Sashe 39
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Raliya na zaune a falo tana waya taga Izzatu ta shigo. Ko sallama batayi ba da wadda suke wayar ta tashi a gigice. Izzatu lafiya? Me ya faru?? Ina yaran??? Tambaya take tana kuma leka waje taga ko zata fahimci abinda ke faruwa. Izzatu tayi murmushi Mum kina da rudewa wallahi. Sai watso min tambayoyi kike a lokaci guda. Tayi maganar tana shirin zama akan kujera. Idanun Raliya kamar su fado don fargaba muryarta har rawa take yi tace kinga I..Izz...Izzatu bana son jan rai. Idan wani abinne ya faru ki fada min tun wuri. Hamzan ya sakoki ne ko me? Izzatu tayi jifa da mayafinta, Ohhh Mum ko ruwa ki bari nasha mana. Ki kwantar da hankalinki all is well.
Hankalin Raliya bai kwanta ba sai da Izzatu ta gama cin abinci sannan tace Mum nazo yiwa Dad sallama ne fa na tafiyarsa Japan. Ran Raliya a bace tace Izzatu zan ci........ki wallahi. Shine zaki zauna ki tayar min da hankali tun dazu ina tambayarki kinyi shiru. Hawan jini kike so ya kamani ko ciwon zuciya? Kuma ko jiya kafin mu baro Kaduna sai da muka sake maganar nan dake nace an daga tafiyar tasa. Munyi maganar nan yafi sau biyu, ina hankalinki ne? Izzatu ta bude baki Mum da gaske na manta munyi zancen nan. Raliya tace to sai ki kwana yau gobe ki kama hanya ki koma gidanki. Izzatu ta kalleta sannan tace Mum nifa sai next week zan koma. Na riga na tambayi Hamza ya barni nayi sati daya a nan. Dariyar takaici Raliya tayi tace lallai Izzatu baki da kai, sai kace ba kece mai korafi akan auren da yayi ba shine kika basu wuri su sha soyayyarsu hankali kwance.
Ya zaki rinka fadin haka Mum? Izzatu ta fada kamar tayi kuka.
Ya bazan fada ba Izzatu? Banda satin da kika je kika yi a Kaduna kamar bikin Najah ake yi kanwarki yanzu kuma kin taho nan zaki kara wani satin. Allah Ya baki sa'a, ni yanzu nawa ido ne idan kina wannan rashin hankalin.
Tana gama magana ta tashi a fusace ta bar Izzatu a wurin. Itama nata ran a bace yake tace ni nasan waye Hamza kuma na yarda dashi. Bazai taba kula wannan kazamar yarinyar ba. Lokaci kawai yake jira ya saketa kowa ya huta.
Washegari tun karfe tara Izzatu ta gama shiri ta tafi dakin Raliya. Rungumeta tayi sannan tace goodmorning Mum. Raliya ta daure fuska. What is good about the morning Izzatu? Izzatu tayi dariya wai har yanzu fushi kike yi don nazo? Kina kallo yadda Dad yaji dadin ganina. Tunda duk yaran nan sun koma school kamata yayi kema kiji dadin zuwana. Raliya tace jindadi na daya ne ki koma gidan mijinki. Ina jiye miki tsoron sharrin kishiya Izzatu. Amma, ki cigaba. Ina zaki da sassafe haka keda bakya tashi da wuri? Izzatu tace aron mota zaki bani cikina ke dan yi min ciwo zani asibiti. Raliya tace ki jira dreba ya kaiki dai. Wane irin ciwon ciki ne? Dan tsaki Izzatu tayi saboda bata son yadda mamanta ke jan zancen. Nima ban sani ba shiyasa zani.
Karfe goma da 'yan mintuna tayiwa Izzatu a wani asibitin kudi. Tayi sa'a babu layi sosai shiyasa bata dade ba ta shiga wurin likita.
Likitar mace ce Dr Mardiya suka gaisa da fara'arta ta dan kalli file din gabanta. Izzatu Sunusi ko? Izzatu amsa da gyada kai. Dr Mardiya tace to Izzatu meye matsalarki. PT strip(abin gwajin ciki na gida) guda uku Izzatu ta nunawa likitan tace ciki gareni ina jin bazai kai wata biyu ba amma ya dan wace daya. Ina so ayi aborting din cikin bana so. Dr Mardiya tace baki da aure ne kike son zubar da ciki? Izzatu tace ina da aure da yara uku sun isheni. Idan cikin ya zube ina so ko dai a daure min mahaifa ko a cireta gabadaya. Bansan yadda akayi na sami cikin nan ba bayan ina shan pills.
Sai da likitar ta gama 'yan rubuce rubucenta sannan tace tunda kina da aure bazamu cire miki ciki ba ba tare da izinin mijinki ba sannan kuma sai munyi bincike mun tabbatar cikin zai iya zama hatsari ga rayuwarki.
Ran Izzatu ya soma baci, kinga doctor zan biyaku ko nawa ne a cire cikin nan. Plan dina na haifi yara biyu accidently na haifi ta ukun to sun isa haka. I am just 33 year old amma saboda haihuwa har na fara loosing shape. Boobs dina sun fara kwanciya saboda shayarwa. Dr Mardiya tayi murmushi tace baiwar Allah ashe da gaske ne idan dadi yayiwa mutum yawa sai yace Allah gani kasheni. Ko kinsan mata nawa ke neman haihuwa ido rufe amma irinku da yawa sai suzo zubar da ciki. Har gara wadanda suka yi na titi ko masu talauci akalla duk da hakan ba dalili bane amma suna da abin fada. Ke kuwa saboda kada kiyi loosing shape zaki zubar da ciki. To ai dole shape da kirji ya tafi tunda ko babu haihuwa akwai tsufa. Ina mai baki shawara kije ki sake tunani zaki gane wannan abinda kike son yi bai dace ba.
Rai na kuna Izzatu ta fito daga office din likitan. Haka kawai zata sakata a gaba da wa'azi. A Kaduna ta gane tana da cikin shiyasa ta yanke shawarar zuwa Abuja ta zubar batare da sanin Hamza ba. 'Ya'ya uku dai ai sun ishesu. Asibiti biyu taje bayan nan duk sai likitocin su bita da nasiha. Karshe wani pharmacy taje ta siyo maganin zubar da ciki ta tafi gida. Yaushe zata yi ta ciki da haihuwa Hamza ya zo ya dena ganin kyanta.
********
Zuhra da yara ta kwana a dakinta. Tala ta dauko mata pampers har uku da za'a sakawa su Khalifa saboda duk suna fitsarin kwance. Ajiyewa kawai tayi don bata da niyar saka musu. Tsabar son jiki na mata yara sun girma sai muyi ta kakaba musu pampers bama tausayin masu siyowa da jikin yaran. Hamza yazo yace ta bari su kwana a dakinsu da Tala tazo ya cigaba da jinyarta tace ita ta warke. Duk yadda yayi Zuhra taki yarda ta kuma kwana a dakinsa. Ba komai ke hanata ba sai kunyarsa da take ji da kuma soma sabawa da tayi na kasancewa tare dashi. Dawowar su Khalifa ya kara tuna mata idan Izzatu ta dawo dole abubuwa zasu canza sannan uwa uba bata san matsayinta a wurin Hamza ba. Tana so taji ina batun maganar rabuwarsu ta kwana.
Cikin dare alarm ta saka sau uku tana tashi ta kai yaran dukkansu suyi fitsari hakan yasa da gari ya waye Junior ne kawai yayi shima da asuba ne ta sauka kasa ta tambayi Tala me ake basu abincin makaranta. Sai da ta gama taje tayi musu wanka.
Suna breakfast Nana kuwa bata tashi ba Hamza ya sauko. Kin kula Zuhra yayi wai yayi fushi. Dariya kawai tayi sannan ta gaisheshi. Khalifa na murna yace Daddy yau banyi fitsari ba ni da Nana, Junior ne kawai yayi. Hamza yaji dadi sosai yace da gaske? Khlaifa yace yes Daddy kuma Maama bata saka mana pampers ba kaimu toilet ta rinka yi, tace duk mun girma mun zama big boys. Junior ya fashe da kuka ance yayi fitsari. Maama ba kince sau daya nayi ba. Zuhra ta dorashi akan cinyarta sau daya ne mana kuma gobe bazaka yi ba in sha Allah. Daddy ayi mana addu'a mu dena fitsarin kwance. Duk wanda ya sake yi zamu cinye abin dadi bazamu bashi ba. Wani irin kallo Hamza yake bin Zuhra dashi mai nuni da farincikinsa a fili. Yace to kowa ya daga hannu muyi addu'a. Bayan sun gama suka dauki jakunkunansu da lunch box suka fita waje wurin motarsa. Zuhra tana dauke kayan da suka ci abinci Hamza ya dawo ya dan tsaya a bakin kofa Cutie bazaki rakani bakin mota ba? Yana cikin lessons dinmu fa. Murmushi tayi tace Ya Hamza ka gama fushin? Daga hannu yayi zai dalli bakinta ta goce, zan gamu dake ne idan na dawo ya fad yana murmushi. Kiyi min addu'a kinji. Yau in sha Allah zan biya mutanen nan kudinsu na rabu da bashi. Tace In sha Allah zanyi, sai ka dawo, Allah Ya tsare. Cike da nishadi kamar ba wanda yake shirin gamo da matsin rayuwa ba ya kai yaransa makaranta ya wuce office. Yana ganin indai Zuhra na tare dashi in sha Allah komai zai zo masa da sauki.
[10/4, 1:40 PM] +234 815 728 4163: AL'ADUN WASU 60
Batul Mamman(Mrs)
Zaman Zuhra da su Khalifa abin sha'awa. Kwana biyu da dawowarsu amma sun saba sosai da ita. Wannan ne ya ragewa Hamza radadin da yake ji a ransa na halin da yake ciki. A yadda ya kukuta ya hada kudin nan kaf gida da account dinsa bashi da kudin da ya kai dubu dari biyu da hamsin. Kudin man inji kadai ya ishe shi banda na mota da sauran abubuwan da zasu iya tasowa. Gashi Izzatu ta sanar dashi motarta da suka tafi Kaduna ta lalace a ta haya a tafi Abujan ta bar motar a gidan Kawunta . Yana cikin tunani Zuhra ta shigo falon da sauri kamar wadda aka biyo da littafi a hannu. Saurin gyara yanayin fuskarsa yayi saboda kada ta gane yana cikin damuwa. Ya rasa yadda ake take sani sai kace mai gani har hanji. Dan durkusawa tayi a gabansa tace Ya Hamza don Allah taimaka ka fitar dani kunya. Mtswwww shiyasa Baba yace na dan maida hankali a karatu ko na koyawa yara homework ne na samu saboda kada naji kunya wata rana. Gashi abinda yake fada yau ya faru. Suma malaman da kyuyar tsiya sai a bawa yaro homework biyar a rana. Tunda ta fara magana Hamza ke kallonta yana murmushi. Zuhra ta iya sawa ya manta da damuwarsa. Lebenta ya hada ya kama da yatsunsa, to aku sai zuba kike yi baki fadi ainihin abinda ya kawoki ba. Hannunsa ta nuna da ya rike mata baki, yana saki ta kwabe fuska shine zaka matse min baki ko? Yace to ko na bashi hakuri ne. Matsawa tayi baya don ta tuna yadda ta kare ranar da ta nemi a bawa lips dinta hakuri., ba sai ka basu ba na hakura.