Sashe 22
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shi da accountant din kamfaninsa ne suke ta lissafin kudi. Duk yadda zaiyi su hada kudin nan kokari yake yi. Sau uku ta kira baya dauka saboda abinda yake yi. A na hudun ne ya dauka Izzy what is it? Honey ni bansan abinda akeyi ba a gidan nan amma ga su Mama da wasu matan da ban taba gani ba a cikin gidan nan. Kamar wata walima suke yi ko me oho. Ana ta ciye ciye dai a falon. Table din gabansa ya buga rai a bace. Ya rasa wani irin abu ke faruwa dashi. Wane irin taro ake yi a gidansa wanda bashi da masaniya a kai. Tunda Izzatu tace harda Mama gara ya kira yaji ko meye. Yayi ta trying din number dinta ba'a dauka. Suna can tasa ana ta shigo da kayan garar cikin falo. Ta tambayi Zuhra tace key din inda akace shine kitchen dinta baya wurinta.
Jin shiru da yayi yasa ya hada kayansa yace da accountant din zaije gida ya dawo. Yana fita Mr Oscar ya fara hada takardun da yazo dasu wurin. Cheques ya gani har hudu na miliyan goma goma da Hamza yasa hannu. A take zuciyarsa ta soma rawa. Kamfanin nan na Hamza nema yake ya durkushe duk su rasa aiki. Gara ya taimaki kansa kawai. Guda daya ya dauka ya fita. Shima rufe nasa office din yayi sai banki.
Hamza na zuwa gida ya tarar saura Anti Faiza dasu Mama. Duk sauran matan sun watse. Izzatu na ganin shigowarsa ta taga ta fito daga dakinta. Sai a lokacin ta gaishe da Mama. Ko kallonta bata yi ba ta cigaba da tambayar Hamza ya aiki. Baya jindadin yadda iyayensa basa shiri da Izzatu. Tace Mariya ya yara? Itama bata kulata ba. Ai nan Hamza ya soma fada akan me zata share matarsa. Jidda tace Yaya munfi awa daya a gidan nan bata fito ta gaishe da Mama ba sai yanzu. Kallon Maman yayi tace kaga ina key din kitchen din Zuhra a bude a zuba kayan nan a ciki. Sai a lokacin idanunsa suka kai kan kayan. Kamar ya tambayi ko na meye sai ya fasa yace yana daki bari na dauko. Mama tace yi zamanka mu danyi hira yanzu zan tafi. Zuhra jeki ki dauko....dibi dibi ta soma yi don bata san inda zata duba ba. Izzatu ta sha kunu , shi kuma ya dan wayance ki duba bedside drawer ta bangaren dama.
A sanyaye ta hau saman. Ita da sau daya ta shiga falonsa ma bata gane inda yake nufi ba. Su Nana ne suka fito daga daki sai murna anga Grams. Shiru Zuhra bata dawo ba yayi dan murmushi Mama bari na bita.
A falon ta tsaya kasa shiga dakin. Bata ankara ba taji ya shigo ya rufe kofar har sai da gabanta ya fadi. Hannunta ya ja cikin dakin ya matse shi iya karfinsa. A tsawace yace what the hell is happening a gidan nan? Jikinta a take ya soma bari ga hannu ya matse mata. Idanunta suka ciko da hawaye, ya sake yi mata tsawa nace me ake yi a gidan nan? Kayan garata aka kawo. Tana fada hawayen ya soma digowa. Ransa ya gama baci, kin fada min za'a kawo gara??? Tayi saurin girgiza kai. Snacks da nagani anci a falon daga ina aka samo su? Shiru tayi saboda yadda hannunta ke zugi. Baki da baki ne? Nan ma bata yi magana ba. Sakinta yayi ya dauko key din sannan ya nuna mata toilet maza kije ki wanke wannan hawayen munafurcin. Da gudu gudu ta tafi. Koda ta fito yana jiranta suka sauka tare.
Mama tana murmushi tace daga dauko key sai ka shanya mu Yaya. Zuhra yake kallo abu ne ya shigar mata ido na tsaya wanke mata. Kowa sai sannu yake mata ana tambayarta ko ya fita. Budar bakinta kawai sai ta soma kuka. Mama ta tashi da sauri tana tambayarta me aka yi mata. Shima Hamzan tambayar da yake mata kenan a dan tsorace. Tana kukan tace idon ke zafi....Mama ta rungumeta Yaya kace yar tawa sarauniyar shagwaba ce. To sannu kinji Fadimatu ki dena kuka. Idan bai fita ba sai kuje asibiti Yaya. Kai kawai ya daga yana kallon Zuhra cike da tsoron kada ta fadi abinda yayi mata.
Sai da aka shigar da komai kitchen din har Mama na fadan garin yaya ba'a fara aikin gyara wurin ba yace sai weekend mai aikin zai zo. Tare da Anti Faiza suka tafi suka ajiyeta a hanya. Zuciyar Mama tana mata wasi wasin dalilin kukan Zuhra. Bata sani ba ko idonta ne amma kamar ta rame ma.
[9/25, 3:52 PM] +234 803 040 6305: AL'ADUN WASU 35
Batul Mamman(Mrs)
Fadan da Hamza yayiwa Izzatu yasa ta kuka sosai bayan fitarsa. Kwana biyu a tsakani yana share lamarinta. Ranar monday ran kowa a bace suka rabu saboda sun kwana da fushi da juna. Ta dage sai ya saki Zuhra idan yana son zaman lafiya. Takaicinsa shine kamar bata san mahaifinsa yayi masa katanga da sakin Zuhran ba. Ita ba ruwanta ko Alhaji zaiyi fushi dashi ita dai bukatarta ta biya. Ko kulata baiyi ba ya fice abinsa. Saboda bacin rai wata jaka ta dauko tana kuka tana watsa kayanta a ciki. Sai da ta gama ta kira mahaifiyarta tana sanar da ita zata taho gida. Idan babu jirgi zata yi shatar mota. Da kyar Raliya ta samu Izzatu ta fada mata abinda ya faru. Tsaki Raliya tayi...ni bansan baki da hankali ba sai yau Izzatu. Yanzu sati daya da zuwan yarinyar har kin karaya? Duk ke kika jawowa kanki ai. Muryarta har ta dashe don kuka tace what do I do Mum? Bazan iya zama da wata mace a gidan nan a matsayin kishiya ba. Raliya tace calm down. Yanzu abinda nake so dake shine ki bude kunnuwanki kiji abinda zan fada miki...........
A site din ginin Hamza ya hadu da Inuwa sakatare yace Inuwa hala baka sami zuwa bankin bane ranar Jumaa banji alert ba. Ikon Allah kuma naje ranka ya dade har ma na hadu da Oscar. Sakon yana cikin motata bari naje na dauko. Hamza ya dakatar dashi. Ka bari sai mun koma office.
Zuhra tayi mamakin abincinta na rana yau. Duk da bashi da yawa sosai amma yafi abinda aka saba zuba mata. Da laasar ma Izzatu har shiga dakinta tayi tace mata zata je unguwa. A darare Zuhra tace Allah Ya kiyaye hanya. Bayan ta tafi Zuhra ta tashi taje inda Izzatu ta tsaya zuwa bakin kofa ta karanta Ayatul Kursiyy ta tofa a ko'ina. Irin wannan makircin na kishiyoyi ai mun saba jin labarinsa ta fada a fili tana dan dube dube ko an barbada mata wani abin. Kin gama yi min masifa yau kice min zaki fita kamar nice dan gatan mijin nan naki. Ga mamakinta da Izzatu ta dawo tare da yaranta suka sake zuwa dakin Zuhra tace ta dawo. Da dan murmushinta na tsoro tace sannu da zuwa. Zuciyarta ta gama bata akwai abinda ke shirin faruwa ko zai faru.
Ranar Hamza bai sami dawowa gida ba sai wajen tara na dare. Gidansu ya biya Mama take tambayarsa yaushe zai kawo amarya. Dammm yaji a zuciyarsa, yanzu jira ake ya dauko wannan kazamar a mota. Cewa yayi weekend in Allah Ya yarda zai kawota. To ka biya da ita taga nata iyayen inji Hajiya.
Lokacin da ya shiga gida falon tsit. Yasan su Khalifa sunyi bacci saboda makaranta. Dinning table ya kalla yaga an jere shi da kwanuka kamar ana jiran baki. Ko bi ta kai baiyi ba ya haye sama ya shige daki. Abinda ya kwana biyu bai gani bane Izzatu ta gyare dakin tas sai kamshi ko ta ina. Murmushi yayi yasan tana neman shiri kenan. Jakarsa da takalma ya ajiye yana cire safa ta fito daga toilet dinsa sanye da wata rigar bacci mai matukar kyau. Binta yayi da ido har ta karaso gabansa. Ba karamin kyau tayi ba tasha kwalliya. Safar ta karasa cire masa sannan ta rage masa kayan jikinsa. Bata ce komai ba shima baiyi magana ba. Toilet ta kaishi ta taimaka masa yayi wanka. Abinda ta dade bata yi ba tun kafin tayiwa Zuhra April fool. Sai da ta gama shirya shi suka je kasa ta bashi abinci da kanta. Da ta tabbatar ya koshi sai suka koma dakinsa durkusawa tayi a gabansa gwiwoyinta a kasa ta soma kuka. My sweetbaby nasan na bata maka rai da yawa a iya zaman da muka yi amma ina rokonka don Allah ka yafe min. Hannuwanta ya kama zai tayar da ita zaune taki tashi. Bazan tashi ba sai ka fada da bakinka ka yafe min. Na janyo maka auren da mu duka bamu shirya masa ba sannan itama yarinyar na dauki alhakinta. Kukanta har ransa yake ji. Tayar da ita tsaye yayi ya rungumeta yana rarrashi. Komai ya wuce Izzy tunda kin gane kuskurenki. Kissing dinta ya soma saboda shi kanshi ba karamin missing dinta yayi na. Wani dadi taji yana ratsata ta biye masa. Sun jima a haka kafin tace Hamza dear ina zuwa. Sai da tayi da gaske ya saketa ta fita.
Dakin Zuhra taje, lokacin Zuhra tana waya da Hajara suna ta hira kamar bata da wata damuwa. Ganin Izzatu a bakin kofa yasa tayi saurin sallama da Hajara. Da fara'arta kamar Izzatun da ta fara sani tace kizo zamuyi magana a dakin Hamza. I hope ban takura miki ba? Zuhra kallonta take da mamaki ga wata irin riga da ta saka. A ranta tace wasu matan dai basu da kamun kai. Yanzu meye na shigo min daki tsirara. Mayafinta ta dauko ta yafa tabi bayanta. Suna zuwa Izzatu bata daukeshi komai ba ta fada jikin Hamza wanda yake sanye da wandon bacci kawai. Dorawa yayi daga inda suka tsaya. Zuhra tayi saurin runtse ido ta juya baya tace wayyo na shiga uku iskan......