Sashe 27
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama da Hamza suna daki suna hira. Da suka gama yace zai fita sai bayan sallar isha zai dawo. Dakin Hajiya taje tace mu leka yarinyar nan ko? Hajiya tace tana kitchen da yan uwanta wai ita zata yi tuwon. Farincikin Mama bazai misaltu ba tace Hajiya kinga ikon Allah ko. Kina ganin Zuhra kinsan yarinya ce mai tarbiya. Hajiyan ma murmushi take, sai wani koda surika kike a gabana ko kunya babu. Bari nawa dan Nura yayi aure kisha mamaki. Haka suka sha hirarsu gwanin sha'awa har suka ji shigowar motar Alhaji.
Ana magariba Hamida ta zuba musu tuwon a katon faranti. Suna ci yan matan na zuba mata santi. Ita duk kunyarsu take ji ta kasa sakin jiki taci sosai. Bayan sun gama Mama tace su rakata falon Alhaji ta gaishe shi. Tuna ranar da ta fara zuwa gidan tayi kunya ta kamata ta rufa katon mayafinta ko fuskarta baa gani. Tana durkusawa ta gaisheshi ya fara miko mata rafar kudi dubu goma. Tayi saurin daga kanta yayi mata murmushi wannan tukwicin ciyar da dan tsoho ne. Itama murmushin tayi Hamida tace Alhaji mun tayata fa. Yayi dariya kin tayata hira dai. Daga shi har Hajiya da Mama duk sun mata karba mai kyau suna ta yabon iya girkinta. Wannan kuwa a wurin Ummanta ta koya. Da zasu koma dakinsu Adabiyya ta dauko turaren ta mika masa gashi inji Baba. Allah Sarki mal Bashir harda wata wahala banda 'ya da ya bani. Ina fata babu wata matsala dai tsakaninki da Yaya da Izzatu. Tace babu komai nagode.
Ledar kayan da Umma ta bata ta bawa Adabiyya ta kaiwa su Mama. Tasha addua sosai a wurinsu. Da Hamza ya dawo falon Alhaji yaje. Suna hira ya bude food flask din yaga akwai sauran tuwo a ciki. plate din Alhajin ya jawo ya zuba yaci harda karawa. Alhaji yace Kaltume kiyiwa danki magana ya bar min na dumame. Hamza na dariya yace yau tuwon yayi dadi amma ba jagwalgwalon su Adabiyya bane ko. Mama tace me ka mayar min da 'ya'ya ne. Don kasan matarka ce ta dafa kake mana santi. Cak ya tsaya da shan miyar da yake da cokali yana kallon Mama. Hajiya tace yau kowa yasan sabon hannu yayi mana girki sai yabonta ake yi. To Hamza, ga abinci da dadi ga kyankyamin Zuhra da yake. Amma dole ya yaba mata don ba karya ta iya girki.
Da zasu tafi Mama atampa Super Exclusive ta bata mai kyau, Hajiya kuma ta bata dubu biyar. Sai godiya take musu kamar ta ari baki. Su Adabiyya suka yi mata alkawarin zuwa su kwana biyu da weekend don duk cikin satin zasu gama jarabawa. Adabiyya na level two Hamida na level one a jamia. Hamza sai mamakinsu yake basa son zuwa gidansa a iya saninsa.
Ba karamin dadi taji ba yadda suka karbeta a gidan. Suna isa gida ya rufe ko'ina yace mata sai da safe. Yana son yaba mata yadda ta kyautatawa iyayensa amma wata zuciyar ta hana shi. Abinda su Hajiya suka bata ta nuna masa yace to Allah Ya saka da alkhairi. Kema an fada min abinda kika kai musu nagode. Taji dadin godiyar tasa ta tafi dakinta zuciyarta fes.
Da sassafe ta farka ta gyara wake ta bawa maigadi ya kai mata markade. Haka kawai taji kosai take son yi. Waken ba dayawa ta hada ba tunda nata ne ita kadai amma tayi yadda maigadin zai samu don tana ta tunanin me yaci jiya da rana da kuma dare. Tafi kowa sanin yunwa ba dadi.
Kunu ta dama da tsamiya ta dan saka lemon tsami sannan ta soya musu kosan. A dan karamin jug din roba ta zubawa maigadi nasa kunun sannan ta sami wata robar ta zuba masa kosai da yaji. Nata kuma ta kwashe daga mai ra barshi ya tsane kafin ta kaiwa maigadin. Tana juyowa taga Hamza har sai da taji tsoro. Ya gama shirinsa zai tafi wurin aiki. Gaisheshi tayi tace zan mikawa maigadi abinci. Hanya ya bata ta wuce ya tsaya yana kallon kosan. Yana jin yunwa amma bazai ce tayi abinci dashi ba duk da jiya yaci kuma ya yaba. Kamar ya fita daga kitchen din sai ya dawo bari yaci yaji ko ta iya kosan. Izzatu bata yi tace abincin talakawa ne. Daya ya jefa a baki yaji dadi harda dan kurbar kununta dake cikin kofi. Gaskiya da dadi, a hankali ya dawo ya dan leka falon yaga bata taho ba. Da sauri yazo ya dauki wani harda saka yajin da ke wata yar roba ya kuma sawa a baki duk da akwai zafi sannan ya dauki biyu a hannu. Ko taunawa bai fara ba Zuhra ta dawo tayi mamakin ganinsa a kitchen din tace ashe baka tafi ba. A ransa yace me zaisa ta dawo yanzu. Gimtse baki yayi yace uhmm. Kallon rashin yarda tayi masa ko akwai abinda kake so? Uhmm uhmm ya amsa bakin nan a rufe. Ya rasa yadda zaiyi da kosan bakinsa. Daukar plate tayi ta juye kosan ta dauki kofin kunun tace to adawo lafiya ta fice ta barshi a tsaye. Sai a lokacin ya saki numfashi sannan ya sami damar tauna da hadiye kosan bakinsa. Ficewa yayi ya shiga mota ya cinye sauran biyun sannan ya goge hannu ta tissue. A mudubin motar ya kalli kansa....Hamza kaji jiki, satar kosai a cikin gidanka. Murmushi yayi ya ja motarsa.
[9/25, 3:55 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 42
Batul Mamman(Mrs)
Iyakar karfinta tasa tana neman kwace hannunta amma rikon da yayi mata ba na wasa bane. A haka ya jata suka je dakinsa ya dauko kwalin tissue sannan suka koma nata dakin. Iyakar tsurewa Zuhra ta gama don bata san abinda zaiyi mata ba sai magiya take yayi hakuri. Yana jinta ya share, sai da suka zo gaban dressing mirror dinta ya jawo stool din ya zaunar da ita. Numfashinta har wani sama sama yake don fargaba. Har tausayi ta bashi sai ya dan sassauta murya tare da daidaita fuskarsa da tata har suna jin numfashin juna...ke, rufe idonki. Ji tayi kamar zuciyarta zata ballo kirjinta ta fito, ba dai hada bakin da ya gama da Izzatu zaiyi da ita ba. Ita ko a litattafan hausa idan tana karantawa ta tsani ace anyi kiss. Turawa dai marasa kunya suyi abinsu amma ita duk yar kazantarta kyankyamin haden bakin nan take yi. Kokarin tashi tayi ya rike kafadunta ya sake zaunar da ita. Kawai sai ta saka masa kuka...don Allah kada kaci amanar matarka. Kamar yau ne zata dawo kuyi abinku. Tissue yake zarowa daga kwali yace me zamuyi? Kanta a kasa tace sumba mana. Bai san lokacin da ya soma dariya ba. Kece sumbar ai....ya nuna bakinta Allah Ya kiyaye nayi kissing wannan dan bakin. Ina miki kallon saliha ashe kema idonki ya bude kinsan kiss. Hannuwanta tasa ta rufe fuskarta don kunya yasa hannu ya sauke su. Rufe ido nace. Ba musu ta rufe...tissue ya ninke ya soma goge mata girarta. Yana yi yana kallon yadda ta bata rai harda turo baki. Bai bar abinda yake ba yana yi yana kallonta. Ya gama da girar ya koma saman idanunta da lips dinta. Takaici duk ya isheta kwalliyar rabin awa an goge mata ita. Hannunta ya sake kamawa ya kaita kofar toilet. Jeki kisa sabulu ki wanke fuskarki. A tsiwace tace bayan duk ka goge min kwalliyata. Daga hannu yayi zai dalle mata baki ta tafi da sauri. Ke dawo ki ajiye mayafin kada ya jike. Kamar bata ji me yace ba sai da ya maimaita da dan fada fada. A hankali ta warware shi. Idanunsa a kanta, dole ta rufe jiki da katon mayafi irin wannan matsatsiyar riga. Doguwar riga ce mai kyau duk ta fito da surar Zuhra. Ta wuyan rigar kirjinta ya dan fito. Tana daga hannu ta ajiye ya hango hammatarta......fal gashi.
Saurin kawar da kansa yayi. Yaso shagala da kallon jikinta sai gashin da ya gani ya dawo dashi. Gaskiya lamarin Zuhra akwai gyara. A inda ta barshi ta dawo ta same shi yace ta sake zama a kan stool din. Wani lotion mai kamshi yasa kadan a hannunsa saboda zafin gari ya shafa mata a fuska. Daga shi har ita wani yanayi suka shiga yadda yake shafa mata fuskar. Bayan ya gama ya dauko hoda ya shafa mata. Sai ya duba lip gloss light brown ya sa mata a baki. Har abin taje gira yasa ya kwantar mata da gashin girar sosai. Ita kanta sai taga tafi dazu kyau duk da tana son saka janbaki da eyeshadow. Kallonsa take yadda ya iya sarrafa kayan kwalliyar mata.
Da ya gama mikewa yayi yana dan sosa bayansa da ya kage saboda ya jima a duke. Hararta yayi saura kice min dan daudu, kuma ko kice kinyi kyau bare kuma godiya. Murmushi tayi tace nagode. Shareta yayi ganin ta fara dariyar shakiyanci bari naje na shirya ki canja kayan nan kafin na fito ki saka mai zani.
Wata atampa mai adon pink da fari ta saka wrapper skirt da riga. Duk Hajara ke kai musu dinki kuma sunyi sa'ar tela. Pink din mayafi ta saka da farin takalmi da yar jaka fara mai kyau. Sake kallon kanta tayi a mudubi tayi murmushi. Mutumin min nan yana da kirki idan yaso. Amma banda wayon ya tabani meye zai goge min fuska da kansa. Tana zancen zuci taji wani kamshin turare mai dadi. Hamza ne sanye da yadi ruwan madara mara nauyi. Ya gyara fuskarsa ya rage gemu da gashin baki. Sai ya kara haske da yi mata kyau. Shima kallonta yayi ta canja kayan yace better...Zuhra tace best. Ta dan daga gira...nima fa na iya turancin nan. Good, better, best waye bai iya ba. Dariya ta bashi ita kuwa ko a jikinta tabi bayansa suka fita.