Sashe 56
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A gida aka bar yaran wurin Tala saboda dare ne. Kowa yana fadar me Daddy zai siyo masa na tsaraba. Suna zuwa gaban mota Izzatu tayi saurin shiga gaba. Dama Zuhra bata yi tunanin shiga ba saboda tasan ba ita ke da girki ba. Kafin su je gidansu Hamza taga kayan takaici kala kala. Hannun Izzatu a cinyar Hamza yana tuki. Ko ta sakala hannun a wuyansa ta wani kwanta a jikinsa. Yayi mata magana har ya gaji. Baya son abinda zai batawa Zuhra rai. Da suka je gidan Izzatu ta zauna kwam sai Hamza ya bude mata kofa. Hakan ya bashi damar tsayawa bawa Zuhra da ta fito hakuri. Don bata son ya tafi da baccin rai shiyasa ta nuna masa babu komai. Izzatu ta gaji da jiransa ta bude ta fito suka shiga ciki.
Duk kannen Hamza sun zo yi masa sallama. Mota uku suka yi zuwa airport wasu a tasa wasu a ta Ibrahim da Nura.
Sai da zai shiga ciki Izzatu ta soma kuka duk ana jinta ta rungume shi tana cewa zatayi missing dinsa. Tamkar ya tona kasa ya rufe kansa saboda kunyar kannensa dake wurin. Ibrahim barin wurin yayi saboda bacin rai. Sai da Hamzan yayi mata tsawa sannan ta kyale shi tana kallon yanayin Zuhra wadda ranta ya gama baci. Abinda yake gudu dai sai da ya faru sun rabo da Cutie dinsa ranta babu dadi. Key din motarsa ya bawa Izzatu yace su tafi gida ita da Zuhra don yasan ta kware a tuki.
Bayan ya shige ciki motocin su Nura da Ibrahim ne suka fara yin gaba sannan Zuhra da Izzatu suka tafi wurin motar Hamza. Da Izzatu ta bude ta shiga sai tayi saurin danna central lock ta rufe Zuhra a waje. A take hankalin Zuhra ya soma tashi ga dare ta fara buga glass tana yiwa Izzatu alama da ta bude mata. Glass din ta sauke kadan tace....naga babu abinda baki iya ba shiyasa kullum Hamza yake yabonki to wannan yabon ya kaiki gida. Daga nan ta fige mota tayi gaba ta bar Zuhra a tsaye.
Wayarta ma Hamza ya jona mata chaji tana cikin motar. Zuciyarta ke wani irin bugu saboda tsananin bacin rai. A rayuwarta bazata taba mantawa da Izzatu da ire-iren wulakancin da take mata ba. Kukan ma ta kasa ita daga airport din ma bata san hanyar da zata bi taje gida ba gashi tasan ko ba'a fada ba shabiyun dare ta kusa. Wani irin tsoro ne ya ziyarci zuciyarta ta fara addu'o'i. Jiki a sanyaye ta fara tafiya hanyar da tasan zata kaita bakin gate ta fita. Motoci kadan ne suke wuceta tana tafiya a gefen titi. Ga irin yanayin da muke ciki na raunin tsaro babu wanda ya tsaya yayi yunkurin taimaka mata. Itama ko an tsaya bazata shiga ba saboda tsoro.
Shabiyu saura minti uku Izzatu ta shiga gida. Maigadi ya tareta yana mata sannu da zuwa. Cike da nishadi ta shige ciki saboda ta gama tsara abinda zata fadawa Hamza idan Zuhra ta kai kararta. Rantsewa zata yi motar Ibrahim ta ga ta shiga shiyasa ta taho. Dama shima Ibrahim din ta tsane shi saboda tun farkon aurenta ta kula baya sonta. Kai tsaye dakinta ta wuce ta tafi ta kwanta hankali kwance.
Shiru Tala bata ga shigowar Zuhra ba tana son bata canjin kudin kulu da ta aiketa saboda bayan asuba take son tafiya garinsu zata je tayi sati biyu kamar yadda Hamza ya bada umarnin ta je. Gajiya tayi da jira ta fita waje maigadi har ya kwanta ta buga masa kofa ya fito ta tambayeshi ko yaga shigar Zuhra ciki. Yace shima yayi mamaki amma Izzatu ita kadai ta dawo.
Har Tala ta juya zata koma ciki sai dai hankalinta bai kwanta ba. Da yake da waya ta fito sai ta gwada kiran Zuhra. Karar wayar suka ji daga cikin mota saboda a gefen motar suke a tsaye. Nan da nan Tala da maigadi suka shiga tashin hankali. Tace bari naje na tambayi Maman Khalifa ko ba a gida zata kwana ba.
Maigadi yace ashe baki da tunani ban sani ba? Tare ya kamata su dawo amma basu dawo ba kuma duk munsan ba da ita maigida zaiyi tafiya ba. Ni a tawa shawarar ki kira wani a gidansu Yallabai kiji ko a can zata kwana tunda ya fada min da bakinsa can zai fara zuwa kafin yaje iyafot din.
Da yake a rude take a take tace bata da numbar kowa. Har ta soma kuka tana tunanin ko wani mugun abin ne ya sami Zuhra. Daga baya ta tuna jiya da safe Hamida ta kira wayarta saboda bata sami ta Zuhra ba. Sai da suka rinka bin nambobin da aka kira a wayar wajen shida gashi babu kudi sosai sannan suka yi sa'ar samun ta Hamida.
****
Hamida da Adabiyya suna ta hira basu ji wayar da wuri ba. Tala har ta hakura sun kira wasu nambobin biyu sai ga kiran Hamida ya shigo. Ita duk ta tsorata ganin daga gidan Yaya aka kira da wannan daren. A tunaninta ko babu lafiya Zuhra ta kirata da numbar Tala. Jiki na rawa Tala ta dauka tace kiyi hakuri na kiraki a tsohon daren nan. Dama tambayarki zanyi ko a nan gidanku Maama zata kwana ko gidan iyayenta?
Hamida tace bangane ba Tala. Kina nufin Anti Zuhra bata dawo gida ba? To ina Anti Izzatu?
Tala tace tana dakinta munga ita kadai ta shigo kuma ga wayar Maaman a motar Yallabai an jona ta da wani abu. Sautin kukan Hamida Tala ta jiyo tasan lallai ba lafiya ba.
Ko ajiye wayar bata yi ba ta tafi dakin Mama ta tarar bata nan. Dama tasan Hajiya na falon Alhaji tun da suka dawo daga airport a nan suka gansu suna hira. Falon ta nufa da gudu tana yiwa Adabiyya bayanin abinda Tala tace. Sallama tayi ko amsawa basu jira anyi ba suka daga labulen suka shiga falon. Alhaji ne da matansa suke ta hira yau basu kwanta da wuri ba.
Hajiya ta daka musu tsawa tana son jin dalilinsu na shigowa a haka. Cikin kuka Hamida ta fada musu wayar da suka yi da Tala. Babu wanda hankalinsa bai tashi ba a wannan lokacin. Alh Nasiru ya dauki waya ya kira Ibrahim ya sanar dashi sannan ya tafi dakin Nura ya taso shi. Ko hula babu a kan Alhaji suka fita da Nura. Airport din zasu fara dubawa kafin suje gidan iyayenta.
*****
Hadari ne yake hadowa garin yayi duhu sosai sai fitilun cikin airport na gefen titi. Iska da kura sai kada Zuhra suke tana tafiya idonta sharkaf da hawaye. Banda Izzatu hatta Hamzan haushinsa take ji. Don me bai tabbatar da ta tafi ba ya shige ciki. Kullum Umma na fada mata maza basa son macen da tafi kawo kara amma wannan karon suna yin waya da Hamza idan har ta isa gidanta lafiya kenan zata fada masa. Dole ayi mata iyaka da Izzatu idan ba haka ba kuma lallai zasu daku. Ko a unguwarsu babu mai takalar Zuhra dambe don da gaske karfi gareta.
Ajiyar zuciya tayi da ta ga ta kusa isa bakin gate sai dai tun kafin ta isa ta fara jin ana daka mata tsawa. Nan take ta gigice ganin sojoji sunfi biyar a kanta da bindigogi.
*****
Sanarwar karshe akeyi cewa jirgi zai tashi kowa yasa seat belt kuma a kashe waya. Ran Hamza a bace ya kira Zuhra yafi sau ashirin bata dauka. Izzatu kuma da suka sake sallama tace Zuhran na dakinta. Ya tabbatar idan yace ta kai mata tata wayar kuma bazata kai ba. Dole ya hakura ya kashe wayar. Sauran mutum hudu da zasu tafi tare duk ta Abuja suka tashi da kyar ya sami alfarmar tashi ta Kano saboda iyalinsa. Yayi yunkurin kashe wayar sai ga text ya shigo. Da sauri ya bude ya zata Zuhra ce.
(Sir idan kana da lokaci gobe ka kirani.
Mr. Oscar)
Rasa abin yi yayi ba don yana cikin jirgi ba ai yanzu zai kirashi yaji abinda zai fada masa. Addu'ar abin hawa da ta tafiya Hamza yayi ya kashe wayarsa zuciyarsa tana tunanin me ya sami Cutie dinsa.
****
Kneel down sojojin suka saka Zuhra suna ta turancin da pidgin ta kasa gane abinda suke fada. Kuka take yi kamar ranta zai fita saboda tsabar fargaba. Wani cikin sojojin ya harare katon hijab dinta yace ta cire shi da Hausa. Zuhra ta sake kankame jiki tace bazata cire ba. Saita ta suka yi da bindigogi suna fada...ki cire hijab mu tabbatar babu komai a jikinki idan ba haka ba a wurin nan zamu harbe ki.
Wasu cikin sojojin har sun fara ja da baya saboda kin cirewa da tayi. Wani yace me ya kawoki nan? Bakinta har hardewa yake ta fada musu abinda tazo yi. Dariya suka yi suka karyata ta. Suka bata umarni na karshe ko ta cire hijab dinta ko a harbe ta. Can gefe wasu sojojin ke ta buga waya ga manyansu suna sanar dasu abinda ke faruwa.
A haka Zuhra tana kuka tana rokonsu ta kama hijab din ta cire gashi kanta ko dankwali babu dadinta ma doguwar riga ce ta atampa a jikinta. Rigar duk ta matse ta sama rabin kirjinta a waje. Idon wasu ya kai nan tayi saurin rufewa tana kuka sosai. Ta saddakar mutuwarta tazo amma har abada bazata taba yafewa Izzatu ba. Shi kanshi Hamza idan har wani dalili yasa ta tsira to ta bar gidansa kenan.
Motoci biyu ne suka iso kusan a tare sai ga motar 'yan sanda guda daya. Tun kafin su tsaya Alh Nasiru ya hango Zuhra a durkushe. Idanunsa suka kada suka yi ja saboda bacin rai. Wannan cin kashi da aka yi mata da me yayi kama, me zai fadawa Mal Bashir? Ibrahim ko kashe tasa motar baiyi ba ya fito da sauri amma da ya karaso sauke idonsa yayi saboda bazai iya kallon matar dan uwansa a wannan yanayin ba. Nura kuwa mai raunin zuciyar da tafi ta Hamza kuka yake yi kamar wani yaro.