Sashe 3
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A bakin rariya ta tsuguna ta cinye tuwonta ta wanke baki. Umma tace ya naji shiru ko bakin ne. Tace a'a almajiri na nema a waje. Wuraren shadayan dare su Umma sun kwanta Zuhra ta lallabo ta fito falo. Tayi sa'a kuwa ledar naman tana nan kan dan tebur din da suka ajiye tare da jug din ruwa. Zuhra ta bude ledar a hankali ta sami yan kasusuwan da basu cinye ba duk ta tsotse don naman yayi mata dadi.
Baba ya taso Umma suka tsaya ta yar kofar jikin tagar dakinsu suna kallonta. Hawaye Umma take sosai a hankali tace bar mana tayi muci. Baba yace muna tausayinta tana tausayinmu. Allah Ya albarkaci rayuwarki Fatima. Suka koma suka kwanta.
Da safe Umma ta riga ta tashi. Ta fito suka gaisa ta dauko tsintsiya zata fara shara. Umma tace kamar na bar ledar naman nan a falo. Zuhra ta dan tsorata sai tace ai da asuba na dauke saboda beraye. Umma tayi murmushi kawai ta fita tsakar gida.
[9/25, 2:39 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿5
Batul Mamman(Mrs)💖
Kafin karfe tara ta gama duk ayyukan da zata yi. Wanka tayi sannan tayi shirin islamiyya tunda asabar ne ana yin ta safe. Ta gama shirinta tsaf ta yiwa iyayenta sallama ta tafi.
A darasi na uku Malama Rabia ta shigo. Ita kadai ce mace da ke koyarwa a islamiyar tana koya musu Nahawu. Zuhra jira tayi sai da aka kammala darasin gaba daya sannan tace tana da tambaya. Yan ajin har sun soma dariya sannin halinta. Wata tambayar idan tayi sai kaji kamar shirme. Ita kuwa sai ta dake, sai an bata amsa tace nasan ku ma kun karu. Malama Rabia tace ina jinki Fatima. Zuhra tace menene hukuncin macen da ke karin gashi ko bleaching a musulunci. Malama tayi dan murmushi ai hukuncinsu a bayyane yake, babu kyau. Zuhra tace ai nima nasan babu kyau ina nufin akwai wata aya ko hadisi da yayi nuni an hana ko kuwa fatawar malamai ce kawai. Malama Rabia tace to bari mu fara da maganar karin gashi tunda shi tabbas akwai ingantattun hadisai a Sahihul Bukhari da Sahihul Muslim da suka nuna anyi hani da yinsa.
Manzon Allah SAW yana cewa Allah SWT Ya tsinewa mai karawa wata gashi da wadda tace a kara mata. Ki duba hadisi na 5934 a Bukhari da 2122 a Muslim.
A wani hadisin kuwa, Asma'u bint Abubakar(RA) tace wata mata tazo wurin Annabi SAW tace masa ta aurar da yarta amma lalura tasa gashin kan yar ya zube. Shin zata iya saka mata gashi? Sai Annabi SAW yayi kashedi ga mai karin gashi da wadda aka karawa. Bukhari 5479, Muslim 3962.
Malamai sun dauki karin gashi a matsayin yaudara sannan suka yi hani dashi. Akwai hadisin Mu'awiyya RA wanda yace Annabi SAW yace karin gashi yaudara ce. Sahihul Bukhari 3229.
Ta koma ga sauran daliban gaba daya. Ku kanku a ma'aunin hankali kunsan cewa akwai ha'inci a karin gashi. Banda asarar kudi da kuma warin da yake yi a kan mai sawa. Sannan duk mai karin gashi bata taba rufe kanta gaba daya domin tayi ne don a gani. Asali ma a shekarun baya muna ganin mace da karin gashi mun san ba musulma bace. Sai gashi a hankali mun dauki al'adu da dabiun wasu muna yi. Allah Ya shirye mu baki daya.
Sai tambayarki ta biyu akan masu shafa mai su canja kalar fatarsu daga baka ta koma fara. Wasu masu zalamar ma fararen ne suke kara kode fatarsu. To duk wannan yana cikin nau'in canja halitta wanda Allah Ya hana. Shaykh Ibn Uthaymeen yayi bayanin canja kalar fata na dindindin kamar bleaching a matsayin laifi kamar masu yin tatoo(zane da wuta ko abu mai kaifi a jiki) da kankare hakori ayi wushirya. Irin wadannan laifukan Annabi SAW ya sanar damu tsinuwar Allah ta tabbata ga masu yinsu. A bangaren lafiya kuwa munsan cewa babu wani nauin bleaching wanda bashi da illa ta kusa ko ta nesa. Wanda munsan Allah Ya hana mu cutar da kawunanmu. Ga zubar da mutumci da kimar mai yi a idon wadanda suke da hankali suke amfani dashi. Ga asarar kudi da sauran abubuwa marasa kyau. Allah Shine mafi sani daga kurakuran da muke aikatawa. Allah Yasa duk abinda zamuyi mu tsaya a iyakar da Yayi mana. Laifukanmu kuma Ya Yafe mana.
Gabadaya ajin suka ce Amin. Jikin yan matan duk yayi sanyi saboda ba'a rasa masu dan shafe shafe da masu dora gashi ko da a jikin acuci ne irin na Hajara. Zuhra tayi godiya ga Malama Rabia sosai. Duk bayanan da tayi kuwa ta rubuce su a yar takarda wanda zata nunawa Hajara shaida. Ta so ace Hajarar na nan tayi tambayar.
Daga kofar daki 'yan matan biyu suka ce Mama mun tafi. Ba tare da ta dago kanta daga laptop din gabanta ba tace Allah Ya kiyaye hanya ku gaishe su. Shiru taji ba amsa...tana dagowa taga sun tafi. A ranta tace na rasa saurin me yaran nan suke yi haka.
Hajiya ta fito daga dakin Alhaji taji karar mota. Sauri tayi kada su tafi ta basu sako su siyo mata a hanya idan suna dawowa. Kayan da ta gani a jikin Adabiyya ne yasa ta kara sauri tana kwala musu kira. A tsorace Adabiyya mai shirin shiga mota ta juyo. Hamida tace shikenan mun gama yawo. Ko kadan ba haka suka so ba. Hajiya na dakin Alhaji suka ki zuwa yi mata sallama. Ita kuma Mama daga bakin kofa suka yi mata basu bari iyayen nasu sunga kayan jikinsu ba. Hajiya ta fito har wajen rai a bace tace duk su shigo ciki.
Mama ta fito daga daki tace Hajiya lafiya? Kafin ta bata amsa yaran suka shigo. Ya Salam...Hamida? Adabiyya? Meye hakan kuma? Hajiya tace kema basu ce miki zasu tafi ba ko. Nima karar mota naji na fito da sauri ashe rabon idona ya gane min ne.
Hamida yar shekara ashirin da biyu jeans ne a jikinta da top wadda ko rabin cinya bata rufe mata ba. Duk ta dameta sai tayi rolling da karamin mayafi. Adabiyya mai shekaru shatara kuwa skirt ne a jikinta amma itama ya matse har shatin pant dinta ake gani. Shima don tafi yayarta jiki ne ta saka. Sai riga matsatstsiya karama har da wata belt a samanta an kara tamketa. Da dan karamin mayafinta. Hajiya ta kalli yayansu Nura. Kai mahaukacin ina ne da kana ganin sun fito a haka kake shirin jan mota. Ku fada min gaskiya ina kuke shirin zuwa. A tare suka ce gidan Yaya.
[9/25, 2:39 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU🗿6
Batul Mamman (Mrs)💖
Mama tace ni na rasa gane me ake yi a gidan Yayan naku ne? Jiya kunje kun ce aiki zaku taya Izzatu yau ma kun ce aikin zaku kara yi. Ko packing suke yi ne zasu tashi bamu sani ba, ta zauna akan kujera kusa da Hajiya tace ni a iya lissafi na ma ai sai karshen August za'ayi birthday din Nana. Kuma ita ce ta rage anyi na yayyenta. Hajiya ta tabe baki kina ma kokarin rikewa. Sun mayar da birthday tamkar wata ibada. Duk shekara sai anyi sau uku a gidan. Allah Ya kyauta.
Mama ta ce Nura fada min gaskiya me ake yi. Indai birthday ne an saba yi mun kuma hakura mun zuba ido. Tunda shima Hamzan bai ji maganar mu su dena ba ai matarsa bazata ji ba. Shiru yayi har sai da Hajiya ta daka masa tsawa...baka ji ana tambayarka ne? Adabiyya ta soma kuka dama ita akwai tsoro tace Hajiya party din wedding anniversary zasu yi na shekara goma da aure. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda su Mama ke fada. Hajiya ta mike tsaya tana magana a hankali...lalacewar Yayanku har ta kai nan? Allah Ya shirya. Daga nan dakin Alhaji ta koma ta cigaba da gyarawa.
Mama ta dubi yaran. Yanzu don Allah waye ya ce ku saka irin kayan nan? Yaushe ma kuka siya? Adabiyya tace jiya da muka je ne Anti Izzatu tace kananan kaya zamu saka yau. Shine muka ce bamu da masu kyau. Sai ta kaimu wani kanti ta siya mana. Mama tace eh lallai yarinyar nan bata nemawa kanta zaman lafiya a gidan miji. Shirun da taga munayi don bama son zama iyaye masu sa ido a lamarin gidan 'ya'yansu ne. Amma wallahi idan na bullo mata ta bayan gida sai ta gane karyar rayuwar turai take yi. An gayyaci su Mariya? Hamida tace eh duk su biyun. Har Yaya Ibrahim ma an gayyace shi da Anti Umma. Mama tace suma duk kananan kayan aka ce su saka? Hamida tace bamu sani ba. Mu da kannenta tace mu saka dai jiya.