← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 67

Sashe 35

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai da suka gama azkar sannan yace mata yau kin janyo mun makara sallar asuba. Tashi tayi tana ninke abin sallah, babu ruwana ko yanzu ma ai na rigaka tashi. Gadon ta tafi zata gyara Hamza ya haye ya zauna a tsakiya yace ni bacci bai isheni ba kizo mu kwanta. Zuhra tace kitchen zani kaga muna da baki. Kinga zo kiyi kwanciyarki ya fada yana mika mata hannu. Indai wadannan yaran ne sai su kai shadaya suna bacci. Zuhra tace to maigadi fa. Tashi Hamza yayi ya zagaya ta bayanta, bata ankara ba taji ya dagata cak ya sauketa a taskiyar gadon. Tsoro taji ta kankame shi ya kwanto a jikinta yana kallon yadda ta runtse idanunta. Sonta yake ji yana shigarsa ko ta ina. Idan da wani ne ya fada masa zai so ta bazai taba yarda ba. Kamar mai rada yace Cutie ba'a son yiwa miji musu. Mu danyi bacci kadan sai ki tashi. A jikinsa ya kwantar da ita tasa hannuwanta duk biyu ta rufe fuska. Matsananciyar kunyarsa take ji fiye da ta da. Kanta na kirjinsa ya sake sassauta murya. In cire miki hijab din kisha iska? Maimakon ta bashi amsa kama jikinta tayi kam. Bai sake magana ba sai bayanta da yake shafawa a hankali.

Har bacci ya soma daukarsa ita kuwa ta zata shima idonsa biyu tace Ya Hamza akan maganar da mukayi jiya akwai shawarar da nake son baka amma don Allah idan hakan laifi ne kayi hakuri. Ina jinki yace cikin muryar bacci. Ta tashi zaune, kayi hakuri bansan ka soma bacci ba. Bude ido yayi yana kallonta, babu komai ina jinki. Komai nata kishiyar na Izzatu ne.

A nutse ta soma magana kamar ba ita ba. "Nasan duk wadanda suka san abinda ke faruwa da kai sun baka shawara kila ma irin wadda zan baka ko wadda tafi ta. Lokacin da tsautsayi ya ritsa da Baba a wurin aikinsu mun sha wahala. Sanda yake da duka hannuwansa munfi wadata da rufin asiri. Da aka yanke hannun yana jinya a gida ga kudin magani da sauran abubuwa na yau da gobe ya kasance an koro ni daga makaranta. Ba don Malam babansu Hajara ba abinci ma sai ya gagare mu wata rana duk da a haka Baba ya fishi rufin asiri. Wata rana Umma tace naje makota na sanar dasu zata fara wainar flawa. Ranar baka ga kukan da nayi ba." Hawayen ta soma Hamza ya sa yatsansa ya share mata. Ta cigaba da magana "bakincikina mun talauce har abin ya kaimu ga sayar da wainar flawa. Ina kuka na sanar da Umma bazani ba, ta soma fada nace so take kawayena suyi min dariya. Sai ta zaunar dani ta dena fada tace min. Zuhra aure ba abin wasa bane. Aljannar mace kuma tana karkashin kafar mijinta. Ma'ana samun aljannarta na tattare da yardar mijinta. Lokacin da babanki yake da lafiya ya wadata mu Alhamdulillah. Yanzu kuma lalura ta same shi 'yan uwa da abokan arziki duk sunyi mana kokari amma dole mu yiwa kanmu. Idan miji ya shiga matsala mace ana so tayi iya kokarinta da yin abinda bai sabawa shari'ah ba wurin kyautata rayuwarsu. Idan har bata da hali kuma sai ta taya shi da addua dare da rana har Allah Ya kawo musu sauki. Kada ki taba daukar maganar masu cewa idan mace ta taimaki mijinta wata rana zai saka mata da tsiya. Dama don Allah kika yi saboda haka ki nemi lada a wurinSa. Tun daga ranar na koyi tattali da adana abu saboda na ragewa Baba kashe kudi. Idan ya siyo min turare ko sabulu na rinka janjaninsa har kazanta ta dan kamani. Amma dai yanzu na dena ko " tayi maganar da murmushi sannan ta dago kanta suka hada ido da Hamza." Kasan me yasa na baka labarin nan?" Yace "sai kin fada". Zuhra ta gyara zama." Ni a shawarar da zan baka Ya Hamza kafin komai ya daidaita ka rage kashe kudi. Misali tunda nazo gidannan tun karfe shida na yamma ake kunna inji har tara na safe. Wani lokacin da rana ma sai an kunna duk yadda abubuwa suke tsada yanzu. Kuma na kula ranar alhamis a waje kake siyo abinci. Gashi yawancin safiya kullum za'a soyawa su Khalifa kwai kowa bibbiyu. Suci rabi su bar rabi ya shiga shara." Ta dan daga hannu " ba cewa nayi a takurasu ba amma a rage irin wannan. A koya musu yau su sami yadda suke so gobe su hakura saboda halin rayuwa. Injin ma a barshi sai kamar tara ko goma na dare a kunna. Da duk abubuwan da kasan basu da mahimmanci sai a barsu."

Tunda Zuhra ta fara magana Hamza yake kallonta. Kallo irin na tsabar soyayya da mutuntawa. Yarinya ce Zuhra sosai a kanshi da Izzatu amma duk yadda suke ganin shirmenta ta san abinda take yi. Matsalar gabansa bata dame shi ba kamar yadda yake son gina soyayyarsa a zuciyar amaryarsa.

Zuhra duk ta tsargu da kallon da yake mata tace Ya Hamza na shiga abinda bai kamata ba ko? Nasan duk aikin Maman Khalifa ne. Dama kawai nayi ne don nima na sami ladan da mata ke samu a gidan aure. Kaga bansan lokacin da zan sake aure ba idan muka rabu. Tayi masa murmushinta mai kyau...shiyasa nake son samun lada a iya zaman da zamuyi.

Kasa magana yayi sai mamakinta kawai. Dan taba shi tayi saboda yadda ya kasa dena kallonta. Ba tare da ya dauke idonsa daga kanta ba ya dorata kan cinyarsa tare da rungumeta sosai a jikinsa. Sannan yace nagode sosai Fatima, Allah Yayi miki albarka. Abinda na fada miki jiya babu wanda ya sani sai ke sai mutane kadan a office dinmu saboda haka ki rike min sirrina. Kuma na baki dama ki fada min duk abinda kika ga ya dace na gyara ni Hamza nayi miki alqawari zan gyara. So yake yace mata yana sonta amma baya son tsorata ta don yasan tana tsoron halin Izzy. A hankali zai bi da ita har sai yasa taji irin yadda yake ji game da ita a tasa zuciyar.

Ba jimawa ta fito daga dakin ta sauka kasa. Adabiyya da Hamida ta gani sun share ko'ina sun dafa tea. Abinda za'a ci ne basu sani ba. Kunyarsu ta kamata ta soma 'yan kame kame. Yau makara nayi wallahi. Kuyi hakuri....da yake su Jidda sun kawo mata dankali tace rbari a soya dankali. Hamida tace gaskiya Anti dankali akwai bata lokaci kawai muci indomie. Tace to Adabiyya ta dafa musu harda ita, zata soyawa Ya Hamza shi kadai.
[10/2, 9:57 AM] +234 803 220 0468: AL'ADUN WASU 55

Batul Mamman(Mrs)

Zuhra na hada kayan wanki a dakinta Hamza ya shigo yace su shirya yaji jiya suna zancen zuwa salon ita da su Adabiyya. Taji dadin hakan sosai dama a dalilin bata son auren taki yarda a saka mata relaxer a kanta wai kada ya rinka hanata zuwa tunda yace kuntata mata zai yi a gidansa. Dubu ashirin ya bata ita da su Hamida kowa yayi abinda yake so. Zuhra ta bude baki, wannan kudin yayi yawa har ka manta zancen da muka yi dazu? Ban manta ba baki nayi ki rike a hannunki koda bukata zata zo miki. Tayi ta masa godiya duk da a ganinta kudin sunyi yawa. Shabiyu saura suka fita tare ya sauke su yace zai je unguwa idan sun kusa gamawa su kira shi. Zuhra tace ai babu nisa sosai muna tafe muna hira ma sai mu koma. Su Adabiyya dake bayan motar yacewa su fita su jirata a ciki. Suna tafe suna waige da yiwa yayan nasu dariya har suka shige. Ya mayar da hankalinsa gareta. Akwai abinda kike so na taho miki dashi ne? Ta girgiza kai Allah Yasa kaje lafiya ka dawo lafiya. Allah Ya bada abinda ake nema. Ya nuna mata jindadinsa da adduarta yace nagode sai na dawo. Da ta fito wata mata ta gani ga baby a hannunta ga jaka da zanin goyo duk kayan sun mata yawa. Da sauri ta karasa ta tare mata jakar da ke shirin faduwa. Matar tayi murmushi kai amma nagode miki. Sai da na zo nan hannun jakar ya tsinke ga Muhsina ta min kuka. Zuhra ta karbi yarinyar matar ta hade bakin jakarta da zanin goyon suka shiga tare. Har su Adabiyya sun kama mata layi da yake weekend ne wurin ya cika. Wuri daya Zuhra da matar suka zauna tana ta yiwa yarinyar wasa ita kuma tana dariya. Matar tace ni sunana Sa'adatu ke fa? Zuhra ta fada mata sunanta tace ina son baby dinnan. Sa'adatu tayi dariya ai naga alama kema tana sonki don kyuya take yiwa mutane amma gashi tana miki dariya. Suna hira matar tace ita har lalle zata yi. Hamida ta taso daga inda Adabiyya ke tayata tsifa Anti don Allah kema kiyi lallen wallahi Yaya yana so. Duk sallah baya fashin bamu kudin lalle ko Adabiyya. Adabiyya tace ce eh.
Chapter 35 · 0% Book details