← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 67

Sashe 50

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin azahar ta gama komai na abincinta ta hada salad da kunun aya yasha kankara. Su Junior duniya sabuwa sunji dadin abinci sai karawa suke yi. Bayan sun gama ta shiryasu saboda Hamza yace tare dasu zasu je asibitin.

Sai da yayi sallah ya gama nuko nukonsa sannan ya fito suka tafi. Duk motsin Zuhra akan idonsa jin kansa yake kamar sabon shiga a aure saboda irin son da yake yi mata. Makarantun da suka bada aikin saka suka fara zuwa ya kai musu duk suka biya suna yaba kyan aikin da saurin da akayi aka gama. Sai gashi ya tashi da dubu dari uku da arba'in da hudu kudin da duka makarantun suka biya. A mota ya rinka yiwa Zuhra addua yasa su Nana suce Amin. Bakinta kamar gonar auduga don farinciki saboda yadda taga Hamza yayi murna. Har cewa yayi washegari zai karbo mata form ta cike zai bude mata account. Dubu dari biyu da hamsin zai saka mata a cikin kudin sauran suyi amfani dashi a gida. Tun a wurin tace bata yarda ba yace to abar magabar sai sun koma gida.

*****
Duk magiyar da Raliya tayiwa Izzatu sam taki yarda taci abincin da aka kawo daga gidansu Hamza da kuma na gidan Anti Larai tace tana jiran Hamza tasan duk tsiya bazai barta da yunwa ba. Anti Larai dai ko kulata bata yi ba dama ba shiri take yi da Izzatu ba. Tun su Hajiya na asibitin ake cewa taci taki cin komai har suka tafi. Raliya tace ke yanzu banda baki da kunya yaushe zaki jira Hamza mutumin da kika batawa rai. Kina kallo yau tun safe bai zo ba shi da yana kai yara makaranta yake tahowa. Izzatu dai ta kafe bazata ci abincin ba dole Raliya ta kyaleta.

Sai wurin karfe uku suka iso asibitin. Su Khalifa ne suka fara shiga dakin da gudu Hamza da Zuhra na bayansu. Shi ya dauko kwandon abincin ma sannan suka shiga dakin yana rike da hannunta yana tsokanarta tana dariya.

Kiris ya rage Izzatu ta hadiyi zuciya sai dai ta hakura. Tunda yazo tasan baya iya dogon fushi da ita. Wannan 'yar banzar yarinyar kuwa sai tayi maganinta.

Zuhra da Hamza suka gaisa da Raliya sannan Zuhra tayiwa Izzatu ya jiki. Kamar tayi magana da dutse haka ta shareta. Khalifa yace Mummy baki ji Maama tana yi miki ya jiki ba? Izzatu ta dan matse banji ba Khalifana. Junior ya dora hannuwansa biyu a baki yace Daddy kaji Mummy tayi karya ko? To mai karya dai dan wuta. Mu duka a dakinnan munji sai ke kadai. Hmmm, Maama fadawa Mummy idan jirgin aljannah yazo a nan zamu barta. Hamza ya kwashe da dariyar mugunta yace haka ne Junior Allah Ya shiryi masu karya. Yara suka ce amin. Ran Izzatu ya gama baci tace zuwa kayi ku wulakantani kai da matarka? Shine zaku saka 'ya'yana ma su tsaneni ko. Zuhra ce tayi karfin halin bata hakuri, shi kuwa Hamza dariya ya sake yi ya cigaba da wasa da yaransa.

Raliya ta bude abincin zata zubawa Izzatu. Tana daga kan gado amma idanunta na ga abinda mamanta ke yi. Kamar tayi kuka tace Mum me nake gani kamar wake da shinkafa. Raliya tace shine kinji kamshin kayan salad ko? Tana bude man Izzatu ta sa ihu, Mum manja ne fa. Raliya tace to sai me kike yamutsa fuska kamar kinga abin kyama.

A raunane Izzatu ta kalli Hamza,Baby wane irin abinci ne wannan kuka kawo min? Yace irin abincin da muke ci ni da iyalina. Sai nanatawa take yi a ranta wake da shinkafa. Basu taba yi ba tunda suka yi aure. Kamar tayi kuka tace ko dai ka sami karayar arziki ne, shi kadai ne dalilin da zaisa a fara cin irin wannan a gidanka. Junior ya dubi abincin da Raliya ta gama hadawa yayi kyau yace Mum ki bani inci, Maama ta iya girki.

Izzatu tace haba ko da naji,ashe Zuhra ce ta dafa. Kaga irin abinda nake fada maka ko. Yarinyar nan bazata ta taba wayewa ba. Kamar kai Baby aci wake da shinkafa a gidanka sai kace wani talaka. Jikin Zuhra duk yayi sanyi.

Hamza yace Cutie ga key ku tafi mota da yaran ina zuwa. Tana fita ya zauna a gaban Izzatu ya warware mata halin da yake ciki da irin gudummawar da ta bayar wurin fadawarsa wanda yasa ta mugun mamaki. Ya mike tsaye...saboda haka Izzy ki kiyayeni domin ko banyi aure ba ina gab da sakinki wallahi saboda kin jefani cikin tashin hankali sannan dayake kinfi amara son biki kika tsallake kika barni. Izzatu tace don ka sami matsala sai kayi min sharri? A take ya tuna mata duk abubuwan da tayi wadanda sukayi sanadiyarsa fadawa wannan halin. Baki bude haka ya fita ya bar Izzatu da Raliya don ma bai fada musu yadda Zuhra ta taimaka masa ba. AL'ADUN WASU 69

Batul Mamman(Mrs)

Daga asibitin gidan 'yan uwansa mata suka wuce. Dukkaninsu sunyi farincikin ganin Zuhra kowacce tana janta a jiki. Daga nan suka je gidan Anti Faiza wadda ta rasa inda zata sa kanta don murnar ganin Zuhra da Hamza tare. Dabarun kula da miji ta sake karanta mata da kyau sannan na karshe suka je gidan Ibrahim. A nan suka ci abincin dare sannan suka taho bayan Hamza da Ibrahim sun dawo daga sallar isha.

Kafin suje gida su Khalifa duk sunyi bacci sai Hamza da Zuhra ke ta hira. Kayan da suka biya suka siyo Zuhra ta iya dauka yaran kuwa Hamza ne ya dauko su. Dama sauri take su iso gida gabadaya bata jindadin jikinta tun yamma daurewa kawai take yi tana tafiya.

A dakinsu ya kwantar dasu Zuhra ta fadawa Tala taje ta kwana dasu sannan ta hau sama. Tana tafiya Hamza na binta da ido, jan kafa kawai takeyi tana tafiya da kyar. Tun yamma ya kula da yadda tafiyarta ta canja amma idan taga mutane sai ta daure ta rinka tafiya daidai tana bata rai. Girgiza kai yayi saboda yasan meye matsalarta.

A dakinta ya sameta tana daura tawul zata yi wanka yace ta jira shi yana zuwa. Turo baki tayi ...Ya Hamza don Allah kada kace zaka yi min wanka yau ni bama ni da lafiya. Yace to Allah Ya sauwake, maganin ciwon naki zan baki. Idonta har ya fara kwalla tace kasan me ya sameni ne? Cike da tausayawa yace na sani Cutie, bari ki gani ina zuwa.

Toilet dinta ya shiga ya tara ruwa mai zafi sosai a katuwar roba ya sirka shi kadan sannan ya fito ya cire rigarsa ya bar singlet yace muje. Duk ta gama tsorata ta fara ja da baya. Bai tsaya sauraronta ba ya dagata tanata dukansa. Tawul din kawai ya zare ya sakata a cikin ruwan zafin. Ihun da tayi yana tsammanin har maigadi sai yaji domin ba wutar inji bace bare ya rage sautin karar.

Zuhra kuka take yi sosai tana kokarin tashi Hamza ya tsaya daga bayanta ya danna kafadunta. Ya Hamza akwai zafi sosai.

Na sani kiyi hakuri, son jiki irin naki yasa baki shiga ruwan zafin tun da safe ba. Yayi 'yar dariya... Yau duk mai hankali kin gama tona min asiri a wurinsa da wannan tafiyar taki.

Sharkaf haka fuskarta ta jike da hawaye tace na shiga ruwan zafin da asuba.

Hannuwanta ya rike da take neman tashi tsaye yace nasan kin shiga ruwan da kika gama sirkawa ba. Wannan idan kika haihu da kaina zan miki wankan jego don kada ki cuce ni.

Muryarta har ta soma dashewa tace cuta har ta wuce gasa ni da kake yi. Ta kai masa cizo a kirji ya kauce yana dariya. Zumbura baki tayi kuma na dena sonka.

Yana dariya yace babu komai Cutie son da nake miki ya ishemu ai.

Bata kula ba ya sake kara ruwan zafin saboda na robar ya fara hucewa. Kuka kala kala Hamza ya gani. Da kyar take magana don bakin ya mutu. A hankali tace to ka dawo ta gabana na rungumeka naji dadi.

Yadda tayi ya bashi tausayi amma yasan abinda yayi mata zaisa taji dadin jikinta. Zagayowa yayi ta rungumeshi tana kuka yana shafa bayanta. Bai kyaleta ba sai da tayi kusan minti talatin a cikin ruwan zafin sannan kamar jiya yayi mata wanka. Sai da ya shiryata sannan ya shiga wankan shima. Kafin ya fito tayi baccin wahala. Gyara mata kwanciya yayi ya rumgumeta cike da tausayawa. A haka suka yi bacci tana kwance a jikinsa.

Yau dai bata ji kunyar tashi da asuba ba har Hamza na tsokanarta. Da wuri ta kammala ayyukanta na gida saboda jiki yayi kwari ta dena tafiya da kyar. Da tayi zancen zuwa asibiti Hamza yace bazashi ba office zai tafi. Itama baiyi mata izinin taje ba. Ganin ya dauki zafi yasa bata matsa masa ba. Bata damuwa da bin kwaf akan matsalarsa da Izzatu. Tare ta gansu tasan idan fushin ya kare zasu daidaita. Kullum Tala ke kai abincin asibitin.

Cikin 'yan kwanakin nan Zuhra da Hamza sun kara shakuwa sosai. Soyayya yake nuna mata tamkar wata 'yar yarinya haka yake lallabata. Itama dai ta fara sakewa dashi amma har yanzu tana jin kunyarsa. Ko kayan bacci tasa sai yayi da gaske yake cire mata hijab. Ana tashi daga office gida yake tahowa su sha soyayyarsu. Ana haka Hajiya ta kirashi tana masa fadan kwana biyu bata ganinsa a asibiti meye dalili. Dama yasan ba son Izzatu suke yi ba, idan ya fadi abinda tayi kuma kara wutar abin zaiyi sai kawai ya bata hakuri yace ayyuka ne suka saka shi a gaba.
Chapter 50 · 0% Book details