← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 67

Sashe 43

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikinta har kullewa yaso yi don kaduwar da tayi. Yana lura da yadda ta kidime ya matso daf da ita. Zuhra idanu kamar su fado kasa don tsoro tace dama riga zan saka na fito. Yace Cutie ba na hanaki daurin kirji ba. Da sauri tace yanzu zan kwance nasa kayan bacci. Don Allah ka tafi zan zo. Bai kulata ba sai ma hugging dinta da yayi yana murmushi. Kamshi kike yi maidadi Cutie. Ita dai kasa magana tayi jin yadda yake shafa kanta. A hankali ya saketa ya bude inda kayan baccinta suke. Wata riga ya dauko ruwan madara wadda da alama sabuwa ce ya warwareta. Bazata wuce mata gwiwa ba amma tamkar net haka take tasha ado sosai. Tana kallo ya karasa gaban mirror ya fesheta da turaruka sannan ya ajiye a kan gado. Wani irin kallo yake bin Zuhra dashi yace saka hijab muyi sallah.

Idan baka kalli bakinta ba bazaka ji yadda tace nayi sallah ba can a kasan makoshi. Yace wannan nafila ce da zamuyi kafin mu kwanta. Abin sallah ya shimfida a gaban nata ya jasu sallah raka'a biyu. Bayan sun idar ya dade yana musu addua sannan yayi mata alama da hannu. Dan matsawa tayi kusa dashi ya dora hannunsa a kanta ya karanto addu'a kamar yadda yazo a sunnah.

Rigar da ya ajiye ya dauko sannan ya kama hannunta ya kashe fitila suka tafi dakinsa. Kamar wani sabon mutum haka take ganinsa. Sonsa ne yake karuwa a zuciyarta amma ta kasa sakin jiki. Sai da ya kaita har bakin gado sannan ya kama hijab din ya cire mata. Duk abinda yake yi idanunsa a kanta yana yi mata murmushi. Rigar hannunsa ya saka mata sannan a hankali ya zare zanin ta kasa. Bin jikinta yiya da kallo ita kuwa kamar walkiya don sauri ta haye gado ta kudundune jikinta. Dariya yake yi yana kallonta ke da kika ce zaki min duk abinda nake so, ai ban fara ba ma. Zuhra ta turo baki cikin shagwaba Ya Hamza haka ake soyayyar,ka sa sai kunyarka nake ji. Sai da ya kashe fitila ya zauna kusa da ita yace wannan sunansa sharar fage yanzu za'a fara karatun sosai. Tana ji ya kwantar da ita rub da ciki, tashi take sonyi domin bata san abinda zaiyi mata ba. Ga mamakinta hannuwansa yasa a bayanta ya fara yi mata tausa tun daga kafada har karshen bayanta. Nasan kin gaji sosai just relax ki huta. Yau karatun bazaiyi nisa ba naga duk kin tsorata. A hankali ta saki jikinta tana dan murmushi. Bata taba kawowa a ranta rana irin wannan zata taba zuwa tsakaninsu ba. Ya kusa minti goma yana yi mata tausa yaji tayi shiru. Cutie, ya kira sunanta a hankali. Itama a hankalin tace Ya Hamza. Gyara mata kwanciya yayi ya dora kansa a kirjinta tare da kankameta a jikinsa. Tace Ya Hamza kunyarka nake ji sosai. Hannuwansu ya hada wuri daya yace zan rage miki ita a hankali ne Cutie. Yanzu bacci nake so kiyi saboda kin yini kina aiki. Kansa ta shafa a hankali tace a haka zanyi baccin da kanka a kirjina kamar wani baby? Dagowa yayi duk da duhun dakin ya saita fuskarsa da tata. Cutie na fada miki miji tamkar baby ake son matarsa ta rinka bashi kulawa. Gyada kanta tayi tace to sai da safe. Yace babu goodnight kiss? Rufe ido tayi ita kam yau Ya Hamza ya hanata sakewa. Idonta a rufe taji lips dinsa akan nata. A hankali yasa ta saki jikinta har suka dade a haka. Daga baya ya kwantar da ita a jikinsa a kunnenta yace love you Cutie, yanzu da nasan wace ce ke bana fata Allah Ya kawo abinda zai raba mu . Kanta na kirjinsa tace love you too Ya Hamza tana mai jindadin abinda ya fada .

A haka bacci maidadi ya daukesu. Hamza yana tunanin ranar da zai mayar da ita cikakkiyar amarya. A hankali yake so ta gama sakin jiki dashi sannan su gina soyayyarsu cikin aminci.

Ita ta fara tashi da asuba Hamza na rike da ita kamar zai mayar da ita ciki. Murmushi tayi cike da farincikin Allah Ya amsa adduarta Ya daidaita tsakaninta da mijinta. Kwantawa ta sakeyi kusa dashi ta kama gashinta ta soma zirawa a cikin kunnensa. Sau biyu yana kawo hannu idonsa a rufe sai tayi saurin matsawa. A na ukun janyota yayi ta fado jikinsa. Ya dan bude idanu, Cutie tsokana ko? Dariya tayi ka tashi asuba tayi. Ya sake rufe ido ba fa haka ake tashin miji daga bacci ba. Ina koya miki karatu kin kasa....bakinta ta hada da nasa tayi kissing yaji wani abu na masa yawo a jiki. Kafin ya ankara ta tashi ta fice daga dakin da gudu. Shi kam ya dace da mata ya fada a ransa sannan ya tafi yayi alwala.

Yana dawowa daga masallaci suka hadu da ita tana saukowa zata kitchen. Kada ma ki karasa saukowa ya fada yana hawa benen. Ta dan bata fuska Ya Hamza ina da aiki da yawa fa. Ya kwaikwayi muryarta Cutie baki da aikin da ya wuce nawa, ni kuma bacci nake so mu koma. Daukarta yayi tana dariya ya koma da ita. Tala dake makale a bakin bene basu ganta ba tace Allah Yasa Hajiya Izzatu sai badi zata dawo gidan nan.

*****
Karfe takwas na safe jirgin su Izzatu ya sauka a filin jirgi na Mal Aminu Kano. Ta kira wayar Hamza yafi sau ashirin bai sani ba. Wayar tana falonsa tun dare yasa ta a chaji. Ranta a bace domin tayi zaton zai zo tararta a airport din. Gajiya tayi ta nemi taxi ta daukota har gida.

Koda maigadi ya bude mata kofa sai da jinin nasa ya dan haura. Shikenan zasu dena jindadi yadda suka saba. Tala ma tsoro ne ya bayyana a fuskarta da suka hada ido da ita. Ta wayance tana tambayarta lafiya ta dawo da sassafe? Izzatu tace Babyna bai fada miki kiyi min girki ba zan dawo yau da safe? Anyway ki kai min jakata daki tana bakin kofa. Tana magana tana hawa sama. Tala tace yau mun shiga uku.....

Dakinta ta fara zuwa tayi wanka aka sha turare da kwalliya sannan tasa wata doguwar riga iya gwiwa. Surprising din Hamza zata yi. Tasan kila makara yayi shiyasa baije daukanta a airport ba.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 64

Batul Mamman(Mrs)

Tunda Hamza ya kai Zuhra daki akan gado ya ajiyeta ya soma bubbuga hannu, wai yarinyar nan haka kike da nauyi dama. Zuhra ta turo baki ni bani da nauyi. Yadda bakinta yayi ya bashi sha'awa ya zauna kusa da ita yasa dan yatsansa yana shafa bakin. Ina son dan bakin nan naki na rashin kunya Cutie mai nauyin buhun shinkafa biyu. Zuhra ta hade fuska kamar zata yi kuka ta sauke kafafunta daga kan gadon. Ni dakina zan tafi, dama dauko ni kayi don ka tsokaneni. Kuma yau da daurin kirji zan wuni a gidan nan. Yayi murmushi Allah Ya baki sa'a da yin daurin kirjin nan. Idan suka koma suka kwanta kamar na wata tsohuwa aure zan kara yi. Zuhra tace suwaye zasu kwanta? Abinda kike daurewa da zani mana ko na nuna miki su? Sunkunyar da kanta tayi tana murmushi don ta gane abinda yake nufi. Shima murmushi yayi ya tashi ya cire rigarsa saboda tun asuba yasa ake kashe inji yanzu. Garin sai yayi zafi kamar za'ayi ruwa dama wasu garuruwan na kusa da Kano sun fara samun ruwa. Tana ji tana gani ya kwance mata zanin da ta daura akan 'yar rigar jikinta tare da cire mata mayafi. Yace to mu kwanta da gaske bacci nake ji. Jiyan nan....sai yayi shiru yana gyara kwanciya a kusa da ita.

Ya Hamza me ya faru jiyan?

Babu komai Cutie kawai dai ki shirya yau ba irin jiya bane.

Danyi min bayani meye bambancin jiya da kuma yau da kace na shirya.

Bai bata amsa ba sai kallo da yake binta dashi. Zuhra tayi masa kyau sosai ga rigar jikinta.....

Kula tayi da abinda yake kallo taji kunya. Rufe jikinta tayi tana cewa Ya Hamza zan dena zuwa dakinka indai haka zaka rinka kallo na. Yace to na dena amma dan cire bargon kinga ai babu laifi idan na kalli matata. Dariya tayi ta sake kankame jikinta. Tashi yayi ya koma can inda kafafunta suke ya daga bargon ya turo kansa. Dariya Zuhra takeyi tana cewa yayi hakuri.

Bakiga komai ba yarinya ya fada lokacin da ya fito da kansa a daidai kirjinta da yake dukan uku uku. Runtse idonta tayi saboda yadda take jin kunyarsa. Gabadaya ya danneta sannan ya zubawa fuskarta idanu. A hankali ya fara kissing ko'ina a fuskar har ya kai bakinta. Jira kawai take yayi mata abinda ta fara sabawa dashi sai taji ya tsaya tana jin saukar numfashinsa a fuskarta. Cutie kice kin yafe min duk abinda nayi miki a baya. Ido a rufe tace Ya Hamza na yafe nima ka yafe min. Ya sake matso da fuskarsa, kin yafe har da na kusa cutar kaina nace zanyiwa Inuwa tayinki? Hakan ya bata dariya ta bude ido a hankali. Har shi na yafe Ya Hamza.

Ya lumshe ido to tabbatar min da hakan.

Bata san a inda ta sami kwarin gwiwar daga hannuwanta ta sauko da fuskarsa sosai ta hada bakinta da nasa. Shiru bata kara komai akan hakan ba yace naga alama karatun nan bai gama shiga kanki ba. Kinga yadda ake yi.....daga nan ya fara nuna mata sabon salon da bata san akwai shi ba.
Chapter 43 · 0% Book details