← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 67

Sashe 33

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zuhra aiki ya kankama. So take ta gama abincin kafin su iso yadda ba zasu zauna da yunwa ba. Katuwar roba ta samu ta dora danwake sai da tayi tukunya uku tana yi tana juyewa a wata roba mai dan girma. A kalla mutum goma sha biyu zasu ci su koshi sosai. A ranta tace idan bai isa ba sai ta kara. Bata san adadin yaransu ba ga maigadi. Bayan ta gama ta dafa kwai guda goma, ta wanke tumatir, albasa, koren tattasai da cucumber ta ajiye bazata yanka da wuri ba kada yayi tsami. Man da ta soya yasha albasa sannan ta duba bata da juice da yawa. Zobo tayi wanda ta dafa da citta da kaninfari. Ta tace ta saka sugar da lemon tsami sai ruwan cucumber da ta gurza ta tace. A leda ta kulla ta zuba a fridge saboda jug bazai shiga ba. Tana sauke mai ne ya tsallo mata a wuya har wuri biyu. Wani uban tsalle ta doka saboda zafin da taji ta soma karanta ALLAHUMMA AJIRNI MINANNAR saboda neman tsari daga azabar Allah. Allah Ya kiyayemu, amin. Sanda ta gama komai shadaya da rabi ta gyara kitchen sannan taje tayi wanka. Riga da zani ta saka tayi irin kwalliyar dazu mara yawa ta sauko kasa.

Sabuwar wayarta ta dauko sai dai ta kasa gane kan wayar. Tana ta tabe-tabenta taji sallamar Hajara. Kamar kananan yara haka suka rungume juna suna tsalle. Can Hajara tace ke dena jijjiga ni kada ki barar da danki ko 'ya. Zuhra ta zaro ido tana shafa cikin Hajara. Doke hannun tayi to yar duniya meye na shafa min ciki. Kema ina tunanin akwai fa, ji yadda kika yi haske kika kara cikowa. Zuhra ta kama hannunta zo ki zauna yau tattalinki zan taya Yaya Sahabi. Ah su Hajara daga aure sai ciki. Hajara tace ke bana son iskancinki fa. Kema naki yana hanya idan babu in sha Allah. Ai burina mu shiga labour room tare. Shakiyanci suka yi ta yiwa juna. Daga baya suka shiga kitchen da Zuhra tace kannen Hamza zasu zo. Hajara ta bude taga danwake...anya Zuhra kina da kai kuwa? Yan uwan miji zasu zo ki rasa abinda zaki basu sai danwake? Zuhra tace yayansu ne yace shi suka fi so. Plates suke hadawa da cups suka ji sallama a falo. Dama Zuhra da hijab dinta a hannu saboda kada suzo da maza. Kuskuren da mata da yawa keyi kenan. Yan uwan miji maza ko abokansa su zo sai mu fito babu lullubi ko hijab. Muji tsoron Allah mu kare mutumcinmu. Mota biyu suka yo duk a gidan nasu suka hadu suka taho tare. Zuhra fuskar nan dauke da fara'a sai kunyar su Mariya take yi. Suka gaisa da Nura yace zai tafi sai bayan sallar Juma'a zai dawo. Bajewa suka yi da 'ya'yansu ana ta hira da Zuhra. Ta sake musu sosai kada ma Adabiyya da Hamida suji labari. Ta tambayi yaran sunayensu suka fada mata. Karamin dan da Ummahani ke goyo kuwa Zuhra ta goya shi saboda ya hana mamansa sakewa. Tun yana kuka har yayi bacci. Da taimakon Hajara dasu Adabiyya ta hado musu abinci. Cikin tabarminta ta shimfida manya biyu. Jidda tace ai ki hada mana a tray kawai muci tare yafi kara zumunci. Zuhra na murmushi tace haka Ya Hamza ma yace. Su Ummahani suka hada ido suna dariya. Yaya yaji dadin aure....

Sakewa da jindadin da basu taba yi ba a gidan dan uwansu yau sunyi. Yabo da addua kam Zuhra tasha a wurinsu. Nura yafi kowa santi da ya dawo aka hada masa nasa abincin. Bayan sun gama kuma dukkansu sunsa hannu wurin gyara falon da wanke wanke. Tamkar 'yan uwana jini haka suke jin Zuhra. Sai da sukayi sallar la'asar suka fara haramar tafiya. Ana haka sai ga Hamza ya dawo daga wurin aiki. Shima yau ya gaji sosai. Kudi ya kusa kammaluwa zai sallami su Mr Peter ya rabo da kaya. Dadi yaji yadda ya tarar da kannensa sun cika gidan ana ta hira. Zuhra na tsakiyarsu da goyo kamar sun shekara tare. Suna ta gaishe shi da yi masa sannu da zuwa ita kuwa kanta na kasa. Duk kunyarsu take ji, tana kallo yace bari nayi wanka na sauko kafin ku tafi. Ummahani ce ta dan zungureta Anti Zuhra tashi mana Yaya ya dawo. Indai don wadannan ne, ta nuna Jidda da Mariya suna dariya...duk ki manta dasu kowacce ta iya rike miji in fada miki. Zuhra harda rufe fuskarta da hannuwanta. Hajara ce ta tasheta ta karfi. Zata hau saman Ummahani tace kawo dan nan kada yace zamu bankare masa kirjin amarya.

Ita fa ba saba binsa daki sannu da zuwa tayi ba. A falon ta dan tsaya sannan tayi sallama tare da cewa in shigo. Daga ciki Hamza yace yes come in. Kwance yake akan gado amma kafafun na kasa ko takalmi bai cire ba. A tsorace tayi saurin zuwa gaban gadon, cikin sanyin murya tace...Ya Hamza jikin ne? Harararta yayi sai yanzu kika ga damar zuwa. Zuhra tace ina? Zama yayi suna fuskantar juna tana durkushe a gefen gadon. Yanzu mijinki ya dawo ba sannu da zuwa bare ki karbi jakata. Tace yi hakuri, bai kula ba ya cigaba da cewa kuma na taho daki baki biyoni kin cire min kaya kinyi min wanka ba. Zuhra ta mike da sauri....eyyeeee Ya Hamza wanka? Ya kashe mata ido wanka fa. Don Allah kayi hakuri....sai kawai ta soma hawaye. Saurin tashi yayi ya janyota jikinsa. A cinyarsa ya zaunar da ita tayi saurin rufe ido. Wai meyesa Ya Hamza ke yi mata hakane yanzu. A hankali yake magana Cutie you scared me. Na kiraki yafi sau goma baki dauki wayar ba. Dafe kai tayi... ina jin hayaniya ce tasa banji ba amma kayi hakuri. Kokarin tashi take yi ya sake riketa sosai yana kallon wuyanta. Cutie me ya sameki a nan ya fada yana dan taba wurin...auchh Ya Hamza da zafi fa. Cikin shagwaba take magana tana kara narkewa jikinsa ba tare da ta sani ba. Sorry meye ya sameki? Murmushi tayi masa mai ne ya kona ni da har zanyi kuka saboda zafi sai na tuna ba karamin lada aka rubuta min ba. Na kone a kokarin karrama baki... ta washe baki tana murmushi. Hura wurin ya rinka yi yana mata sannu. Zuhra dai duk tsigar jikinta ke tashi ta dan wayance, 'yan gidanku suna da kirki duk ina sonsu. Zanyi kewarsu idan na tafi. Tashinta yayi shima ya mike...tam, zaki fara ko? Ni tashi muje na sallamesu sai na dawo nayi wankan.

Suna saukowa su Mariya suna ta dariya. Hamza yace zan hanaku zuwa gidan nan tunda gulma kuka zo yi. Cikin raha suka yi sallama duk suka tafi. Dubu biyu ya bawa Hajara ta shiga mota. Tayi masa godiya sosai. Suna shiga mota mai gyaran inji yazo ya fara aiki.

Zama Zuhra ta sake yi suka kafa sabuwar hira dasu Hamida sai ga Hamza ya leko yana kiranta. Tace bari ta sauko sai suyi shawarar abincin dare. A kofar dakinta ta ganshi ya bude tabi bayansa. A ina su Hamida zasu kwana? Zuhra tace ai tare zamu kwana a nan dakin kayansu na cikin kwaba. Sai da ya gama dariya sannan yace don Allah ki dena cewa kwaba sai a zata baki waye ba, wardrobe sunanta. Ta sha kunu sai kayi ta tsokanata ko? To Cutie kauyancinki ne yayi yawa. Yanzu dai har su Adabiyya su tafi a dakina zamu rinka kwana tare. Kinga kada suyi tunanin akwai matsala a tsakaninmu sannan zamu cigaba da lessons dinmu ko. Yana kare magana ya bude wata drawer inda yaga ta ajiye kayan bacci ya dauko mata wasu riga da wando. Rigar dai kamar bra ta sama sai ta bude kadan taga kasa. Wandon kuwa ko cinya bai gama rufewa ba. Zuhra na gani ta kwace kayan daga hannunsa a kunyace, ni gaskiya bazan saka wannan a gabanka ba. Yace to dauko wadda kike so....ta fara neman wata kenan yace amma ki kwana da shiri duk wadda kika saka ko kinyi bacci sai na cireta. Baki bude ya barta ya shiga toilet ya dauko brush dinta. Sannan ya dibi turaruka da body spray harda man shafawa. Ki karo wasu abubuwan idan kina bukata harda kayan da zaki saka da safe. Fita yayi ya barta a tsaye ta ma rasa abinda zata yi.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 53

Batul Mamman(Mrs)

Tunda suka yi maganar nan Zuhra take bata rai ko dakin nasa bata je ba . Ya ma za'ayi yace tasa wannan kayan duk ya gane mata jiki. Ta fasa kwana a dakin nasa ma a falon zata kwana a kan kujera. Sun gama girki sannan suka yi sallar Isha. Bayan sun idar tana daura dankwali Hamida tace Anti Zuhra meyasa bakya saka relaxer a kanki gashi kanki yana da yawa, irinsa yafi kyau. Adabiyya ta taba gashin don Allah ki fadawa Yaya gobe ya barmu muje salon din bayan layin nan. Baki ga yadda suka yi suna ba kuma duk musulmai ne matan wurin. Hamida tace ni da bikin Zayya munje har lalle suke yi mai kyau. Don Allah Anti Zuhranmu ki tambayar mana. Zuhra tayi murmushi nifa bana son Antin nan haka kawai bayan inajin duk kun girmeni. Nan aka fara fadar shekaru Adabiyya ta girmeta ita kuma ta girmi Hamida. Duk hirarsu Hamza yana tsaye a bakin kofa yana ji ya dawo daga masallaci. Zuhra ta sake tana ta hira amma tun bayan dawowarsa bai sami damar kebewa da ita ba. Abincinsa ma a falonsa na kasa ya gani. Gyaran murya yayi sannan ya shigo...kun hadu kun cika gida da hira ko sallama bakwa ji. Hakuri suka soma bashi Zuhra ta kawar da kai. Hakan baiyi masa dadi ba don ba na kunya bane, da gani fushi take yi. Tunanin dalilin fushin yake yi amma ya kasa ganewa. Kiranta yayi sannan ya shige falonsa. Kanensa na zaune bare ya tambayeta a nan.
Chapter 33 · 0% Book details