← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 67

Sashe 62

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Muryarta yaji daga bakin kofa tana sallama. Dama a tsaye Hamza yake tana shigowa yayi saurin rungumeta ita kuma tana kokarin ture shi. Su Hajiya kowa sai kawar da kai yake yi. Alhaji da yaso tarasu yayi musu nasiha yace kai Yaya ku bar wurin nan.

Sam Hamza bai ji ba ya fara neman bakin Zuhra.

Alhaji ya daga murya yace kai Hamza zan saba maka. Nace ku bar wurin nan. Wani murmushi yayi ya juya ya kalli iyayensa. Sai a lokacin yaji kunya yaja hannun Zuhra wadda take jin kamar ta nutse a kasa suka fita.

Mama ta kwashe da dariya. Alhaji ni bazan ce komai ba sai Allah Ya kara. Dama rabon kaga rashin kunya yasa kaki bashi matarsa da wuri. Dariya suka soma yi harda Hajiya sai suka kula da Ibrahim da ya rufe fuska da hula. Alhaji yace bana son gulma kaima tashi ka tafi wurin matarka. Da gudu ya fice yana dariya.

****
Rasa dakin da zai shiga da ita yayi ya ja hannunta zuwa dakin Nura. Yana rufe kofar ya juyo yana kallonta. Sai da ya juyata a gabansa yace Cutie babu inda yake miki ciwo? Dariya take yi tace Ya Hamzana babu.

Ya rungumeta sosai yana suna ajiyar zuciya. Ya dago kai yana shafa bakinta...I miss you Cutie. Kiyi hakuri don Allah ban kula dake yadda ya kamata ba. Duk abinda ya faru laifina ne. Yakamata ace naga tafiyarku kafin na koma ciki.

Hawaye fal idonta tace duk ya wuce. Zai sake magana ta rufe masa baki da nata. Sun jima a haka sannan yace Cutie duk kin canja kin kara kyau.

Hannunsa ta kama ta zira a karkashin rigarta. Ya ware ido sosai yana kallonta...tauri fa nake ji Cutie. Sai kuma taji kunya ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi. Ya sa hannuwansa biyu ya dago kan nata....are you pregnant? Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta rungumeshi. A hankali tace wata hudu kenan. Sakinta yayi ya durkusa a gabanta yana shafa cikin cike da kulawa...baby your daddy is back. Yayi kissing cikin sannan ya tashi ya kura mata ido. I love you so much Fatima.

Tace nima haka..

Hamza yace ban karba ba.

Tayi dariya I love you Ya Hamza.

Wani kallo yake binta dashi ya kama hannunta muje ki dauko mayafinki mu tafi gida.

Tace har girki nayi maka kuma su Hajiya basu ce na tafi ba.

Kinga na baki minti goma ki dauko abinda zaki dauko mu tafi idan ba haka ba kuma na maimaita irin abin dazu a gabansu. Fita tayi cikin farinciki ta dauko dan kwandon da ta saka flask din abincin. Dakinsu Adabiyya ta shiga daukar mayafi su Jidda suka fara tsokanarta. Mariya tace kinga wuce ki tafi Mama tace sun yafe sallamar wai wadda kuka yi dazu ta wadatar. Zuhra taji kunya sosai ta fita suka rakata har bakin mota suna ta shakiyanci. Ganin Hamza ya hade fuska yasa suka koma ciki. Shi kuma ya tada mota sai gida.
Chapter 62 · 0% Book details