← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 67

Sashe 29

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dan kadan ta bude kofar ta zura hannu. Wata rigar bacci ce mai kyau amma cotton mara nauyi ta wuce gwiwarta ma da karamin hannu. Yace ki goge jikinki sosai kafin ki saka. Dama ta goge ta saka ta yafa tawul din ta fito. A kan stool din yake zaune yace tunda yau akwai zafi sosai ba sai kin shafa mai ba. Har gabanta ya karasa ya cire mata tawul din sannan ya fesa mata body spray kala uku. Don Allah baki ji dadin jikinki ba yanzu ya tambayeta yana murmushi. Kanta a kasa tace naji...yace good, lesson one duk dare sai kinyi wanka kafin ki kwanta kinji ko. A hankali tace to. Wayarsa ya kunna yace to sai da safe ya fita ya bar mata fitilar.
Gado ta haye tayi addu'o'in kwanciya sai dai baccin yaki zuwa. Duk abinda Hamza yayi mata tun shigowarsa ta rinka tunawa tana murmushi......
[9/26, 12:32 AM] +234 803 244 1205: AL'ADUN WASU 45

Batul Mamman(Mrs)

Amma yarinyar nan bata da hankali. Rai a bace ya tashi ya zaki min haka? Don me bakiyi shawara dani ba kika fadawa maigadi kamar zamansa kike yi? Ni gidana babu aljanu. Dariya take kasa kasa, daga abin arziki sai kayi min fada. A take ta kwabe fuska tana shirin yin kuka....sau biyu suka ci min abinci. Wannan wace sabuwar rigimar ce kuma ya fada a zuci. Sannan ya dan rage murya ni kada kiyi min kuka. Kamar yace yi kukan kuwa hawaye ya wanke mata fuska. Sai dai bai sani ba hawayen dariyar da takeyi ne ta wayance kamar kuka take. Rannan sunci min kosai a kitchen sannan a gabanka ma suka ci min tuwo. Subhanallah.....da gaske wai ta zata aljanu ne? Muryarsa da kyar take fita yace ke banda jaraba meye na kirga kosai har kika san anci miki. Kuma ya akayi kika san anci tuwonki a gabana? Zuhra na kukan karya tace ka manta da suka ci tuwon har suka saki cokalin a kasa. Kawar da kansa yayi gefe, ni banji ba bana son sharri. Da dankwalinta ta share idanunta tace kosan zai kai goma wanda suka ci. Hamza bai san lokacin da yace kiji tsoron Allah uku ne zuwa hudu kawai.

Ai kuwa Zuhra ta kyalkyale da dariya sosai. Duk yadda yaso dakewa fuskarsa sai ta bawa mutum dariya. Har yayi hanyar fita ya fadawa maigadi kada a kira malam mai ruqiya sai kawai ya gano tsokanarsa take yi. Ya rufe bakinsa da hannunsa da ya tuna har adadin kosan da yaci ya fada mata. Yana juyowa suka hada ido Zuhra ta kwasa da gudu tayi sama. Binta yayi wato kin mayar dani abokin wasanki ko. Nine aljani me satar abinci.... bata jira ya iso ba ta shige daki ta rufo kofa. Duk yadda taso ta kasa murda key din ta rufe saboda tsoro gashi yana turo kofar. Karfinsu ma ba daya bane sai kawai ya tura kofar.

Hanyar toilet tayi yayi murmushi kina shiga zan rufeki a dakin nan sai kin kwana biyu. Can gefen gado ta tafi babu wurin buya....gabanta na dukan uku uku taga ya biyota. Sai kawai ta zauna a wurin ta boye fuskarta a cikin cinyoyinta. A hankali ya tako yazo gabanta yana murmushi sannan shima ya zauna suna fuskantar juna. Zaman nasu yayi kusa da yawa saboda wurin yayi musu kadan. Da wata irin murya mai dadi yace dago kanki. Sake tura kan tayi cikin cinyoyinta zuciyarta na bugawa da karfi. Bata ankara ba taji yasa hannu biyu ya daga kan nata. Babu inda baya rawa a jikinta don tsoro...shi kuwa wani irin yanayi na daban ya tsinci kansa. Kukan gaske yaga tana yi sai ya soma dariya har sai da tayi mamaki. Yayi ajiyar zuciya, kin iya tsokana amma kina tsoron hukunci ko. Shiru tayi yau babu rashin kunya su kadai a gida. Duk laifinki ne baki taba yimin tayin abinci ba, baki damu da inda mijinki yake samun abinda zaici ba. Kunnenta yaji da kyau kuwa? Miji fa yace. Bata iya kallonsa ba tace kai kace na rinka dafa na iya cikina. Kuma itama kafin ta tafi tace kada nayi girki da kai. Hannunta ya kama suka tashi muje na hukunta ki. Sake yin alamar kuka tayi yace kinga ni na dena yarda da kukan naki na karya.

Plates din ya dauka yace babu ruwa ne ko juice. Akwai ta amsa da mamakin me zaiyi. Ki dauko ki hado da wani spoon din. Falonsa ya shige da abincin. Sai a lokacin tayi ajiyar zuciya....wai amma ta tsorata. A tray ta dora jug cike da zobo mai sanyi da cup da kuma spoon din da yace ta dauko. Samunsa tayi a falonsa yana zaune a kasa yana cin abincin. Murmushin da tayi yayi masa kyau yace na dena satar abincin a bayan idonki. Gabansa ya nuna mata zauna muci.

Dawa??? Ta kwalalo idanu tana kallonsa. Tashi yayi ya zaunar da ita. Punishment dinki kenan na tsokanata kici abinci tare dani. Idan baki ci ba kuma nayi bakinki zan dalle. Don Allah kayi....hannu ya daga mata. Kada ki bata bakinki ki bani hakuri. Daga yau har Izzy ta dawo zaki rinka yin abinci dani. Tace to amma ni bazanci da kai ba. Harara ya sakar mata. Don ma kin samu Hamza zaici abinci plate daya dake...kuma wallahi bana son kazanta. Idan zakiyi na dare zan zo inspection naga yadda kike girkin don nasan halinki.

Ba yadda ta iya dole ta zauna suka ci. Sai dai bata iya sakin jiki ba don da ta diba zaice lomarta tayi girma ko kuma tayi kadan. Haka yayi ta mata har suka gama ta kwashe komai ya wanke. Zobon kuwa bayan ya shanye cewa yayi ta hada masa wani...zobo ma yana cikin abinba Izzy bata masa. Shima na masu karamin karfi ne.

Da daddare tuwon semovita yace tayi da duk miyar da ta ga dama. Su Hamza an sami sake Izzy bata nan. Miyar kuka ta kada taji wake da nama. Bai iya boye mata santinsa ba. Sai da ta gyara kitchen din tsaf ta tafi dakinta.

Wurin shadaya da rabi tana kallo aka dauke wuta. wayarta tayi saurin janyowa daga jikin chaja sai taga ashe bata yi chajin ba. Chajar bata shiga jikin socket din da kyau ba, ga wayar dama bata rikon chaji yanzu. A take ta fara jin tsoro ga zafi. Da bin bango ta janyo bargo daga gadonta da pillow tayi shimfida a gefen kofa. Bata son duhu ko kadan shiyasa take kwana da fitila a kunne ko ta kunna torch light din wayarta.

Hamza na fesa bodyspray ya fito daga wanka aka dauke wuta. Wurin minti biyar baiji maigadi ya tayar da inji ba sai ya sauka. Maigadi yayi yayi injin yaki karbar wuta kuma akwai mai a ciki. Dama irin babban nan ne da yake daukar har AC da fridge. Sunyi iya kokarinsu abu yaci tura Hamza ya kira mutumin dake masa gyara yace ko zaizo da safe. Mutumin yace yana kauyensu yaje karbar kudin auren kanwarsa amma jibi zai dawo. Hakan baiyiwa Hamza dadi ba ya yanke shawarar neman wani washegari domin zafin gari sai ya hana mutum bacci. Dakinsa ya koma sai ya tuna da Zuhra yace bari ya doba ko tayi bacci.

Tsoro yasa Zuhra ta dukunkune kanta cikin bargo duk zafin da akeyi. A hankali ya bude kofar dakin gudun kada ya tasheta idan baccin take yi.

Dishi dishi take ganin inuwar mutum da yayi hanyar gadonta. A ranta tace shikenan barawo ya fado dakinta. Tashi tayi da sauri zata gudu ko da bin bango ne taje dakin Hamza taji anyi saurin rungumota ta baya. Sandarewa tayi a wurin don tsoro kamar ta saki futsari, gumi ya rinka tsatstsafo mata. Hamza bai ankara ba yaji ta kai masa naushi a ciki ta soma ihu...Wayyo Allah barawo. Duk da zafin cikin bakinta ya samu ya toshe da hannunsa ai kuwa ta gantsara masa cizo iya karfinta.
[9/26, 8:58 AM] +234 815 728 4163: AL'ADUN WASU 47

Batul Mamman(Mrs)

Zuhra na idar da sallar asuba ta sauka zuwa kitchen. A zafin nan da rashin wuta tana tsoron kada naman cikin fridge din ya lalace. Fito dashi tayi tana wankewa Hamza ya dawo daga masallaci ya sameta. To acici me kike yi a kitchen da asubar fari. Muryarsa taji kamar hancinsa a toshe yake. Amma yau gabadaya kunyarsa take ji da ladabin musamman ta gaisheshi. Sannan tace nama zan tafasa na soya kada ya lalace saboda babu wuta. Ta sunkuyar da kanta, ya jiki naji kamar yau murar tafi ta jiya. Hamza yace eh amma da sauki. Yaji dadin yadda har ta fuskanci bashi da lafiya ta nuna damuwarta. Kallonta yake yadda take aiki ga hijab dan madaidaici a jikinta, hakan bai hanashi tuno surarta da ya gani ba daren jiya duk da duhun dakin. Ji tayi kamar ana kallonta ta dan juya suka hada ido. Murmushi kawai yayi mata ya tafi.

Flask ta dauko sabo na tea ta wanke sannan ta tafasa ruwan zafi da lipton, citta da kaninfari. Ta soya kwai guda uku da albasa yar kadan saboda bata sani ba ko Hamza na son kwai da albasa. A karamin plate ta zuba ta rufe shi da wani irinsa sannan ta dora mug na shan tea da teaspoon a tray. Bread daya ta bawa maigadi ya siyo musu jiya gashi bata da dankali ko doya. Duka bread din ta dora masa da kayan tea. Kasa shiga falon nasa tayi tana tunanin ko tayi masa karambani ne.
Chapter 29 · 0% Book details