yana dariya...Mal Talle anya kayi farincikin ganina ranar da na dawo kuwa. Irin wannan murna haka? Zuhra tayi murmushi kawai ta shige ta barsu. Maigadi yace Yallabai ka rike matarka da kyau. Wallahi tana da kirki sosai. Hamza yace nagode. Ga wannan gobe kaje gida kayi sati biyu....Kudi ne maigadi ya karba da murna. Lallai an sami canji. A da Hamza don kansa baya barinsu zuwa ganin gida sai sunyi ta roko amma yanzu ya san hakkin mutane sosai. A cikin gidan ma tamkar an kawo wutar nepa bayan shekara daya haka suka yi ta murna. Tala ta kwashi 'yan kayan da Zuhra ta sami daukowa ta kai sama. Su Khalifa kuwa suka dane jikinta. Nana sarkin rigima tace Maama goyani.. Zuhra na durkusawa Hamza ya shigo yace ke rufa min asiri. Nana zo na goyaki kinji. Maama da kayana a jikinta. Nana ta sa kuka ita bayan Maama. Tun yana lallabata har ya soma fada. Zuhra ta dage zaya iya goyata yace sam bai yarda ba. Izzatu ce taji kukan ya isheta ta fito. Ganin Hamza yasa zata koma sai kuma ta kula da Zuhra. Ba karamin kyau tayi ba idan aka hadata da Zuhran da ta sani da farko. Kamar ta sauko tayi mata magana taji dalilin da yasa ta boya ta jawo mata saki. Sai ta tuna da shawarar da Raliya ta bata ta koma dakinta tare da bugo kofa da karfi. Da kyar Hamza ya lallaba Nana ta yadda ya goyata. Amma ta dage sai ya saka zani. Zuhra dasu Junior suna ta yi musu dariya yace bazai saka ba. Zuhra ya kalla yace zaki san ni kika yiwa dariya idan na kamaki. Tana jin haka ta haye sama tasan zata sha aiki. Sai dai ga mamakinta dakin fes ta same shi. Komai a gyare, hatta zanin gado Hamza ya dauko sabo Tala ta shimfida a kan gadon. Tare dasu Junior ta tafi dakin suna ta bata labarin abubuwan da sukayi lokacin da bata nan. Hamza ya shigo da Nana a hannu tun yana saka baki a hirar har ransa ya soma baci. Yau da yake son kasancewa da Zuhra bayan lokacin da suka dauka basa tare shine ta biyewa yara hira. Gajiya yayi ya fita dakinsa ya bude jakar kayan tsarabar da bai sami damar budewa ba tunda ya dawo. Kayayakin da ya siyowa yaran ya debo harda wasu riguna da ya siyowa Tala da maigadi. Bawa kowa nasa yayi sannan ya basu nasu Tala. Harda kashedi idan kun kai musu kuje ku nunawa Mummy. Yara an sami abinda ake so suka fita suna ta murna. Suna tafiya ya rufe kofar harda murda mukulli. Zuhra ta dawo kusa dashi ta tsaya yana ta kallonta musamman dan cikinta da ya tasa kadan. Hannuwanta ta sakala a wuyansa ta rungumeshi. Yace da kinsan abinda kike so kenan kika biyewa yara kina hira kawai don ki ja min aji....ya kama hannuwan nata ya cire...nima yanzu zan ja nawa sai ki bisu kuyi hira ni bacci nake ji. Zuhra tayi dariya ta sake rungumarsa. Haba Ya Hamza kaga suma nayi kewarsu ne shiyasa. Dan zo kaji irin yadda nayi kewarka duk tafi ta kowa. Matsawa ya kara yi naki din. An fada miki mata ne kadai suka iya yanga. Sai nan da sati daya zamu fara kwana a daki daya ma. Kinga tafiyata. Yana tafiya Zuhra ta sake binshi ta rungumeshi ta baya tana masa dariya....idan ka fita abinda na kawo maka na murnar dawowarka zan fasa baka....yadda take magana tana jan kowane harafi yasa shi saurin juyowa suna kallon juna. Kafin ya daga hannu ya tabata an soma kiran sallar magriba. Ya cije lebe Zuhra ta kwashe da dariya. Ai kaga yanzu sai kayi yanga da hujja. Ni bari naje nayi alwala sai bayan sati idan mun hadu. Hannunta ya rike suna bin kiran sallar har aka gama suka yi addua sannan yace yau idan kika shigo hannuna Cutie...hmmmm sai na dawo dai. Love you. Itama tace masa Love you too sannan ya fara shiga toilet dinta yayi alwala ya fito ya tafi masallaci. Da Zuhra ta idar da sallah kasa ta sauka wurinsu Tala. Abincin da tayiwa Hamza bashi da yawan da zasu ci duka gidan shiyasa ta dora jallof din taliya. Ba jimawa ta gama ta zubawa kowa. Tala sai kallonta take tana murmushi. Ba karamin kewa ta barsu dashi ba. Bare da ta kula kamar Zuhran ciki gareta shikenan komai sai tace kawo na karasa. Haka suka gama girkin ta koma dakinta tayi sallar Isha. Bayan Ishar Hamza ya dawo. Yau fa anga Cutie bashi da wurin zama sai inda take. Hijab din da tayi sallah ya samu tana ninkewa ya karba ya karasa mata sannan yace ta zauna zasu yi magana. Zancen abinda Izzatu tayi yayi mata sannan yace nasan kina sane da hukuncin da Alhaji ya yanke na cewa na saketa ko? Sunkuyar da kai Zuhra tayi bata ce komai ba sai hawaye dake barazanar saukowa daga idonta. Sauran abubuwan da Izzatu tayi mata duk da bata ji dadi ba amma tana iya danne bacin ranta ta hakura. Wannan karon kuwa idan har tace ta hakura babu komai ita kanta tasan dole a jerata sahun farko a makaryata. Babu macen da zata fuskanci abu makamancin wannan tace ta hakura lokaci daya. Duk tunanin da Zuhra take yi Hamza na kallonta. Abu ne mai wuya ace Zuhra ta yafewa Izzatu....sake matsowa yayi
Chapter 63 · 0% Book details