← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 67

Sashe 32

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanka ta dauki lokaci tayi don so take duk abinda ya koya mata ta rinka yi. Zafin yau da sauki akan na jiya shiyasa ta dan shafa mai kadan sannan ta shiga barnar bodyspray. Har humrarta da bata taba shafawa ba ta dauko kwalba daya mai kamshi ta rinka bin duk gabobinta tana shafawa. Rigar baccin da ta dauko yar karama mai siririn hannu har tafi ta jiya kankanta da rashin kauri. Wani dadi take ji ashe haka tsafta ke da dadi...gadonta ta haye ta ajiye fitilar a bedside drawer tayi kwanciyarta. Zafi baisa ta rufa ba amma ba bacci ma take ji ba. Tunani take ko me Hamza yake yi yanzu.......

Kusan rabin awa kenan da yayi wanka ya gama shirin kwanciya sai dai ko alama babu bacci a idanunsa. Zuhra yake son gani amma yana kokarin hana zuciyarsa sabawa da son kasancewa tare da ita. Sakon kudin da Mama ta bashi ya tuna yana wallet dinsa ga wayar da ya siyo mata duk bai bata ba. Murmushi yayi ya tashi don ya sami dalilin zuwa dakinta. [10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 51

Batul Mamman(Mrs)

Kiran farko na assalatu Hamza ya bude idonsa. Murmushi ne ya bayyana a kyakykyawar fuskarsa saboda jin har yanzu Zuhra na jikinsa. Hannunta ya zagaye cikinsa, ga kanta a wurin wuyansa. Yana jin lips dinta a wuyan nasa. Sake matseta yayi zuciyarsa na fada masa yayi a hankali kada ya fada soyayyar da zata iya zame masa rigima nan gaba. A hankali ya rinka shafa kanta yana kiranta da sabon sunan da ya rada mata. Cutie ki tashi asuba tayi. Sake makalewa tayi a jikinsa batare da tasan halin da hakan ke sake jefashi ba. Cikin dabara ya fara janye jikinsa sai itama ta bude ido. Ji yayi ta tashi da sauri Ya Hamza ba dai a haka muka kwana ba. Mikewa yayi ni bana son gulma kin gama makale min a jiki kamar babu pillow a kan gadon zaki wani wayance yanzu. Kunyarsa sosai take ji ta koma cikin bargo ta dukunkune kanta. Gudun kada ya makara sallah yasa yayi murmushi kawai ya fita. Sai da taji ya rufe mata kofa ta tashi ta shiga toilet. Har addua tayi bayan ta idar da sallah,kada yayi mata kallon mara kamun kai.

Tana idarwa dakinta ta gyara da toilet sannan ta sauka ta share falon tayi mopping. Falon ne da girma shiyasa taga gara tayi aikin da wuri. Tun dare ya fada mata bread kawai zaici da safe da tea, wani maidadi ya siyo a Grand square. Ruwan zafi ta dafa ta juye a flask ta hada da kayan tea ta kai dinning table ta ajiye. Ta sallami maigadi ma sannan ta koma daki ta tsefe kitson kanta ta kama gashin da ribbon. Wanka ta shiga ta bata lokaci a bandaki don yanzu an dena jika jika. Ta zauna gaban mudubi ta shafa mai sannan ta rinka feshe jikinta da turaruka. Ta kula Hamza na son kamshi sosai, yau so take ta burge shi yasan tana daukar karatun da yake mata. Wani dogon wando tight baki ta saka ta hada da riga pink wadda ta kusa gwiwarta mai hannu three quarter. Rigar da dan matseta daga sama sannan ta yi fadi kadan daga kasa. Da Hajara suka je kasuwa aka siyo kayan da kudin sakarta. Hoda tasa da kwalli sai dan janbaki kadan pink wanda tayi lining lips dinta da liner pink amma mai dan duhu. Har wani tsalle tayi da tafi ganin tayi kyau. Ta fesa turare a kayanta sannan ta dauko karamin pink da bakin mayafi ta daura irin yadda dai 'yan gayu suke yi. Kasa ta sauka har lokacin Hamza bai sauko ba gashi har takwas da rabi. Tana son zuwa ta duba ko bacci ya koma bayan ya dawo daga masallaci amma tana jin kunyar kayan jikinta.

Wayarta da ta dan sami chaji ta duba taga text din Hajara tana sanar da ita zata zo wurin shabiyu ta kira wayar tun jiya taji a kashe. Wayyo dadi, Zuhra sai murna. Kada Hamza yace wannan karon bata fada masa zata yi bakuwa ba ta yanke shawarar zuwa dakinsa.

A darare tayi sallama ta shiga falon sai taji ya amsa daga cikin daki. Kanta tsaye ta shiga ciki ta ganshi daure da tawul yana tsaye a gaban wardrobe dinsa yana neman kayan sawa. Kafin ya juyo ta runtse idonta tana cewa yayi hakuri. Dariya yaso yi sai dai shigarta ta matukar daukan hankalinsa. Ji yake kamar ya dauketa yayi hugging. Zata fita yace tsaya a nan ina zuwa. Kayan ya saka sannan ya taho gabanta da coat a hannunsa da necktie. Kamshin turarensa ya sanar da ita isowarsa. Cikin murya mai jan hankali yace bude idonki Cutie. A hankali ta budesu ta ganshi tsaye da shirt dinsa duk maballan a bude. Yace jiya na fada miki ana taimakawa miji yasa kaya ko? Kai ta gyada kawai tana kallon kasa. To balle min buttons dinnan naga ko kin koyi karatun. Ta dan zaro ido tana kallonsa. Come on Cutie ina da meeting kada na makara. Hannu na rawa ta soma ballewa daga kasa. Shi dariya take bashi ga tsoro ga baki. Har tazo na karshen wuyansa jikinta sai bari yake. Bayan ta balle ya bata tie din saura wannan. A sanyaye tace ban iya daurawa ba. Gwada mata yayi sannan ya ware ya bata ta daura masa. Kallon da yake mata yasa hannunta ya kasa tsayawa sosai. Nasa hannun ya saka ya taimaka mata har suka daura tare. Yau duk ta kasa kallon shi ya dago kanta da hannunsa sai kawai ta rufe ido tace Ya Hamza kunyarka nake ji ka barni na fita. Zagayeta yayi da hannuwansa sannan ya matso da ita gabansa. Cutie kinyi kyau. Ta danyi murmushi da gaske? Yace da wasa. Kafa ta buga a kasa cike da shagwaba tace haba Ya Hamza mana kace nayi kyau don Allah. Hancinta yaja sannan yace kinyi sosai shiyasa na saka miki Cutie. Muje muyi breakfast kada na makara. Dan tsayawa tayi yau ban gaisheka ba, sai ta durkusa ina kwana ya jiki? Tayar da ita yayi tsaye kinga irin wannan gaisuwar bata dacewa da miji da mata. Kinga yadda ake yi ko don gaba. Duka hannuwansa yasa a kafadunta yayi kissing din lips dinta lightly. A take taji wani abu yana yi mata yawo a ciki. Shi kuwa jan hannunta yayi suka sauka don yasan ko rabin minti suka kara a wurin abinda zai mata sai ya fi wannan.

Yau cin abinci nasu babu wata hira ake yi domin dukkansu tunani suke. Hamza sai tambayar kansa yake ko dai ya fara son Zuhra ne? Itama Zuhra tambayar da take yiwa kanta shin zata iya rabuwa da Ya Hamza. Suna gamawa ya tashi tace anjima Hajara zata zo kanwar Anti Faiza. Yace nima kinga na manta su Adabiyya zasu zo kwana. To da safen nan kuma naga text din Jidda ita da Mariya da matar Ibrahim kanina zasu zo. Inajin duk da yaransu zasu zo anya zaki iya da baki da yawa haka? Ga mamakinsa murna take yi sosai, zan iya mana in sha Allah. Gara na dora girki da wuri saboda yara ma. A dawo lafiya....bata saurare shi ba shige kitchen tana tunanin abinda zata dafawa bakin nata. A hadith na shabiyar a Arba'una Hadith Manzon Allah SAW yace duk wanda yayi imani da Allah da ranar karshe to ya karrama bakonsa. Kuma tarbiyar Ummanta da Baba kenan. Ita yanzu me zata dafa ta burgesu kuma kowa yaci ya koshi?

Hamza ya gaji da tsayuwar mamakin irin wannan murna da Zuhra keyi ya dauki jakarsa ya fita. Izzatu bata taba son 'yan uwansa su zo gidansa ba. Idan sunzo ma zasha ruwa ne da juice su koma gida. Zuhra daban take.... Sai da ya shiga mota ya tuna da sabuwar wayarta ya dawo ya dauko har lokacin tana kitchen. A tsaye ya ganta ta rike haba ita a dole tunani take. Tana ganinsa tace yauwa Ya Hamza dan bani shawarar abinda zan dafa mana. Yace naki din, nida kika tafi kika barni daga cewa zaki yi baki. Ta marairaice masa to yi hakuri kaji Ya Hamzaaaaa. Murmushi yayi Cutie kina abinda kike so. Tayi murmushi tana kallonsa. Shima yayi mata kyau. Zo ga wannan I hope you like it. Da dan murmushi tace ina fa dan gane turanci kalma me tsauri ce dai bana fahimta. Amma dan fassara min abinda kace yanzu turancinka ba irin na malamin English dinmu bane. Fassarawar yayi yana dariya ya mika mata wayar. Gashi nan na saka miki wani sim din sai ki saka na daya wayar tunda mai sim biyu ce. Bade baki kawai tayi tana kallonsa. Sai kuma hawaye Ya Hamza wannan tawa ce? Ya gyda kai, tace Allah Ya saka maka da alkhairi Ya baka ladan faranta min. Allah Ya kareka daga dukkan sharri. Nagode sosai. Wayar dubu ashirin Zuhra kewa kuka da wannan addua, Izzatu kuwa dubu dari ya bata da zata yi tafiya amma kirikiri ta nuna ta raina. Matsowa yayi gabanta ya goge mata hawayen da hannunsa sannan yace nagode da adduarki. Su kuma bakin kiyi musu danwake idan kin iya, a iya sanina dasu Mariya duk mayun danwake ne. Yana gama magana ya fita tabi bayansa. Sai da motarsa ta fita daga cikin gidan ta dena daga masa hannu.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 52

Batul Mamman(Mrs)
Chapter 32 · 0% Book details