Sashe 30
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai da ta gaji da tsayuwa sannan tayi sallama ta shiga. A kwance ta ganshi kan doguwar kujera ya zurfafa a tunani. Ba komai ke damunsa ba kamar harkar office ga mura tayi masa kamu sosai. Sallamarta ce ta tashe shi ya zauna. Batayi magana ba ta ajiye masa tray din a gabansa sannan ta koma ta dauko flask din. Kallon kayan yakeyi har ta dawo...ta ajiye flask din tana dan sosa kai tace uhmm dama nasa citta da kaninfari a ruwan. Idan baka so sai na tafasa wani. Dago kansa yayi jikinsa duk babu kwari sosai yace me yasa kika dafa da cittar? Naga kana mura ne zai bude maka kirji. To nagode da kulawarki, taimaka ki hada min amma kada kisa sugar. Tausayi ya bata sosai bata yi masa musu ba ta hada masa sannan ta fita ta koma kitchen.
Kazar dama daya ce tayi mata saura ta wanketa sosai ta hada da kayan kamshi da jajjagen kayan miya tayi farfesu. Yana kan wuta ta wanke shinkafa ta baza a tray sannan ta shiga yanka su cabbage, albasa, attaruhu, karas da koren wake. Harda grating din tafarnuwa kadan. Duk bayan ta gama ta sake komawa falon ko ya gama cin abincin. Ya gama amma fa bread din da rage bazata iya raba musu ita da maigadi ba saboda dama ba wani babba bane. Duk yadda take jin yunwa da ta kwashe kayan kwai biyu ta soya ta hadawa maigadi tea da bread din. Tace idan ya gama zai kai mata nikan shinkafa. Talle maigadi yanzu duk gidan babu wanda yake ganin girmansa kamar Zuhra yace to Hajiya nagode. Kitchen ta koma ta kashe farfesun sannan ta fara soya sauran naman. Tana yi ta hada tea ta zauna a kan kujera tana sha don bazata iya cin kwai zalla ba.
Bayan yaci abinci yasha magani jikinsa yayi dan kwari. Shiru babu motsin Zuhra sai yaji babu dadi. Sama yazo hawa yaji alamun har yanzu tana kitchen. Tea ya hangota tana sha shi kadai. Shiga yayi yana kallonta tea kadai kike sha ba bread? A'a na cinye bread din ne. Yadda tayi magabar yasa bai yarda ba ya duba dustbin dinta ina ledar. A zuciyarta tace kaji mutum da bin kwaf. Shiru tayi ba amsa yace bakya jina ne? Na bawa maigadi....kin me? Dama bashi da yawa kika bani, kuma sauran kika bawa maigadi to ke me zaki ci. Baki da Indomie ne? Murmushi kawai tayi ai yanzu zan dora abincin rana bana jin yunwa ma. Mamakinta yake...yanzu kamar Zuhra tasan ta hakura da abinda take so domin wani. Ji yayi ta sami wani gurbi a zuciyarsa. Hannunta ya kama suka koma falo...meyasa baki fada min ba kika yi shiru zaki kwari kanki. Wasa ta soma yi da yatsunta taki kallonsa..ai naga baka da lafiya kuma zan iya jira. Lallai yau ya koyi darasi a wurin Zuhra...shi bai taba bata kudin siyan wani abu ba yasan da kudinta ta sayi bread din kuma ta bashi. Kallon da yake mata yasa duk ta kasa sakewa . Shi kuwa hannu yasa yana shafa gefen fuskarta har sai da tsigar jikinta ta tashi. Nagode kinji, Allah Ya baki lada, kin nuna damuwa da rashin lafiyata sannan kin iya hakura da abinci don wani yaji dadi. Amma daga yau ki rinka fadamin duk abinda kike bukata, tace to cike da kunya sannan ya saketa ta koma aikinta zuciyarta na bugawa da sauri. Sauran naman ta kwashe ta bawa maigadi nikan shinkafar sannan taje tayi wanka. Har ta dauko foundation sai ta tuna da kwalliyar da ya gyara mata ranar da suka fita. Irin yadda yayi mata haka tayi aka dauki deodorant da body spray aka fesa. Sannan kayanta ma suka sha turare mai kamshi.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 48
Batul Mamman(Mrs)
Hamza na falonsa ya gama waya da assistant director akan wasu ayyuka. Duk yayi musu bayanin yadda yake so ayi aikin da alkawarin idan yaji sauki anjima zai shiga office. Bayan ya gama Izzatu ya kira. Hira kadan suka yi ya gaisa da su Khalifa tace masa tana son wucewa Abuja idan an gama bikin. Dad dinta ne zai tafi Japan shine zata je yi masa sallama sai wata lahadin zata dawo. Ransa a bace yace Izzy ba haka muka yi dake ba. I need you here, bama ni da lafiya. Izzy tace kayi hakuri baby amma Dad zaiyi wata biyu kaga ya kamata naje muyi sallama. Idan yace bai amince bama yasan sai taje ko tasa mamanta ta kira shi a waya. Abin mamakin ma tsakaninsa da Allah rashin dawowar tata bai wani dameshi ba. Shi da baya iya nisa da ita...yace to su Khalifa kinsan zasuyi missing school da yawa ko. Eh zasu taho da Tala ranar lahadin amma da Nana zan tafi Abujan. Bye baby, love you. Dip ta ajiye wayar, rike tasa wayar yayi a hannu yana mamakin Izzatu. Ko sau daya bata yi masa sannu ba duk da muryarsa data canja ko bai fada ba za'a gane bashi da lafiya. Har tunani yake yi wai dama haka take masa ko yanzu ne dai saboda bikin da suke yi.
Zuhra na saukowa aka kawo wuta. Tsabar murna yasa tayi ihu har sai da Hamza yaji. Da sauri ya fito yaga abinda ya sameta sai yaga tana ta juyi a falo tana kiran nepa, nepa.... baki ya rike yana kallon ikon Allah, sai kace wata karamar yarinya sai tsalle take yi. Riga da skirt ta saka na yadi mai laushi. Dinkin ya kamata tsam ta daura dankwalinta. Duk da ba wata kwalliya tayi sosai ba amma tayi masa kyau. Gabadaya surar jikinta ta fito sai tuna masa daren jiya take. Sannu da aiki yar kauye ya fada yana tsaye a bakin koma.
Da farko tsoro taji har zata gudu sai kuma ta tsaya ta fara neman wuyan hijab dinta ta saka. Jira yayi ta saka din sannan ya karasa gabanta ya kama kasan hijabin. Hannunta tasa tana neman kwacewa ya janyota gabadaya jikinsa. A take ta fara rawar jiki tana cewa kayi hakuri na dena tsallen. Sosai ya rungumeta yana kallon fuskarta ya cire mata hijab din cikin nutsuwa sannan ya saketa. Kirjinta ta fara kokarin rufewa yace ke jiki ba jiki ba kiyi ta wani rufewa. Haushi taji ta dan tura baki sai ta fara juyi a gabansa tace a hakan? Wallahi ina da jiki, kaga fa...dariyar da yake mata yana cewa juya na gani da kyau yan mata yasa ta bar abinda take yi ta soma kokarin kwatar hijab dinta. Hannunsa ya daga sama tace to na bar maka bari na dauko wani. Baifi taku biyu tayi ba ya jawota jikinsa. Hannuwansa na gaban kirjinta ya dan rage tsaho daidai da kunnenta...ki hakura da hijab din kinga akwai zafi. Kuma naga ashe kina da jikin da zan kalla. Yana magana taji yasa hannunsa a kafadarta yana mayar mata da hannuwan breziyarta da suka fito. Daga daren jiya zuwa yau Hamza yasa Zuhra tsananin jin kunya. Yadda ya rufe mata jiki gabadaya ta baya yasa ta kasa motsi. Zuciyarta ce kawai take bugawa da sauri. Tana wannan yanayin har ya saketa bata sani ba. Ganinsa kawai tayi a gabanta yana murmushin da yanzu take yawan gani tare dashi. Hada ido suka yi ta kawar da kanta, a hankali tace duk kasa ni jin kunya. Sai ka rinka wayon taba min jiki. Kuma dai kasan babu kyau. Ya daga gira kina matar tawa. Tace to ba sakina zaka yi ba. Tana fada ta wuce kitchen ta barshi a tsaye. Maganar Zuhra tasa ya shiga damuwa sosai.
Dambun shinkafa ta hada mai rai da lafiya. Ta rinka yawo tsakanin falo da kitchen har abincin ya dahu. Daya da yan mintuna ta gama ta mikawa maigadi. Shi kam yana jindadin sauyin da ake samu na girki a gidan nan. Gashi harda ruwan sanyi tunda an kawo wuta. Na Hamza ma ta hada masa komai a tray ta shiga falonsa ta ajiye sai dai baya ciki. Yunwa take ji sosai domin yau tayi dauriya. Nata tayi niyar zuwa ta diba a kitchen sai taga wata kofa ta bude ashe da toilet a wurin. Tashi tayi zata gudu yace dawo ki zauna fita zanyi, da alama alwala yayi. Zan canja kaya naje office zaman gidan ya isheni. Ba komai ke damunsa ba sai maganar Zuhra ta saki. Ya rasa gane yana son zancen sakin nan yanzu ko kuwa. Da 'yar damuwa a fuskarta tace amma baka da lafiya, ka hakura mana. Yana jindadin yadda take kulawa dashi yace bazan dade ba in sha Allah. A gaban tray din ya tsuguna Me kika dafa mana ne...yar kazama ta iya girki. Tray din ta dauka tunda ni kazama ce ka nemi wani a waje. Yi hakuri ki kawo kinji, ai kinfi kowa tsafta a gidan nan. Bubbude flask din yayi yaga dambun shinkafa tayi da farfesun kaza. A take yawunsa ya tsinke. Wai me yake damunka ne Hamza da kaga abincin sai ka rude kamar wani mayunwaci. Kinsan abincin da Hajiya tafi so kenan dambu ko wane iri ne. Zuhra tace da gaske? tare da dauke flask din da ta zuba masa nasa. Bari naje na juye sauran ina ga zai kai cin mutum uku idan aka hada. Tana magana tana neman fita daga falon. Hamza yace ke dawo bangane me kike nufi ba? Ya daga kawo min abinci ko tasting banyi ba kin dauke. Buga kafa tayi irin ya ma zai ki ganewa...yanzu fa kace min Hajiya na son dambu. Zan hada da sauran sai ka kai mata. Bari nayi sauri ko taliya na dafa mana tunda kaima fita zaka yi.