← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 67

Sashe 14

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A falo suka zauna Zuhra da Anti Faiza suka rakube jikin kujera. Mariya ta bada labarin abinda idanunta suka gane mata a gidan Yaya. Mama da Hajiya sai salati suke. Ita kam Hajiya har kunya taji ace wai Hamza danta ne kuma na fari ma. Alhaji ya dubi su Zuhra yace ko zaku yi mana bayanin yadda abin ya samo asali. Nan Zuhra ta soma basu labari. Tana yi tana kuka. Su Ummahani sunji tausayinta sosai. Alhaji yayi murmushin bacin rai Mariya ku tashi ku kaisu gida. Sai ku gane mana gidan. In sha Allah anjima zamu zo gidan nayi magana da mahaifinki. Amma kafin nan don Allah kada ki sanar dasu komai. Zan gyara matsalar in sha Allah. Mama ta matsa kusa dasu ta rike hannun Zuhra ki yi hakuri kinji 'yata. In Allah Ya yarda Alhaji zai share miki hawaye kuma zai hukuntasu daidai da abinda suka yi miki. Zuhra ta gyada kai ni dama dariyar ce ta fi bani haushi. Anti Faiza tace to ba an baki hakuri ba. Tashi mu tafi. Bayan sun fita Mama tace Hajiya ya kika yi shiru? Hajiya tace hmmm to me zan ce? Kina kallo kullum lamarin gidan yaron nan kara lalacewa yake. Wai april fool sai kace wasu kasurguman kafirai. Na rasa yadda ake suke kwakulo duk wata al'adar banza suna dabbaka ta. Alhaji yace ku kyale ni dashi. Alkawari ne tsakaninmu akan idan haka ta sake faruwa zan hukunta shi.....wani murmushi kawai Alhaji Nasiru yayi. Sai na nunawa yaron nan nima ina riko da namu al'adun nagari.

Izzatu ta rike kumatu ta soma kuka. Ita Hamza zai mara a gaban mutane. Sai a lokacin ta kula kowa ya watse sai yan gidansu da mamanta. Da sauri ta nufi wurinta zata rungumeta, sai taga maman tata ta matsa. Izzatu ta zaro ido meye ma'anar hakan. Raliya mahaifiyar su Izzatu ta kalli 'yarta fuskarta na nuna alamun rashin jindadi tace Izzatu that was extreme. Ban taba nuna damuwata ba idan kuna wasanku ke da yan uwanki. Kuma ni mutum ce da ta yarda a bar yaro ya sake yayi abinda ransa yake so. Amma ban yarda da cin zarafin wani don nishadi ba. Me yarinyar tayi miki haka da har zaki kirawota har gidanki ki mayar da ita laughing stock(abin dariya) a gaban mutane? Hawaye ne ya cigaba da sauka daga idanun Izzatu tace Mum har me nayi mata? Kawai ba'a fahimceni bane amma yi nayi don ayi dariya. Raliya tace kada ki manta yarinyar nan nan mutum ce kamar kowa. Ya zaki ji idan kika sa rai da abu kamar soyayya sai kawai ace miki wasa ne har a biki da dariya? ta dubi sauran 'ya'yanta ku tashi mu tafi. Laifinmu ne ni da Dad dinku da muka dora ku kan al'adun da basu dace da society dinmu ba. Gashi mun dawo Nigeria kina ta samun matsala da inlaws dinki. Izzatu na kallo duk suka fita jiki a sanyaye.

Share hawayenta tayi ta hau sama. A hankali ta bude kofar dakin ta hango Hamza zaune a kan kujerar gaban madubi ya dafe kansa. Karasa shiga tayi ta tsaya a gabansa, ka kyauta Hamza. You slapped me for no reason. A yadda ya dago kansa sai da ta razana ta matsa baya da sauri. Gani take wani marin zai kai mata. Har wani huci taga yana yi saboda yadda ransa yake a bace. Izzy kinsan abinda kika yi kuwa? Ta dan sha kunu ita a dole bazata nuna masa ta yarda tayi laifi ba. Don kawai nayi april fool shikenan sai ya zama laifi. Har ka manta babu shekarar da bama yiwa juna. Last year kaya ka kawo min wai na fadar kashiya. Sai da na gama yarda nasha kukana sannan kace april fool. Shi inda ya dosa daban da abinda take fada. Saboda tashin hankalin da yake ciki ya manta da wani wasan april fool da tayi. Wannan last year ne, har kin manta nace mun dena duk irin wadannan abubuwan. Tace ban manta ba amma ai wannan ba na kudi bane. Ya rasa yadda zaiyi da ita. Kinga sami wuri ki zauna kin tsaya min a ka. Bakin gado ta zauna tana fuskantarsa. Izzatu ya kira sunanta..... naam. Kin taba goge min text da Inuwa ya turo ranar wedding anniversary dinmu? Dan tunani tayi tace eh, amma na karanta farkon sakon na kuma fada maka abinda nagani. Shine duk ka wani daure min fuska har da mari. To wallahi bazan hakura ba. Ta fadi maganar ne tana tashi. Bata ankara ba taji ya janyota iya karfinsa ya hadata da bango. Da sauri yake numfashi don ji yake kamar zuciyarsa zata iya bugawa. Idanunsa duk sun kankance. Sai a lokacin Izzatu ta ji tsoro tayi tunanin tambayarsa abinda ya same shi. Kafin tayi magana yace daga yau idan kika sake daukar min waya sai nayi miki abinda baki taba tsammani ba. A dalilin wayar karyar da kika yi kika ce Junior ya karye da deleting text dina da kika yi karayar arziki na iya samuna. Ga mamakinta hawaye ta ga ya zubo daga idanunsa, abinda bata taba gani ba. Nan da nan ta rikice, babyna ya zamuyi idan ka talauce? Zamu sami abincin da zamu ci ko sai Daddyna ya taimaka mana? Gashi kayi min alkawarin zaka canja min mota. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya ke nanatawa. Zancen ace ransa ya baci da maganarta ma bata lokaci ne. Izzatu dama baki da hankali??? Tace bangane ba. Ya daga murya ya soma fada... ina fada miki matsalata kina zancen canjin mota. To hell with canjin motar taki. Ya dauki kujerar gaban madubin yayi wurgi da ita. Wani irin bakinciki yake ji wanda yake tunanin idan ya taba Izzatu kila sai dai ta kwana a asibiti. Ba talauci ba ko me zai sameni tare zamu zauna. Kin jawo min tashin hankali kala kala kinga ina rabuwa dake shine yanzu zan fada miki halin da zamu iya fadawa kiyi zancen damuwarki ta banza. Gefe ta koma don gaba daya ta tsorata da Hamza. Mutum ne wanda da wuya kaga bacin ransa. A hankali ta soma matsowa kusa dashi zata bashi hakuri sai wayarsa tayi kara.

Ita ma wayar ji yayi kamar ya kwadata da kasa sai yaga Alhaji ne yake kiransa. Yana dauka Alh Nasiru yace ana saukowa daga masallaci kazo ina nemanka. Sai kawai ya kashe wayar. Hamza ya rike wayar yana kallonta...Allah Yasa ba gulmar abinda ya faru dazu Mariya ta kai gida ba.
[9/25, 3:41 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿22

Batul Mamman(Mrs)💖

Daga masallaci gidansu ya wuce ya baro Izzatu tana ta aikin kuka a gida. Lokaci daya duk ya birkice mata abinda bata saba gani ba. Allah Ya sa su Khalifa ta hadasu da Tala suna dakinta suna cin abinci duk wannan tashin hankalin da ake yi.

Baiyi mamakin ganin motar Ibrahim ba don yasan kullum sai yazo gidan. Yana ta sallama yaji shiru ba'a amsa ba. Kande mai aikinsu ce ta fada masa suna dakin Alhaji.

Sallama yayi ya shiga ya tarar dasu suna ta hira. A ransa yace babu wanda yasan matsalar da yake ciki. A lokacin da yake jindadi bai kyautatawa iyayensa yadda ya kamata ba saboda haka yanzu bashi da dalilin tada musu hankali ya fada musu halin da kamfaninsa zai iya shiga. Mama na ganinsa ta washe baki ta soma guda. Murmushin yake yayi yace Mama alkhairi muka samu ne? Kwarai kuwa Yaya in sha Allahu alkhairi zamu samu. Ya karasa ciki ya gaishe da iyayensa. Ibrahim ya miko masa hannu suka gaisa suna tambayar juna aiki da iyali. Bayan sun dan nutsu Alh Nasiru yace bayan magriba in Allah Ya yarda zamu je gidan surukan naka. Hamza ya kalli Ibrahim da alamar tambaya. Alh Nasiru yace da kai nake Yaya. Ni kuma Alhaji, wani abin ne ya faru? Mama ta katse shi cike take da murna tace babu komai. Rabon da ta sake masa sosai tun kafin ta karye a gidansa. Alhaji ya ce bani hankalinka nan Yaya. Duk aka yi shiru ana sauraronsa. Dazu Mariya da Ummahani sun zo gidan nan da yarinya tana ta kuka akan cin zarafin da kuka yi mata kai da matarka. Hamza yace wallahi Alhaji ban san da abin ba sai da naje gida. Yau har marin Izzatu nayi akan abinda tayi. Hajiya ta tabe baki sai kace kayi wani abin arziki. Ai ba laifinta bane ita kadai. Alhaji ya cigaba da magana...kasan akwai alkawarinmu na ka amince da duk hukuncin da zan dauka a kanka idan irin haka ta sake faruwa ko? Tuni Hamza ya gano inda Alhaji ya nufa..muryarsa har tana sarkewa yace don girman Allah Alhaji kada kace nema min auren yarinyar nan zaka yi. Kayi min wani hukuncin ba wannan ba. A rana daya abubuwa sai samunsa suke yi. Ba don kada ya nuna karayarsa ba babu abinda zai hana shi fashewa da kuka. Alhaji yayi yar dariya. Dadina da kai akwai hazaka gashi har ka gano inda na nufa. Kamar yadda kuka sawa yarinya rai cewa bayan magariba zaka je gaishe da mahaifinta to tare zamu ayi mai gaba daya. La'ila ha ilallah...Alhaji kayi hakuri. Idan kaga Hamza a lokacin shima sai ya baka tausayi. Yana cikin wannan matsalar ina shi ina aure. Auren ma da wannan kucakar yarinyar mara kunya. Muryar Alhaji ce ta katse masa tunani. Wallahi idan har kaki yarda da auren nan daya hukuncin da zan iya yanke maka shine na zare hannuna daga dukkan abinda ya shafeka. Babana ba fa kai kadai na haifa ba, kuma kaine na fari amma matsalar gidanka ta isheni. Sam ka kasa rike matarka. Hamza yayi shiru yana jinjina kalaman mahaifinsa. Can dabara ta fado masa yace Alhaji nayiwa Izzatu alkawarin bazan taba yi mata kishiya ba. Alhaji ya tashi yana cirw babbar rigarsa yace ashe auren zobe kuka yi bamu sani ba. To kada ka damu yanzu ma alkawarin naka bai tashi ba tunda ba kai ka nemi auren ba. Ita da kanta ta nema maka. Mu nan karashen aikin ta barmu dashi kawai. Ka tashi ka tafi gida ka saka manyan kaya don bazamu gidan surukai da kai a haka ba ka wani ci zanzaro.
Chapter 14 · 0% Book details