← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 67

Sashe 55

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shafa lebenta da yake kyallin lip gloss da ta saka mai kyau...so nake ki soni har abada kuma kada ki taba rabuwa dani.

Maganarsa tasa jikinta yayi sanyi saboda ta lura kamar yana cikin damuwa. A hankali tace Ya Hamza har a aljanna ni matarka ce in sha Allah. Amma nan...ta nuna lebenta...kai dashi sai jibi. Tana magana tana masa dariya. A hankali ya rinka sakewa. Dama bacin ran abinda Izzy tayi masa ne.

Cutie nayi nasarar cin wannan jarabawar har ana bukatar ganina a Abuja. Da murna Zuhra ta rungumeshi tana cewa Alhamdulillah. Can sai ta sake shi ta durkusa tayi sujjadar godiya ga Allah SWT. Tayi kusan minti biyu tana hamdala da takbir. Ko da ta dago kanta wasu zafafan hawaye ne suka sauko daga idanun Hamza. Kullum Zuhra daban yake ganinta.

A tsorace ta tashi yana daga zaune ta rungumeshi a kirjinta. Murya a raunane tace Ya Hamza me yasa ka hawaye?

Muryarsa a can kasa yace Cutie ina sonki. Ina sonki. Ina sonki. Kuma nagode miki for being who you are.

Sake kankameshi tayi tace nima ina sonka Ya Hamza. Uhmm sai dai dan turancin nan na karshe kace who you are ko.. Toh, I am Fatima Bashir.

Mai Hamza zaiyi in ba dariya ba. Zuhra tayi kicin kicin da fuska ita tayi fushi. Hamza ya rike habarta haba my darling Zuhra? Kada kiyi fushi dani. In sha Allah idan komai ya daidaita na wannan course din da za'a turani zamu fara English lessons dake. Dole na ware lokaci na koya miki da kaina.

Zuhra ta turo baki ni bazan koya ba kuma ka tashi ka koma dakinka ni munyi fada. Cakulculi Hamza ya rinka yi mata har ta soma dariya sannan ya fita zuciyarsa fari kal.

Washegari da safe ya sami cikakken bayani game da zuwansa Abuja. Da yake abin na gwamnatin tarayya ne kuma da izininsu kwana biyu aka ce zasu yi a tantance su. Babu wani zancen masauki alamun kowa yayi ta kansa kenan. Harda dariyar mugunta ya fadawa Izzatu basu da masauki saboda haka bazai tafi da ita ba. Kila yaje gidan abokinsa ya kwana. Itama dariyar tayi tace ta riga ta sanar da iyayenta batun zuwansu har an gyara musu wurin kwana a gidansu. Baiji dadin wannan karambanin ba shiyasa yace mata baza shi ba. Ko minti ashirin basuyi da maganar ba Alh Sunusi mahaifin Izzatu ya kirashi da kansa yace lallai yazo gidan anyi masa masauki ko da shi kadai ne. To ta yaya zaije gidan shi kadai dole ya tafi da Izzatu. A haka suka rabu yayi shirin tafiya office.

Da rana da ya dawo a kitchen yaji motsin Zuhra. Yana shiga ya tarar da ita tana rabon abinci a cikin irin abin take away dinnan. Jallop din shinkafa tayi sai kwai da ta dafa ta yanka shi bibbiyu take sakawa a abincin. Hamza ya dan dauki lokaci yana kallonta bata kula ba saboda ta juyawa kofa baya. A hankali yaje ya rufe mata ido tayi murmushi tace Ya Hamza ka dawo?

Cikin wasa ya bata rai, ya akayi kika gane nine?

Tace da kamshin turarenka mana.

Jera abincin yaga tana yi a wasu manyan robobi yace abincin meye wannan Cutie?

Ta dan kalle shi tayi murmushi...ni banso ka dawo ka tarar ban gama ba. Abincin sadaka ne zan bawa maigadi yace akwai makarantar allo a nan baya. Nayi da niyyar Allah Ya baka sa'a kuma Yasa kayi karatun ka gama lafiya. Tana kaiwa nan idonta ya ciko da kwalla, tunanin rabuwarsu da Hamza na wata biyu ke damunta. Shi kuwa kasa magana yayi kamar kodayaushe idan tayi wani abin da yafi karfin tunaninsa. Har abincin sadaka take yi wanda yasan akan yi lokaci lokaci a gidan iyayensa. A take yayi wa kansa alkawari indai ya sami sarari da yardar Allah Hajji zai kai Zuhransa. A duniya dai shine kawai abinda zaiyi mata na karshen jindadi a matsayinta na musulma. Amma a nan kanta ya dafa ya rinka saka mata albarka. Sonta kuwa kullum karuwa yake a zuciyarsa saboda kyawun halayenta.

Kwanaki biyu a tsakani su shirya tafiya Abuja. Izzatu sai rawar kafa take kamar farin shiga a zuwa Abuja. A motar Hamza suka tafi da aka gyaro. Zuhra tasha kukanta a daki Hamza na rarrashi sannan ta fito ta rakasu.

Kwanansu uku suka dawo aka fara shirye shiryen tafiyar Hamza zuwa kasar South Korea. Kwanaki uku suka rage ya tafi idan kaga Zuhra duk tayi wani iri. Har rama ta danyi saboda zulumin tafiyar Ya Hamza. Dambun nama ta roki Umma tayi mata saboda ita idan tayi duk sai rabi ya kone. Ai kuwa Umma tayi mai dadi musamman da tasan na tafiyar Hamza ne. Da aka kawo yayi ta murna.

Izzatu ma a nata bangaren cake tayi masa kanana mai dadi ta jera a wata roba sannan ta liketa saboda kada ya bushe. Itama Hamza yayi mata godiya.

Da asuba ana saura kwana biyu ya tafi kuma ranar Zuhra zata fita girki. Tunda ta idar da sallah take masa kuka. Duk abinda zaiyi mata tayi shiru yayi amma minti kadan sai ta cigaba. Ya zuba mata ido kawai yana kallonta.

Cutie wai kukan nan na meye? Ba fa yau zan tafi ba.

Ta dago jajayen idanunta...to meye maraba Ya Hamza daga yau kai da ka sake kwana...sai tayi shiru kanta a kasa

Ya share mata hawaye kina tunanin zanyi wata biyu bamy hada shimfida ba ko? Gashi ke kuma kina son kwanciya a jikin mijinki.

Rufe ido tayi a kunyace...ni ba haka nake nufi ba.

Hamza yayi dariya yace ai ba sai kin fada ba na sani. Addua kawai nake bukata daga gareki. Kinga jiya munfi awa daya ina nuna miki yadda ake whatsap saboda haka zamuyi ta hira kullum kinji ko. Idan kika yi kwalliya kullum ki turo min hotonki na gani.

Ta gyada kai wani hawayen na taruwa a idonta...Ya Hamza yau kada kaje ko'ina har sai lokacin da zan fita girki. Don Allah ka zauna dani.

Hannunta ya kama ya tasheta daga kan gadon. Muje har breakfast tare yau zamuyi.

Manne jikin juna suka sauko saboda asabar ce su Khalifa basu da makaranta. Sai karfe goma zasu je islamiyyar safe.

Kayan kwabin fanke Zuhra ta debo ta fara kwabawa. Hamza taji ya tsaya a bayanta ya zira hannu a robar da take kwabin yana wasa da hannunta sannan yana bin wuyanta yana kissing. Gabadaya aikin gagararta yayi cikin kankanuwar murya tace Ya Hamza don Allah ka bari na gama. Koma can gefen ka tsaya.

Yi yayi kamar yayi fushi yace ba ke kika ce kada na barki ba yau. Ni babu inda zani ya fada yana sake rumgumarta ta baya. Muryar Junior ce tasa ya saketa ba shiri da ya shigo kitchen din yana murza ido.

Maama fanken zaki yi min don Allah?

Zuhra tayi murmushi tace kaga har na gama kwabawa sai mu dan jira ya tashi ko.

Rungumeta yayi daidai kafarta yace Maama kinfi sona akan Daddy shiyasa kike dafa abinda nake so.. nima idan na girma ke zan fara siyawa mota da jirgi kafin Mummy da Daddy.

Hamza ya bude baki
yana kallonsa. Lallai yaran zamani kun iya sa ido. Kai yanzu har kasan so? Ya fada yana daga Junior sama suna dariya.

***********

Wannan shafin naki ne Maman twins. Gaisuwarki ta riskeni ina fata nima tawa ta iso gareki. Godiya mai tarin yawa tare da fatan alkhairi. Allah Ya albarkaci zuria. AL'ADUN WASU 73

Batul Mamman(Mrs)

Jirginsu Hamza shabiyu da rabi na dare zai tashi shiyasa ya yanke shawarar barin gidan karfe goma domin ya sami damar zuwa gidan iyayensa yayi musu sallama.

Sai da ya dawo daga masallaci bayan sallar isha sannan yaci abinci kadan yaje yayi wanka. Gidan duk yayi wani iri saboda kowa na tunanin tafiyar Hamza. Ya shirya cikin kananan kaya yayi kyau sannan ya dauki rigar sanyi a hannu saboda banda sanyin jirgi ya bincika ana sanyi sosai a South Korea. Ya gama shirinsa tsaf suka sake wata sallamar da Izzatu sannan ya fito zaije dakin Zuhra. Gabansa Izzatu tayi saurin tarewa ta daure fuska....Baby ina zaka je kuma?

Shima tasa fuskar a daure saboda bata masa lokaci da yake ganin zata yi yace zanje sallama da Zuhra mana.

Yana soma tafiya ta rike masa hannu....bafa zan yarda ba. Yau girkina ne saboda haka bai kamata kace zaka wata sallama da Zuhra ba. Ba tare zamu airport din ba? Sai kuyi sallamar a can.

Dan rufe idonsa yayi sannan ya bude a hankali....Izzy kada kisa mu rabu da bacin ran juna. Zanyi tafiyar wata biyu har zancen wani girki zai taso? Kije ki fito min da jakar kayana, idan bazaki iya ba ki jirani a kasa ina fitowa zamu tafi.

Bai kara saurararta ba ya tafi dakin Zuhra. Zaune ya ganta akan kujera tana sharar hawaye. Ta gama shiryawa ta saka wani katon hijab tana jira Hamza ya fito su tafi. Tana ganin ya shigo tayi saurin goge hawayenta ta mike tsaye...Ya Hamza har ka fito?

Murmushi yake yi yana kallonta. Na fito Cutie, wato baki dena kukan ba ko?

Kamar yace yi wani kukan ta soma wani sabo. Ya dauki lokaci yana bata hakuri da rarrashi duk ta hanyar da yasan zai dauke mata hankali. Da kyar tayi shiru tana fada masa irin yadda zata yi kewarsa idan ya tafi. Wayarsa ya dauko yana daukarta hoto tana ta rufe fuska wai bata yi kyau ba.

Yace gara na dauki fuskar a haka nasan cewa idan na tafi kullum zaki tuna dani kamar yadda zan tuna dake.

Jin haka yasa ta dauke shi itama sannan suka yi wani tare. Suna cikin haka suka ji wani mahaukacin bugun kofa. Yasan aikin Izzatu ne dama yana sane ya kulle kofar dakin don ba karamin aikinta bane ta bude su. Sai da ya sake yiwa Zuhra kyakkyawar sallama sannan suka fito tare fuskokinsu dauke da murmushin da ya kona ran Izzatu.
Chapter 55 · 0% Book details