Sashe 17
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tabarma ta dauka ta fita soron. Kamshin turarensa ya cika wurin. Yau suit ce a jikinsa ruwan toka. Zuhra ta gaishe shi ta sami wuri ta zauna don baya zama akan tabarmar. To yau nayi zuwa uku ina fata kina rike da dukkan abinda nake fada miki. Ya dan jima yana magana sannan ya lura ba saurarensa take ba. Shi ta kurawa ido....ke, keee, KE lafiyarki? Bata dawo hayyacinta ba sai da ya dan tafa hannuwansa a gaban fuskarta. Ajiyar zuciya tayi sannan tace yanzu don Allah kana iya numfashi? Ni bansan haka ake saka abinnan a zahiri ba sai yau. Waige ya fara yi don bai gane kan zancen ba. Tace neck tayil dinka nake nufi. Naga ya shake maka wuya kamar mai shirin rataye kansa. Yanayin maganarta yasa shi yin murmushi. Necktie ake cewa sannan bai shake ni ba. Amma dai baka sakewa ko? Dauri irin wannan akwai ganganci a cikinsa. Dole Izzatu tace yarinyar nan tana da shirme. Yace ni zan tafi ina tunanin jibi Alhaji zai zo. Ki kiyaye abinda na fada miki. Har ya juya sai ya dawo...by the way nayiwa Inuwa maganarki sai dai mun makara. An kusa kai kudin aurensa. Zuhra tace babu komai. Nagode.....yadda yaga kamar ta nutsu yasa ya kwantar da hankalinsa. Dubu goma ya dauko yan dari dari sababbi ya mika mata. Ga wannan ki rike. Nagode ta sake cewa sai kawai ta nade tabarmarta ta shige ciki. Mayar da kudinsa yayi aljihu yana mamaki da bata karba ba.
Bayan Isha Baba ya kira Zuhra da Umma. Wani katon littafi ya dauko mai hotunan kayan daki irinsu gado, kujeru da kitchen cabinet masu tsada. Kunsan aikina ba wai ina yin kayan daki na masu kudi bane sosai. To amma na sami wani ya bani aron littafinsa nake son kwaikwayon duk wanda kika zaba zanyi kokari na kwatanta miki irinsa uwata. Atine gashi ki tayata zabe. Hawaye ne mai zafi ya saukowa Zuhra. Tabbas iyaye sun cancanci dukkan girmamawa daga 'ya'yansu. Allah Ka sakawa iyayenmu da alkhairi. Baba ne ya fara gani yace meye haka uwata ta kaina? Da yake Umma ma akwai rauni sai kawai suka hadu suna kuka maimakon ta rarrasheta. Baba ma dai ta maza yayi ya fara musu fadan su dena yi masa kuka. Burina Zuhra tayi aure ta sami mai kula da ita. Sai da shekaru suka zo mana muka haifeki dole nayi murna idan na sami wanda zai tayani kula da Fatima kyauta daga Allah. Zuhra fadawa tayi jikin Baba tana kuka. Ni bazanyi aure ba. Saurin tashe mata baki yayi...kul na sake jin irin haka. Aure ai shine rufin asirin kowa. Zaki yi aure cikin gidan mutumci kuma in Allah Ya yarda zaki kawo min jikoki su zo in basu labarin tabara irin ta babarsu. dariya ta rinka yi. Daga baya suka zabi gado da kujeru ita da Umma.
Sai da ta kwanta ne a kan dan gadonta maganar Hamza ta rinka dawo mata. Tabbas da niyarta ta aureshi ta kuntata masa. Don duk zancen da yake mata jinsa kawai take yi. Sun dauketa wata gaula daga shi har matar tasa. To amma maganar Baba ta tsaya mata a rai. Duk shirmenta tana kaunar iyayenta kuma bata son bata musu suna. In Allah Ya yarda bazata wasta musu kasa a ido ba. Idan har baayi auren ba sai dai idan Hamza da bakinsa yace baya so.
[9/25, 3:46 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 27
Batul Mamman(Mrs)
Bayan kwana biyu Umma ta sanar da Zuhra yau iyayen Hamza zasu zo. Mamansu Hajara ta shigo tayata aiki. Kaji hudu suka soya, Anti Faiza sarkin flour tayi musu cake, meatpie da doughnut. Zuhra ta wanke tsakar gidansu tas dama irin fasassun tiles dinnan ne. Nan da nan wurin ya hau sheki. Bayan ta gama aikin ta hau magiyar a barta taje gidan Hajara. Tunda akayi biki Baba ya kafa mata dokar sai tayi sati baya son yawon gulma. Anti Faiza tace ke da zasu ji ta bakinki ai bai kamata ki fita ba. Kannen Umma biyu suma suna ta zolayarta da matar kanin Baba.
Sai bayan la'asar suka watse aka bar Maman Hajara da Umma. Baba ya shigo tare da Malam yace su bakin zasu shigo. Kaninsa da yake aikin masinja ma yazo tunda Alh Nasiru yace indai ta amince to a lokacin zasu bada kudi asa rana. Su Umma daki suka koma bayan an jerawa baki kayan motsa baki. Sai da suka gama barkwancinsu sannan Alh Nasiru ya bukaci ganin Zuhra domin yaji amsarta. Dan karamin falonsu ya shiga tare da Baba. Kanta a kasa ta gaishe shi ya amsa yana mai yabon halayenta. Sannan ya tambayeta domin baya son matsa mata ta auri wanda bata so. Murmushi kawai tayi ta sake sunkuyar da kai. Ganin haka ya mike suka koma tsakar gida. Ya dubi sauran jamaar wurin. Shirun budurwa alama ce ta amincewarta saboda haka idan duk kun amince ina so asa rana nan da sati hudu. Kowa yayi naam da hakan harda Baba. A take suka bada kudin aure dubu dari aka yi addua taro ya watse.
Ranar murna a wurin Baba da Umma ba'a cewa komai. Kudin da aka bayar Baba yace zai ajiye mata zuwa lokacin biki. Kinga ko mijinki bai yarda ki cigaba da saka ba kina da dan abin hannunki. Sannan ku shirya karshen sati zamu je Ajingi. Nan Zuhra ta hau murna zata je wurin Inna.
Yinin ranar Hamza suna ta meeting da maaikatansa akan yadda zasu samu su karasa biyan kudin da turawan ke binsu kamfanin ya dawo mallakin Hamza shi kadai. Ya sanar dasu dole su zage damtse ayi aiki sosai domin su fitar da kudin kafin watanni shidan da aka basu su cika. Suna fitowa gidansu ya tafi saboda amsa kiran Alhaji. Yasan zancen bazai wuce Zuhra taki amincewa ba ayi masa fadan bai yi abinda ya dace wurin jan raayinta ba.
Mama bata gida lokacin da yaje sun fita da Nura. Da Hajiya suka gaisa kafin ya karasa wurin Alhaji. Fuskarsa a sake ya amsa gaisuwar Hamza sannan yace ya kamata ka fara shiri tunda sati hudu kawai aka sa rana. Idan baka son hadasu gida daya sai ka gyara mata tsohon gidanka. A dan daburce Hamza yace wa zan gyarawa? Alh Nasiru yayi murmushi amaryarka mana. Yadda gabansa ya fadi bai san lokacin da yace amincewa tayi??? Alhaji yace ba haka kaso ba ko. Ai nasani Babana. To sai ka dau hakuri yarinya tana neman albarkar iyaye. Hamza yace Alhaji nima ina nema. Don Allah a janye zancen nan. Ko Nura ka aurawa ita. Dariya Alhaji yayi shi kuwa Hamza kamar yayi kuka yace yarinya ce karama. Ya za'ayi na zauna da ita? Alhaji ya gyara zamansa. Kaga ba jan zance nake so muyi ba. Aure ne sai an daura in sha Allah. Ni ban dora maka nauyin komai ba sai sadaki. Tunda na fika son ayi auren na dauke maka duk wata hidima da zata taso. Rasa bakin magana yayi yana kallon mahaifinsa. Mama ce ta shigo tare da Nura da su Hamida suna rike da wasu jakunkuna masu kyau. Seti ne guda shida, tace Alhaji kaga wadanda muka samu. Sai ta kalli Hamza, a'a kaga babban dana angon Zuhra. Ta tura masa daya daga cikin jakankunan. Kaga wannan sunyi kyau? Yanayin fuskarsa bazai fasaltu ba yace Mama harda ke? Nice ma kan gaba ta bashi amsa. Uhm Alhaji gobe da safe zamu je da su Jidda kasuwar, kasan hada lefe akwai cin lokaci. Yana shan furarsa yace Allah Ya kaimu. Share Hamza suka yi tamkar baya wurin. Tunaninsa daya yadda zai fadawa Izzatu plan dinsu bai karbu ba.
[9/25, 3:47 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 28
Batul Mamman(Mrs)
Abinda yaji tsoro ne ya faru. Izzatu tayi kuka har ta gaji. Rokon Hamza take yi ya rufa mata asiri kada yayi auren. Tun yana rarrashinta har ransa ya baci da tace duk gidansu babu mai kaunarta. A hasale yake kallonta ke har kina da bakin cewa ba'a sonki Izzy? You caused everything. Lokaci guda kin lalata farincikin gidan nan. Ganin ya soma fada yasa ta rungumeshi. Am sorry baby. Na yarda kayi auren amma bayan lokaci kadan sai mu nemi dalilin da zaisa ka saketa. Jinta kawai yayi. Shi da Alhaji ya kafa masa sharadin indai ba da dalilin da ya sabawa shariah ba bai yarda ya saki Zuhra ba.
A bangaren su Zuhra kuwa shirye shirye ya kankama. Makota da abokan arziki kowa yana son gwada bajintarsa wurin bikin tilon yar baban yara. Gudunmawar kudi suka rinka bawa Mal Bashir sai da ya tashi da dubu dari biyu da talatin. Shi kanshi ba karamin mamakin wannan karramawa ta mutanen unguwarsu yayi ba. Anas da Sani ma ba'a barsu a baya ba domin kuwa gas cooker karami suka kawo. Baba yayi murna da godiya sosai. Haka Umma ta rinka shiga gida gida tana godiya itama.
Zuhra taje gidan Hajara a nan suke nasu tsarin bikin duk da ba damunta yayi ba don tasan wahala zata sha kawai. Hajara tace wato Zuhra da gaske kike da kika ce idan kika tashi aure sai munyi mamaki. Gashi zaki auri dan gayu dan boko. Wallahi ki dage sosai tunda yana da mata. Zuhra tayi dariya wace irin dagewa kuma. Ai kawai indai zasu bani abinci naci na koshi to suje can su karata. Sahabi da yake daki ya fito ba shiri. Amma dai Zuhra wasa kike ko? Tace da akayi me fa? Maganar da kika fada yanzu nake nufi. Yaushe zaki ce abinci zaki je ci. Wuri ya samu ya zauna yana karanta mata yadda zata yi a gidan miji. Hajara sai dariya saboda Zuhra rufe kanta tayi da mayafi. Irin wannan bayani na Sahabi yafi karfinta. Shi kuwa ya dauketa kanwarsa ne tunda duk unguwarsu daya.