Sashe 12
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Su Zuhra ana ta shirye shiryen bikin Hajara zama ya gagare su. Kullum sai sun fita. Sune kasuwa ko wurin mai dinki. Ana saura kwana biyu kamu ta dawo daga raka Hajara saloon din unguwarsu taji Baba da Umma suna magana a tsakar gida. Allah Yasa Hajaran ta wuce gida. Baba ne yake cewa...ina farinciki da auren Hajara amma lamarin Zuhra na damuna. Duk samarin da ke zuwa sai kiga babu na aure. Bana son tayi ta zama a gida tunda ba karatu take yi ba. Umma tace haka ne, kuma abin ba zai dameta ba yanzu sai taga an kai Hajara dakinta. Amma da kake damuwa yarinyar nan ko shekara ashirin da daya bata cika ba. Baba yace to ai dai ta kusa. Shekaranjiya da naje Ajingi baki ji fadan da Inna tayi ba wai mun sa yarinya a gaba munki yi mata aure. Yaya Sabiu kuma sai cewa yayi ko Garzali ne na wajensa a hada su tunda shima yaki karatun. Zuhra tana daga soro ta dafe kirji....Yaya Garzali kuma? Allah Ya kiyaye. Mutum mai shegen ji da kai kamar wani mai mulki. Baba taji yace duk da ba kudi gareni ba bana fatan yarinyar nan ta auri mara ilimi irinta. Ba mai kudi nake jira ba amma ina mata fatan samun rufin asiri a rayuwarta. Umma tace Allah Yayi mana zabi nagari. Idan ta dawo sai kayi mata maganar Garzalin tunda a gaban Inna akayi ya kamata ta sani.
Hawaye ne suka saukowa Zuhra ba tare da ta sani ba. Allah Sarki Baba da Umma. Sai yanzu take jin inama ta dan mayar da hankali a makaranta. Wayarta ta zaro daga yar jakarta ta bude sakonnin da yau kwana uku kenan kullum sai anyi mata safe da dare. Ta rasa ko waye yake mata wadannan sakonnin soyayya. Lokaci yayi da zata dena sharewa kila alkhairin da Baba ke jira ne ya tunkaro ta. Ta goge fuska ta shiga ciki.
Jikin Umma ta fada tace wash Allah nagaji sosai. Umma ta ture ta to dagani kada ki karasa kashin tsufa. Zuhra ta tashi ta koma kusa da Baba. Tana dan daga gira tace in kwanta a jikinka Baban yara? Rankwashi ya kawo mata ta goce...yarinyar nan kin gama rainani. Wayarta ta mika masa Baba sirri nazo muyi. Umma tace ai sai dai idan na fita amma babu inda zani ayi a gabana. Shi kuma Baba yana murmushi yace to ko daki zamu shiga. Dariya kawai tayi ta bashi wayarta ta nuna masa sakonnin text da ake yi mata. Baba ya karanta yafi sau uku uku murmushinsa na fadada yace waye wannan? Zuhra tace nima ban san shi ba. Amma kaga a sakon karshe yace yana jiran amincewata ne ya gabatar da kansa wurinka. Da izininka zai fara zuwa. Duk dadi ya kama Baba sai murna yake. Umma tace kuyi min bayani mana. Baba yace saurayi muka yi. Umma tace kai Baban Zuhra akan yar nan ka iya rufe ido ka manta kai babanta ne. Yace to da 'yar wani kike so nayi. Kinga Zuhra ki tura masa da amsa mai dadi...banda shirme kinji ko sannan kice kin amince ya gabatar da kansa. Tunda yace yana aiki a wani kamfani ai kinga ko ba komai da dan iliminsa ko da na sakandare ne.
Karfe tara na dare text ya sake shigowa wayar Zuhra.
** Kewarki ta dameni, ki amince na nuna miki soyayyata gareki**
Wani juyi Zuhra ta rinka yi cike da tsananin jindadi. A yan kwanakin nan ta tsinci kanta da jiran text duk safiya da dare. Reply ta tura kamar yadda Baba ya bata shawara
** Na amince**
Har Izzatu ta kwanta taji shigowar text. Hamza ya kai hannu zai dauki wayarsa tayi saurin dauka. Yace ni da wayata zaki min kwace? Tayi murmushi ta bude ta karanta. Dadi ne ya kamata. Hamza yace text din waye ne kike murmushi. Kamar yadda ta saba saurin gogewa tayi tace kyale tallan MTN ne.
[9/25, 3:37 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿19
Batul Mamman(Mrs)💖
Su Zuhra an fara biki. Sunyi kamu ranar laraba a wani fili nan cikin layinsu. Yan makarantarsu da yawa sun zo bikin. Wata cikinsu mai suna Ikilima ce tayiwa amarya kwalliya. Zuhra tana daura dankwalin ankonta Ikilima tace don Allah ki bari nayi miki kwalliya. Wannan fuskar taki duk kin bata ta. Tissue tasa ta goge fuskar Zuhra sannan tayi mata kwalliya. Nan kawayensu suka rinka cewa tayi kyau sosai.
Washegari da babu abinda zasu yi amma an dan taru a gidansu Hajara. Yan mata kuma suna gidansu Zuhra. Tana zaune ana yi mata kitso wayarta tayi kara. Ta daga taga sunan Izzatu. Hankalinta ya dan tashi bata gama mata sakar yaranta ba. Hakuri ta soma bata tana daga wayar.
Izzatu tace ba komai ai nasan kuna bikin kanwar Faiza. Ni magana daban na bugo muyi.
Zuhra tace to ina ji.
Izzatu tayi yar dariya, dama ranar da kika zo gidana kina fita kanina ya shigo kila ma kin ganshi.
Zuhra ta dan yi tunani kai babu kowa a hanyar.
Izzatu tayi saurin gyara zancen kada Zuhra ta gane. Cewa yayi ya ganki don yana shigowa tambayata yayi ko kina da aure. Nace a'a. Shine ya dame ni har na bashi numbarki. Ina tsammani ya kiraki ko yayi text.
Daga daya bangaren Zuhra taji wata murya mai dadi ana cewa haba Izzatu na fada miki ban fara yi mata waya ba sai naga babanta. Zuciyarta har wani saurin bugawa tayi, ba dai mai yi mata text dinnan bane.
Izzatu ta katse mata tunani yace sai gobe zai zo gidanku magana da babanki bayan magariba. To a ranar zamu tashi shine za'ayi walima a sabon gidan. Don Allah kizo in nuna miki shi. Ni a ganina gara ku fara haduwa kafin maganar taje ga iyaye. Kuma sunansa Hamza don yace bai fada miki ba ko.
Lallai da gaske Izzatu take don jiya yayi mata text yace zai zo ranar Jumaa. A take taji tana jin kunyar Izzatu. Ashe ma dan gayu ne indai kanin Izzatu ne. Ji tayi ance Zuhra zaki iya zuwa din ko ma hadu a gida? Farinciki fal zuciyarta ta rike wayar tana murmushi. Wai ita ce saurayi ke mata magana irin haka. A hankali tace zanzo in sha Allah. Daga nan ta ajiye wayar.
Izzatu ta kalli kaninta Walid tace gobe akwai show a gidan nan. Walid yace amma sis sai naji ba dadi kuma. Dungure masa kai tayi...to kill joy idan ka ga dama kada ma kazo. Ya gyara face cap dinsa da ta karkace wai da yaya kike daukar wayar Hamza ne bai sani ba? An gaya maka ni din ta wasa ce? Baya amfani da wayar sosai sai nace ya bani aronta don kada Zuhra tayi text ko waya yana office.
Bayan an watse ne ta sanar da Umma yadda suka yi da su Izzatu. Umma tace ba komai amma idan kinje kada ki dade saboda lanchin din Hajara. Ku ne iyayen biki. Haba ai bazan dade ba Umma. Don tana ta rokona ne ma. Umma tace ba komai ki yi sauri dai. Daga nan fita tayi taje ta sanar da aminiyarta Hajara. Amma fa ban fadawa Umma zamu hadu dashi ba. Hajara tayi mata dundu tana dariya tace yarinya ta fara sanin soyayya. Tana dawowa gida ta tarar da Umma tana wanke wata farar shaddar Baba mai kyau. Zuhra tace gobe zashi daurin aure ne? Umma tace ba kince yaron nan Hamza zai zo gaishe shi ba, ai gara a ganshi da kwarjininsa shima. Wani dadi Zuhra taji tace to kawo na karasa wankin. Umma tace bari dauraya ta rage min.
Biyun dare ta wuce sannan aka kawo wuta. Zuhra ta tashi tana magagin bacci dama jiran wutar take yi. Da sanda ta lallaba ta dauko kayan Baba daga shanya tazo ta goge masa. Itama cikin kayanta na bikin Hajara ta sake gogewa. Daya zata je gidan Izzatu walimar tarewa, dayan kuma sai da yamma idan Hamza yazo.
Rigunan sanyin da ta karasa sakawa ta saka a leda ta gama shirinta tsaf. Shigen gyaran girar da kawarta tayi mata a kamun Hajara ta kokarta tayi. Sai dai tata tayi girma da baki da yawa. Leben nan yasha janbaki purple don ance mata shi ake yayi yanzu. Tayi daurin dankwalinta sannan ta kawo katon mayafi ta dora a kai. Umma ta yaba da kwalliyar tace idan kin kai mata kayan kada ki karbi kudi tunda kinga inda rabo kaninta zaki aura. Zuhra tayi dan murmushi tace to Umma. Ko daga nesa ka hangota za ka san tana cikin nishadi. A haka ta je gidan anti Faiza don tare zasu tafi. Anti Faiza tace naga alama dai Izzatu na ji dake. To dai muyi sauri kinga akwai sauran shiri a gabanmu. Ni ba don aikin meatpie dinta ba ai ba inda zani. Sai dai ta bani fiye da kudin aikin shiyasa na karba. Dreba Izzatu ta turo ya dauki su Zuhra saboda kulolin da Anti Faiza ta zuba meatpie har uku ne.
Hamza ya gama magana da lauyansa an gama komai a takardun tsohon gidansa. Da daddare in Allah Ya yarda zai kaiwa Alhaji a bawa kaninsa Nura. Idan yaso in ya tashi aure sai a kara gyara gidan. Ya dan shafi kansa yasan yau iyayensa zasuyi farinciki da abinda yayi musamman Mama. Sakonnin email dinsa ya bude yana karantawa don yau bazai koma gida da wuri ba sai sun gama walimarsu. A firgice ya tashi yana kiran Inuwa sakatare. Inuwa ya shigo da sauri yana tambayar ko lafiya. Hamza ya nuna masa wani sako da aka turo daga Mr Peter wakilin turawan da suka hada gwiwa dashi. Gumi ke keto masa ko ta ina yace Inuwa mutanen nan sunsha kwaya ne da zasu ce wai suna yi min tuni akan basu ribar da muka samu a watannin nan shida gaba daya. Ya ture takardun tebur dinsa. Ni ban fahimce su ba kwata kwata ina aka taba kasuwanci haka.. Inuwa yace ranka ya dade ka manta a contract din ance ribar wata shidan farko tasu ce. Daga nan kuma sai ku rinka raba ribar kai da su. Hamza ya daka tsawa inji uban wa??? Inuwa ya zabura ya matsa gefe.