Sashe 67
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read
na yin adalci tsakaninku. Tunda Hajiya ta fara magana Izzatu da Zuhra ke kuka. Izzatu tace Hajiya mungode kuma don Allah ku yafe min. Kema Zuhra ki yafe min duk abinda nayi miki. Tun daga april fool har bayan auren. Zuhra ta share hawaye na yafe miki nima ki yafe min. Banyi wani kokari na daidaita ku ba saboda ina jin haushin abinda kika yi min. Hajiya dai tana kallonsu tana jindadi. Addu'a ta sake yi musu sannan ta tafi duk yadda suka so taci abinci ta ki. ***** Hamza na tuki yana murmushi shi kadai. Yadda gidansa ya koma yasa shi jindadi. Tun kafin rasuwar Junior dama babu wadda ke kwana a dakinsa. Yau zai bukaci su daidaita yadda zasuyi. A son ransa dai Izzatu yake son ta fara karbar girki saboda wasu dalilai nasa. Tun ana zaman makokin ya fada mata ya mayar da ita. Siyayya ya tsaya yayi musu ta kayan kwadayi sannan ya wuce gida. Da sallama ya shigo falon Nana da Khalifa suna masa sannu da zuwa. Zuciyarsa ce tayi masa zafi da ya tuna da Junior. Allah sarki rayuwa. Zuhra da Izzatu suna hira suma suka yi masa barka da zuwa. Bakinsa ya kasa rufuwa don jindadi. Sai da yaci abinci ya basu tsarabar da ya kawo musu. Wurin goma da rabi na dare ya bukaci ganinsu a dakinsa. Kowacce tayi wanka tayi fes da ita. Kusan tare suka shigo yana zaune a tsakiyar doguwar kujera yayi murmushi to sai ku sakani kawai a tsakiya irib yadda matan Alhaji suke yi masa. Zuhra ta rike baki ...sai na fadawa su Hajiya. Yace ke kuma daga magana sai ki fassara mutum. Izzy ai ba haka nake nufi ba ko? Ya fada yana kallonta. Dariya tayi sannan tace zaka ga fassara mutum idan kaji mun maimaita abinda ka fada. Zama suka yi suka saka shi a tsakiya yace mata kun iya sharri. Dama wani albishir nazo muku dashi amma tunda abin naku yazo da haka na fasa. Magiya suka shiga yi masa har ya fada musu cewa ya sami kwangilar zane daga gwamnatin tarayya kuma an biya shi kudin aikinsu. Sannan Mr Oscar ma ya dawo masa da wani bangare na kudinsa. Sunji dadi sosai suka yi masa addua. Daga nan suka dan taba hira sannan Zuhra ta tashi ta tafi daki bayan sun amince Izzatu ce zata fara karbar girki. Tun daga wannan rana zaman lafiya ya kara samun wurin zama a gidan Hamza. Cikin kudin da ya samu ya nemi shawararsu akan ya sayi mota daya ya daukar musu dreba ko ya sayawa kowa daban tunda Izzatu ta amince ya sayar da tata. Guda daya suka nemi ya saya musu nan gaba idan ya sami hali kowa sai ya saya mata. **** Wata rana da daddare Zuhra na kwance Hamza na yi mata tausa saboda kafafunta duk sun kumbura. Tun bayan rasuwar ta zama yau da lafiya gobe babu. Hamza yana kallonta tana lumshe ido yace Cutie kin tuna sarkar da kika bani na sayar lokacin da Izzy bata da lafiya? A hankali ta gyada masa kai don har bacci ya fara daukarta. Wata karamar leda ya ciro daga aljihunsa ya saka mata a tafin hannu. Sai a lokacin ta bude ido tace menene wannan Ya Hamza? Murmushi kawai yayi ta tashi zaune ta bude. Sarka ce da dankunne da zobe na gwal mai matukar kyau. Dadi ya kamata ta rungume shi tana masa godiya. Wani kallo tayi masa tace ina fata ba biyana kayi ba? Ko kadan Cutie. Abinda kika yi min sakayyarki na ga Allah. Wannan kyauta ce kawai. Na bawa 'yar uwarki ita ma. Zuhra tace to Allah Ya saka da alkhairi Ya kara budi. **** Yau ta kama asabar sun tashi da sanitation din gida. Izzatu da Tala ke aikin harda Khalifa. Zuhra kuwa an hadata da zama da Nana, Izzatu tace kada ta tashi sun yafe mata aikin. Tana zaune taji mararta ta fara ciwo kadan kadan. Da yake tasan watan cikin bakwai sai bata damu ba. Yinin ranar haka tayi ta fama da dan ciwo amma bata fada ba. Sai dare har ta fara baccin ciwo ya tasheta. Tun tana daurewa har ta soma kuka. Da kyar ta iya zuwa dakin Hamza ta kwankwasa kofa. Cikin bacci Hamza yaji kamar ana kiransa. Juyawa yayi yaga Izzatu tana bacci. Sake kiran akayi da karfi wannan karon ya tabbatar Zuhra ce. Shi da Izzatu suka taso yana bude kofar ya sameta a tsaye ta kasa daga kafa. Daga shi har Izzatun sun rude ya daga Zuhra ya sauka kasa da ita Izzatu na bin bayansu. Koda suka isa asibitin likita ya tabbatar musu haihuwa ce Allah Yasa suna da dakin da aka ajiye yara bakwaini da dole sai dai su tafi Aminu Kano ko asibitin Murtala. Ga fargaba ga ciwo Zuhra ta rinka kuka. Dama Hamza yana ta tsoron ranar haihuwarta saboda ta iya kuka da raki. Shi da Izzatu suna waje kowa hankali a tashe. Zuhra na kuka a ciki Izzatu tana yi masa nata a waje. Ya rasa inda zaisa kansa. Sai da ya tafi sallar asuba sannan Zuhra ta haihu. Nurse ta fito ta kira Izzatu bayan sun gyarawa Zuhra jiki. Wani sabon kukan ta saka da taga Izzatu. Nurse din ta soma tsokanarta wai sun gama ganin rakinta. Izzatu ta rike mata hannu sannu Maama. Kukan kuma na meye ai an gama wannan saura na gaba kuma. Fuska a kwabe Zuhra tace wane irin na gaba. Don Allah dena fada. Duk kankantar yaron nan sai da yaja min dinki. Kunji salati na da anayi ko? Nurse tace salati ko kuka. Da kyar fa muka yi duk taki tsayawa. Ina ganin idan likita ta dawo daga inda suke duba baby din sabo zata bukaci yi miki. Shigowar Hamza yasa duk hankalinsu yayi bakin kofar. Bakinsa kamar gonar auduga duk da basu ga baby din ba. Izzatu ta dan wayance tabi bayan nurse don ta basu wuri. Tana fita kuwa Hamza ya karasa wurin gadon ya rungume Zuhra....'yar shagwaba yau ta shiga labour room. Ta turo baki...tsokanata ma kake yi ko? Baza'a sake ba daga wannan. Rufa min asiri Cutie ai an bude kofar kenan. Daga wannan sai munyi tara. Uhmm kai da wa? Ni dai na gama. Kaje ka duba mana baby din ko ganinsa banyi ba. Allah Yasa dai yayi kama dani don nasha wahala. Hamza yayi dariya kada ma kisa rai. Mu jininmu akwai karfi duk jikokin Alhaji dashi suke kama yadda muke kama dashi. Bari naje idan zasu barni na ganshi zanyi masa huduba da sunan babanmu Muhammad Bashir. Dadi ya mamaye zuciyar Zuhra tace Ya Hamza nagode ko baiyi kama dani ba babu komai. I love you. Kiss yayi mata a goshi yace I love you more. **** Tun daga ranar asibitin kullum a cike da 'yan uwa da abokan arziki. Gwaggo Hasiya yayar Umma ita ke kwana da Zuhra. Gabadaya Izzatu bata hutawa daga gida zuwa asibiti. Yadda take kulawa da Zuhra yana bawa kowa sha'awa. Raliya ma tazo barka da kanwar Izzatu. Duk da ba'a sallame su ba amma Hamza ya gama tanadin radin suna. Raguna biyu ya siyo manya aka daure a cikin gidan. Ana gobe suna da daddare Zuhra na cin tuwo kowa ya tafi suna hira da Gwaggo Hasiya tace kina nan da cin abincin nan naki ko Fati. Gashi kin haihu yanzu rumbun Hamza zai girgiza. Zuhra tace ni da labari yazo min cewa a wurinki na gada. Kaniyarki, Gwaggo Hasiya ta fada tana dariya ita ma. Dama shawara nake son baki ina fata kuma zaki dauka. Nasan kin riga kin fada mana sunan yaron nan har kina ce masa Babana to amma ni ina ganin me zai hana ki kara karfin zumunci tsakaninki da abokiyar zamanki? Wallahi na kula da gaske take kaunarki. Jiya da za'a gyara miki dinki ita da Atine har da hawaye saboda kin cikawa mutane kunne da ihu. Zuhra ta sunkuyar da kai kasa. Gara ta koyi dauriya dai kowa yace ta fiye raki. Gwaggo Hasiya ta cigaba shagwaba ce su Atine sun koya miki. Batun sunan yaron don Allah ki daure asa sunan marigayi yaron wajenku. Nasan Izzatu zata ji dadi kuma zumuncinku zai kara karfi. Idan da rabo sai ki haifi mai sunan Babanyara. Shawara ce fa kawai na baki bance dole ba. Kada ki dauke shi a matsayin sunan baban kishiya. Ki dauka yaro yaci sunan wansa ne. Zuhra tace Gwaggo nagode sosai. Naso saka masa sunan Baba amma shawararki tasa nafi son yaci sunan dan uwansa. Tana gama cin tuwon ta turawa Hamza text sai taji tsoron kila yayi bacci kada yazo bai gani ba sai da safe. Kira tayi kuma tayi sa'a ya dauka. Da yaji bukatarka ba karamin murna yayi ba yayi ta sa mata albarka. Bai fadawa Izzatu ba ya bari sai da safe taji. Yasan zatayi murna. Bayan asuba kuwa Izzatu ta sauko hada kayan abincin asibiti Tala ta shigo kitchen gaisheta harda dan hawaye tace Hajiya munji sunan jariri Allah Ya raya mana Muhammad Sunusi. Shikenan sai mu rinka kiransa Junior. Izzatu taji zancen wani iri tace Amin amma sunansa Bashir. Tala tace a'a yanzu babansu Khalifa ya fada min sunan kafin ki sauko. Da sauri sauri Izzatu ta hau sama. Hamza na jin motsinta ya tsaya yana dariya. Karasawa tayi ta rungumeshi tana kuka. Baby da gaske ne abinda Tala tace? Sai da ya share mata hawaye sannan yace jiya kina wanka Zuhra ta kirani tace ga sunan da take so. Izzatu ta sake kankame shi tana kuka tana dariya. Kafin taje asibitin sai da ta kira Raliya ta fada mata. Ita ma taji dadi sosai. Tana shiga dakin kuwa rungume Zuhra tayi tana ta yi mata godiya. Daga murna suka koma kukan rashin wancan Junior din. Gidansu Hamza ma duk sun yabawa Zuhra da wannan karamci da tayiwa Izzatu. Da aka sallamesu bayan sati biyu gidansu ta tafi wanka duk da ba haka Hamza da Izzatu suka so ba. Har kara'in suna sai da suka yi wanda mutane da dama suka halarta. Haka rayuwar gidan Hamza ta cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya da kokarin koyi da addini da al'adunmu wadanda basu sabawa addini ba. Zuhra da Izzatu kuwa kullum suna
kokarin kyautatawa mijinsu da junansu. Yanzu haka ma islamiya ya sama musu a nan unguwar tasu suke zuwa tare. Junior kuwa idan ka ganshi a wurin Zuhra to yunwa ce ta kawo shi. Komai Izzatu ke yi masa. Watansa takwas Zuhra ta fara wani laulayin. Hamza ba karamin dadi yaji ba. Saboda yadda take wahala aka yaye Junior. Cikin ikon Allah bayan wata tara ta haifi 'yan matanta guda biyu. Murna wurinsu ba'a magana su Nana an zama yaya. Yaran suka ci sunn Umma wato Fatima da Mama wato Ummukulthum ake kiransu Ummi da Ummu. Suma shekararsu biyu aka haifi Muhammad Bashir. Gidan Hamza ya soma cika da yara. Sai da muyi musu fatan zaman lafiya mai dorewa. ALHAMDULILLAH! Godiya ta musamman taku ce 'yan gidan Batul Mamman Novels. Ni da ku 'yan uwan taka yanzu ma muka fara. Allah Ya kara zumunci Ya albarkaci rayuwarmu. Marubuta Hakika naji dadin kwarin gwiwa da kuka rinka bani a wannan littafi Al'adun Wasu. Nagode sosai.. Ummu Abdoul Aisha Yau Kurah Ummu Nass Feenat Ja'far Maryama Mmn Afreen Baby Maryam Queen Mimi Ummi Aisha Mamu Ummu Hannan Groups Bazan manta daku ba yan... Feenat Ja'afar Novels Taskira Rufaida Omar Fan's duka biyun Allah Ya saka muku da alkhairi Ya kara mana zumunci. Sai kuma 'yan uwana na Fikrah Writers Association ina kara mika godiya tare da fatan alkhairi. Masu waya da text kuma bazan manta daku ba. Nagode sosai.
kokarin kyautatawa mijinsu da junansu. Yanzu haka ma islamiya ya sama musu a nan unguwar tasu suke zuwa tare. Junior kuwa idan ka ganshi a wurin Zuhra to yunwa ce ta kawo shi. Komai Izzatu ke yi masa. Watansa takwas Zuhra ta fara wani laulayin. Hamza ba karamin dadi yaji ba. Saboda yadda take wahala aka yaye Junior. Cikin ikon Allah bayan wata tara ta haifi 'yan matanta guda biyu. Murna wurinsu ba'a magana su Nana an zama yaya. Yaran suka ci sunn Umma wato Fatima da Mama wato Ummukulthum ake kiransu Ummi da Ummu. Suma shekararsu biyu aka haifi Muhammad Bashir. Gidan Hamza ya soma cika da yara. Sai da muyi musu fatan zaman lafiya mai dorewa. ALHAMDULILLAH! Godiya ta musamman taku ce 'yan gidan Batul Mamman Novels. Ni da ku 'yan uwan taka yanzu ma muka fara. Allah Ya kara zumunci Ya albarkaci rayuwarmu. Marubuta Hakika naji dadin kwarin gwiwa da kuka rinka bani a wannan littafi Al'adun Wasu. Nagode sosai.. Ummu Abdoul Aisha Yau Kurah Ummu Nass Feenat Ja'far Maryama Mmn Afreen Baby Maryam Queen Mimi Ummi Aisha Mamu Ummu Hannan Groups Bazan manta daku ba yan... Feenat Ja'afar Novels Taskira Rufaida Omar Fan's duka biyun Allah Ya saka muku da alkhairi Ya kara mana zumunci. Sai kuma 'yan uwana na Fikrah Writers Association ina kara mika godiya tare da fatan alkhairi. Masu waya da text kuma bazan manta daku ba. Nagode sosai.