Sashe 18
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
An kawo lefe akwati shida da kit. Komai Alhaji ne ya siya. Makota da yan uwa suna ta san barka. Washegari Baba yayi shatar mota suka dauki kayan suka wuce Ajingi. Nan ma kowa yace Zuhra tayi goshi. Yan uwanta suka shiga hada mata abubuwan da zata gyara kanta. Yi kawai take don kada a gane auren da matsala. Cikin wannan lokacin ko text bai taba hada Hamza da Zuhra ba. Har Umma sai da tace naga kwana biyu shiru yaron nan. Zuhra tayi yake muna waya kullum Umma. Wani aiki ne yake son karasawa kafin bikin. Umma tace to Allah Ya bada saa.
Alhaji ya sake tuntubar Hamza inda zai ajiye Zuhra. Takardun tsohon gidansa ya dauko ya mikawa Alhaji yace na riga na gama komai ya zama mallakin Nura. A sabon gidan akwai dakuna sai ta zauna a cikin daya. Alhaji yasa masa albarka sannan ya tura Mama ta gano dakin da za'a bawa Zuhra. Dakina ne babba a kasa da toilet a ciki. Mama tace sam amarya ma a sama zata zauna. Dakunan saman uku ne har an gama jera kayan su Khalifa a ciki. Bisa umarnin Alhaji dole aka dawo dasu kasa ba da son ran Izzatu ba aka sabonta fentin. Katon daki ne kamar na Izzatu da toilet. A ciki aka jerawa Zuhra gadonta daga wani gefe da yayi dan tudu. Dayan gefen kuma kujerunta da su tv. Mama tace kuma lallai ayi kitchen kabinet a daya daga cikin dakunan kasan saboda a raba musu kitchen.
An fara biki cikin kwanciyar hankali. Baba yana ta yabon Hamza saboda yana yawan kiransa a waya su gaisa. Hakan yasa suka cigaba da tunanin komai lafiya tsakaninsa da Zuhra. Anti Faiza kuma ta sake ja mata kunne akan tayi shiru da bakinta. Sannan tayi mata nasiha akan kwalliya da tsafta. Ni girar nan da kike ja ce bana so Zuhra. A shagwabe tace nufinki bana yin kyau Anti Faiza. Kinsan ni gaskiya zan fada miki. Bata miki kyau don ba iyawa kika yi ba. Kuma babu ruwanki da Izzatu ki kama kanki kinji ko. Zuhra ta gyada kai. Kinga yadda iyayensa suka tsaya miki sosai. Ina so ki kyautata musu daidai gwargwado. Babu fitsara ba rashin kunya. Nagode Anti Faiza in sha Allah zan kiyaye.
Anyi kamun Zuhra a unguwarsu washegari alhamis suka tafi Ajingi. Jumaa bayan masallaci aka daura auren Arch Hamza Nasir Hamza da Fatima Bashir Ajingi. Kai ka dauka auren yar wani maikudi ake yi saboda yadda mutane suka zo. Asabar da safe suka dawo kano aka fara shirin kai amarya.
Jikin Zuhra a sanyaye tunda aka daura auren. Shikenan zata bar iyayenta ta zauna da mutumin da babu soyayya a tsakaninsu. Ba'a tashi kuka ba sai da motocin daukar amarya suka zo. Aka rasa yadda zaayi a raba Zuhra da Umma. Gabadayansu kuka suke yi tamkar sun rabo kenan. Baba ya shigo yana fadan sun bar mutane a waje. Sai dai Zuhra na rungumeshi ya soma hawaye. Daki yaja hannunta suka koma. Yana kuka yana mata nasiha....uwata ki rinka tsafta kinji ko, ki rike Allah da ManzonSa SAW komai zaizo miki da sauki. Ki rinka taimakon mijinki. Kuma banda katuwar loma a gaban miji. Murmushi tayi hade da kuka ta sake fadawa jikinsa. Baba wa zaku rinka gani a gidan nan idan na tafi? Umma ce ta bata amsa bayan ta fyace hanci cikin yaran Yaya Shafiu matarsa tace na dauki duk wadda nake so. Baba ya dauko wata leda ya damka mata. Ga wannan dubu hamsin ne. Cikin kudin da na samu ne. Zan ajiye miki sauran. Ki rinka amfani dashi. Allah Yayi miki albarka. Basu fito ba sai da Malam babansu Hajara yazo ya buga kofar. Haka suka tafi tana ta rusa kuka ita da Hajara. Anti Faiza tace gulmammu duk wadda bata son auren sai mu koma da ita. [9/25, 3:48 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 29
Batul Mamman(Mrs)
Idan kaga dakin Zuhra baka ce na yar Mal Bashir kafinta bane. Tabbas duk dakunan gidan sunfi nata kaya masu kyau da tsada. To amma itama nata iyayen sunyi kokari sosai. Gida ya cika da yan kawo amarya. Izzatu ita kadai ce a daki dama ita ba mai rakice rakicen kawaye bace. Daga ita sai 'ya'yanta. Duk da tasawa ranta bazata kula Zuhra ko tayi kishinta ba sai da tayi kuka da aka shigo ana guda. Adabiyya da Hamida sunfi kowa rawar kafa Yaya yayi amarya. Hakuri da nasiha aka sake yi mata sannan suka tafi. Hajara da wasu yan uwanta ne karshen tafiya bayan sun sake gyara mata daki. Tashi tayi ta cire mayafin jikinta saboda su hudu ne kawai a dakin. Hajara tayi saurin mayar mata.
"Abinda ake son amarya da jan aji. Kin wani cire mayafi, idan wasu suka sake shigowa fa."
Sake cire mayafin tayi "ke kyaleni nasha iska. Da zafin gari zanji ko na rabuwa dasu Umma." Tana magana idanunta suka cika da hawaye.
Hajara ta ja hannunta suka koma kan gadon. Sake gyara mata dauri tayi aka fesa turare."to mu zamu tafi amarya. Kada ki tashi nasan ango na hanya. Kuma ki dena kukan su Umma haka. Irin haka sai yaga kamar auren dole aka yi muku.
A zuciyarta Zuhra tace meye maraba. A zahiri kuwa godiya tayi musu suka tafi. Sai da taji dakin tsit ta tashi tana leka ko ina. Wurin yayi kyau sosai ga kamshin turaren wutar da kanwar Umma ta hada mata. A hankali ta bude kofar toilet ta shiga. Wani murmushu tayi. Irin wannan bandaki kamar a gidan shugaban kasa. Ta mika hannu sink taga ruwa ya fito tun kafin ta kunna famfon. Zabura tayi da gudu zata fita don a zatonta famfon ya lalace ne , kada ace ita ta lalata. Ko da ta juyo sai taga ruwan ya dauke. Gabanta na dukan uku uku ta sake komawa tana mika hannu saman zata kunna sai taga bai sake fitowa ba. Har tayi ajiyar zuciya ta sake saka hannu a wurin fitar ruwa sai gashi ya sake fitowa. Fita kawai tayi ta rufe toilet din. Allah Yasa tayi sallar Isha. Dama nafila take son yi, sai ta hakura.
Tun tana jira ko angon nata zai shigo har ta fitar da rai. Dama bata sa a ka ba. Wuri ta samu a tsakiyar gadon tayi kwanciyarta ko kaya bata chanja ba. Bata dade ba bacci mai nauyi yayi gaba da ita.
Hamza bai shigo gidan ba sai shadaya da rabi na dare. Tun kayan jikinsa na daurin aure bai dawo gida ba. Babbar rigarsa da hula duk a hannu ya shigo dasu ya hadu da Tala tana ta gyara gidan. Ita kam dole a yaba mata wurin tsafta. A gajiye yake sosai, tayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama.
Sai da yaji ba dadi da ya kalli kofar dake hagun dakinsa. Wai matarsa ce a ciki. Ko alamar zuwa baiyi ba. Kofar dakin Izzatu ya taba yaji bata rufe ba. Muryarta a shake alamar taci kuka yaji tace
"Waye?"
Shiga yayi ta taso da sauri ta rungume shi tana kuka. Bai hanata ba sai da tayi shiru don kanta.
"Ina su Nana?" Ya tambaya lokacin da yake cire takalmansa.
"Suna sabon dakinsu. Tala zata rinka duba min su." Yadda take maganar kasan har yanzu tana bakin cikin canza musu daki da aka yi.
Kiss Hamza yayi mata a kumatu." Goodnight Izzy. Kije ki kwanta" Ya juya zai fita. Kansa ke ciwo kamar ya tsage. Yau baici wani abin kirki ba tun safe. Yana son tambayar Izzatu amma yasan idan bata da nutsuwa girki ma baya gabanta.
Saurin biyoshi tayi. Ta rike masa hannu" Don't tell me wurin Zuhra zaka kwana".
Hannun nata ya saki." No, dakina zani. Na gaji kema ki kwanta haka"
Kallon tuhuma take masa." Are you sure?". Kai ya gyada mata. Baya son magana saboda yadda kansa ke sarawa "Ko nazo mu kwana? Ina fargabar ranar da zaka kwana dakin yarinyar nan. Zan iya mutuwa saboda kishi." Ganin baya son magana yasa ta kyale shi. Tasan bazai fadi magana ba yaki cikawa.
Bayan ya tafi itama sake gyara jikinta tayi tabi bayansa. Da ya tambayeta abinci tace babu amma bari tayi sauri ta dafa masa wani abin. Jallop din taliya tayi masa. Kafin ta gama yayi wanka. Abinci yaci ya dan zauna ya fada masa. Suka kwanta shi da Izzatunsa. Ba wata hira tsakaninsu domin kuwa akwai abinda ke damunsa.
[9/25, 3:49 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 30
Batul Mamman(Mrs)
Zuhra anji dadin bacci saboda gajiyar da ta tara ta biki. Ba ita ta farka ba sai bayan tara. A firgice ta tashi ganin hasken rana a dakinta. Ko sallar asuba batayi ba. Sai da ta shiga bandakin ta tuna da matsalarsa ta jiya. Gashi ta makara sallah. Banda bahon wanka daga gefe wata yar matakala ce mai karamin bene da yayi kasa akwai shower a wurin. Kunnawa tayi ruwa ya watso mata saboda yayi karfi. Da kyar ta iya rage karfin ruwan. Cire kayanta tayi ta koma tayi wanka tare da alwala.
Tun kafin ta gama shiryawa cikinta ya soma kukan yunwa. Nan fa ake yinta. Zuhra bata jurar yunwa gashi tunda aka kawota ko motsi bataji a kofar dakin ba. Haka ta gama duk abinda zata yi ta sami wuri ta zauna. Tunanin iyayenta ne ya zo mata ta soma kuka.
Izzatu da Tala sun gama hada komai na breakfast suka jera akan dinning table. Sama ta hau ta kira Hamza. Sanye yake da jallabiya light brown sai kamshi yake. Yayi kyau sosai sai dai fuskarsa da ta zama maabociyar damuwa yan watannin nan. Yaransa duk suka yi masa kiss a goshi kamar yadda suma iyayen suka saba yi musu. Sannan suka zauna Izzatu tayi serving dinsu. Lomar farko da zai kai bakinsa ta tuna masa da Zuhra da ke daki tun jiya ko lekata baiyi ba. Tsaki tayi ya tura kujerarsa ya tashi.
"Baby what is wrong?" Izzatu ta tambaye shi itama tana mikewa tsaye.
Sama ya kalla ya sake yin tsaki "zan kira yarinyar nan tazo taci abinci ne."
A take Izzatu ta hade rai. "Ka bari Tala ta mika mata mana. Ai ba sai kaje dakinta ba."