Sashe 47
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hanyarsa ta tsallaka titi ya koma motarsa yaga wata tsohuwa tukuf itama ta rasa yadda zatayi ta tsallaka. Da a lokacin da yake Hamzansa ne mijin Izzatu ita kadai baya jin zai iya yadda hannunsa ya taba matar. Amma yanzu ya koyi darasin zaman duniya. Hannun matar ya riko tana tafiya da kyar har ya tsallakar da ita titi. Godiya ta rinka yi masa tare da addua. Harda dan kukanta tace ba don kai ba sai nayi kusan minti shabiyar ina kokarin tsallaka titin nan. Magani na karbowa dana yana fama da lalurar asma. Ta dauki wata leda da magani ta nuna masa. Hamza ya tausaya mata yace baki da wasu yaran ko jikoki da zasu je miki? Tayi murmushi, shi kadai ne dani. Bayan shekaru shabakwai sai yanzu matarsa take da tsohon ciki. Idan abin ya tashi ita take zuwa amma yanzu bazata iya doguwar tafiya ba. Yana ganin kansa a wani yanayi ga wadanda suka fishi. Kudin aljihunsa ya shafa ya sa hannu ya kirga dubu goma ya bawa matar. Hannu na rawa ta karba tana ta kuka...Allah Ya albarkaci rayuwarka data iyalinka, Allah Ya rabaka da masifun zamani, Allah Ya baka arziki na halali daga inda baka taba tsammani ba. Yaro nagode, nagode. Hamza na tsaye har ta shiga adaidaita sahu sannan shima ya tafi zuciyarsa kamar an cire masa wani nauyi. Hakika sadaka maganin masifa ce kuma waraka daga bacin rai.
Asibitin ya koma ya tarar Izzatu ta farfado. Raliya ya kira a waya ya sanar da ita halin da Izzatu ke ciki. Cikin kidima tace gobe zata taho in sha Allah. Tana ajiye wayar ta kira kanwarta Larai ta fada mata asibitin da suke.
Tsananin bacin rai da kishi yasa Izzatu kuka tunda ta farfado. Yanayin da taga Zuhra da Hamzanta shi kadai yake mata yawo a ka tunda ta bude ido. Su Mama kuwa sai tausayinta suke yi a nasu tunanin bakincikin bari da cire mata mahaifa da akayi take yi. Cike da tausayi Hamza yake mata sannu amma ko kallonsa taki yi. Su Mama sai suka dauke kai kamar basu kula da abinda suke yi ba. Adabiyya tace Yaya ina Anti Zuhra? Yace zata taho girki yasa bamu fito tare ba.
Basu dade ba kuwa sai gata da kwandon abinci. Bata tashi daga kan sakarta ba sai da tayi mai yawa ta yadda abin da ya rage mata saura kadan. Itama ko kallo bata ishe Izzatu ba duk da halin ciwon da take ciki. Sauran 'yan uwan Hamza suma duk sun zo. Zuhra ma ta kira Baba ta fada masa Izzatu na asibiti yace zasu zo washegari tare da Umma.
Anti Larai kanwar Raliya tazo tare suka karasa yinin sai dai ta baro maigidanta babu lafiya saboda haka bazata iya kwana a asibitin ba. Dole aka yanke shawarar Adabiyya da Zuhra su kwana da Izzatu. Ranta inyayi dubu ya baci amma ko tashi bazata iya yi ba shiyasa dole ta hakura. Shabiyu saura na dare su Zuhra suka fita suka bashi wuri ya dan zauna wurinta. Sai lallabata yake tana kuka ita bazata zauna da wadda tayi sanadiyar zubar mata da ciki ba. Da kyar ya lallabata yace gobe shi zai kwana. Haka suka rabu ranta a bace. Itama Zuhra yayi mata sallama sannan ya tafi gida.
********
Wasu matasa ne su uku duk da bakaken kaya harda abin rufe fuska suka shigo cikin kauyen da gudu da cikon na hudun a kafadar wanda yafi sauran girma. A kofar wani katon family house suka ajiye na kafadar wanda yake ta zubar da jini sakamakon harbinsa da aka yi a cinya suka gudu. Da yake tsakar dare ne babu wanda ya kula dasu. Sai can wasu maza biyu suka zo wucewa a buge suka ga mutum a kwance a kasa. Da har zasu gudu sai daya ya haska shi da touchlight, da sauri ya karaso giyar da yasha ta fara barinsa yace sa dayan kazo mu taimaka masa Felix ne kanin Mr Oscar miloniya.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [10/10, 1:59 PM] +234 809 156 9113: AL'ADUN WASU 66
Batul Mamman(Mrs)
Daga Zuhran har Adabiyyan babu wanda Izzatu take son gani. Har gara Adabiyya tunda ita kanwar Hamza ce. Haka suka kwana jugum jugum ba abin suyi hira ba a junansu tace sun dame ta. Sau biyu Zuhra na fita kiran nurse a canjawa Izzatu drip idan ya kare. Ko baccin kirki bata samu ba amma banda sakon harara da tsaki babu abinda Izzatu ke aika mata. Wurin karfe bakwai Nura ya kawo Hamida da abinci yace Hajiya tace ya tafi da Adabiyya gida itama Zuhra ya kaita gida.
Zuhra suka fara kaiwa. A falo ta hadu da su Khalifa duk suka rungumeta suna murnar ganinta. Khalifa yace wai Mummy bata da lafiya tana asibiti? Zuhra tace kuyi mata addua Allah Ya bata lafiya. Daddy ya tashi ne? Tala tace bai dade da fita ba kika shigo. Hanyar dakinta ta nufa tayi wanka Nana ta soma yi mata rigima wai sai ta goyata gata akwai jiki. Haka Zuhra ta sabata a baya ta hau sama. Kafin ta fito daga wanka ma Nanan tayi bacci, gefenta ta kwanta itama ko mai bata shafa ba, bata dade ba bacci ya dauketa.
Sai shabiyu da rabi ta farka bata ga Nana ba, tasan kila tashi tayi ta sauka kasa. A gaggauce tayi alwala ta shirya ta sauko. Allah Yasa Tala ta riga tayi girki sai taci ta dauki na asibiti. Kafin ta fita Hamza ya kirata yace ta jira zaizo gida sai su tafi tare.
Kamar ance Izzatu ta kalli kofa tana juyawa ta hada ido da Hamza da Zuhra. Wani karin takaicin ya isheta dama dakin daga su Mama sai Umman Zuhra. Tare suka zo da Baba shi ya tafi ya barta da Maman su Hajara. Zuhra murna an ga Umma sai washe baki take yi. Bayan ta gaishe da kowa kusa da ita ta zauna kamar zata shige ciki. Mama ta rinka tsokanarsu wai itama a bata sirrin shagwabar nan. Umma dai har kunya taji ita kuwa Zuhra ko a jikinta.
Kamar jiya yau ma Zuhra tayiwa Izzatu sannu kin amsawa tayi tana wani yamutsa fuska. Suna haka Raliya da Larai suka shigo. Ganin mamanta nan da nan Izzatu ta soma kuka. Tausayinta suka rinka yi ana ganin kamar duk saboda ciwo ne ga rashin mahaifa.
Haka su Zuhra suka zauna ana ta zuwa dubiya. Anti Faiza ma tazo tare dasu Mariya don sun zama kawaye. Ana sallar Isha su Hajiya zasu tafi Hamza yace Zuhra ta bisu Nura ya ajiyeta a gida. Babu musu ta tashi suka yi sallama da Raliya wadda ba kamar 'yarta ba ita tana dan sakar mata fuska suka tafi.
Sai shabiyu saura Hamza ya dawo ya shiga dakin Zuhra. Bacci ya gansu suna yi ita da su Junior ga TV a kunne. Murmushi yayi cikin jindadin yadda take kula da komai da ya shafe shi ya kashe TV din ya rufe musu kofa. Da safe bayan su Khalifa sun tafi makaranta Zuhra ta koma ta dan kwanta. Kafin ta tashi Hamza ya tafi office daga can ya wuce asibiti. Yau saka ta zauna tayi sai da ya rage gabadaya saura biyar sannan ta tashi tayi jallof din couscous wadda tasha hanta da kayan lambu. Bata dade ba ta gama ta sake yin wanka.
********
Izzatu ke kuka tana fada ita dole sai Hamza ya saki Zuhra idan ba haka ba aurensu yazo karshe. Babu kowa a dakin daga shi sai Raliya da ta kwana a wurinta. Dukkanninsu sai rarrashinta sukeyi suna bata hakuri amma ta rufe ido tace bazata taba zama da Zuhra ba. Idan wata matar yake so ta amince yaje ya auri 'yar boko irinta amma bazata yi kishi da kazama kamar Zuhra ba. Duk da cewa maganganunta nayi masa zafi saboda ko kadan baya son abinda zai taba mutumcin Zuhra amma saboda tausayin yanayin da Izzatun ke ciki yasa yake bata hakuri. Idan ta warke dole asan me ake ciki don bazai dauki wannan wulakancin ba.
Suna haka wayarsa tayi ringing. Yana ganin Cutie yayi murmushi ya dauka. Can kasakasa take magana tace Ya Hamza kana asibiti ko?
Ina nan, ya akayi?
Garin sauri na fito na manta jakata gashi mun kusa isowa asibitin. Ka fito ka bawa mai adaidaita sahu kudinsa kada ya tara min jama'a.
Sai da yayi dariya sannan yace bazan zo ba, zan bari ya dan saita min bakin nan naki mai tsiwa.
A shagwabe tace to shikenan zan ce ya saita shi irin yadda kake yi dinnan.....
Ke, wallahi kada ki soma ina bakin gate din asibitin.
Dariya tayi ...da ka koma kawai Ya Hamza ko na rabin minti sai.....
Cutie bana son irin wannan maganar please. Na janye da nace ya saita miki baki. Ni kadai zan saita kayana.
Sun dauki mintuna suna hira har suka karaso baki gate din ya biya mutumin ya tayata daukar kwandon abincin.
Suna tafe suna hira abin sha'awa yace yau zaki san ni kika tsokana. Gwalo Zuhra tayi masa ai dai kai ka fara meye laifina don na taya ka? A haka suka iso kofar dakin. Hamza zai bude kofar kenan ya jiyo abinda Raliya ke fada wanda yayi matukar razana shi.
Yanzu ke Izzatu har kina da bakin cewa Hamza ya saki matarsa? Me tayi miki da zaki tsaneta haka.
Mum kinfi kowa sanin ni bazan iya sharing mijina da kowa ba talkless of kazama irin wannan yarinyar.
Raliya tayi tsaki....ni bansan baki da hankali ba sai yanzu. Izzatu mahaifa aka cire miki fa. Kina tsammanin idan ya saki Zuhra bazai auri wata ta cigaba da haifar masa 'ya'ya bane?
Muryar Izzatu suka ji tana kuka tace wallahi Mum idan ya dage sai ya zauna da yarinyar nan to zai ga tashin hankali. Sai na hana shi nutsuwa balle ya sami lokacin soyayya da ita.