← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 67

Sashe 1

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[9/25, 2:37 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU🗿1

Batul Mamman(Mrs)💖

Bismillahir Rahmanir Rahim

Mal Bashir dattijo mai kimamin shekaru hamsin da takwas na shigowa cikin layinsu yara suka fara binsa suna oyoyo Baban yara. Da yake kullum haka suke masa shiyasa baya rabo da yar tsarabar da zai kawo musu. Hannunsa daya yasa a aljihu wanda daga tsintsiyar hannun a yanke yake ba yatsu sakamakon zarton da ya fada kai har ya tsinka masa jijiyoyin hannu. ya sha wahala sosai likitoci suka ce hannun ya mutu dole a yanke shi. Duk da haka bai dena zuwa wurin sanaarsa ba ta kafinta. Da dungulmin hannun ya bude aljihunsa ya saka mai lafiyan ya zaro carbin malam ya mikawa yaran. Suna ta murna suka tafi su raba. Yayi gaba yana dan murmushin suka hada ido da wani matashi a layin. Da sauri ya taba na kusa dashi kai don ubanka kashe ga Baban yara nan. Tare suka tashi suna karkade jikinsu. Baban yara barka da yamma suka fada da ya karaso kusa dasu. Ya dan bata rai bazan amsa ba Sani. Yanzu don Allah baza kuyiwa kanku fada ba da shaye shayen nan? Ya kalli katon ciki Anas so kake ciwon babanka ya sake tashi saboda kai ko? Wanda aka kira Anas ya girgiza kai. Kayi hakuri in Allah Ya yarda bazamu sake ba. Yayi murmushin takaici Allah Ya bada ikon denawa. Kuna ta batawa kanku rayuwa a banza. Idan baku sani ba abinda mutum yayi da kuruciya yakan bishi har girma. Na tabbatar babu wanda zai so nan gaba a bawa dansa labarin ya taba busa wiwi a tarihin rayuwarsa. Sani ya dan yi murmushin jin abinda ya fada. Baban Yara ya ce au dariya na baka ko? Ya kama bakin ya murde. Muna nan da ku idan baku dena ba wata rana kwata zaku shiga ku kwanta kuce gado ne. Yayi gaba abinsa yana ta mitar halin da yara ke saka kansu a yanzu.

A kantin kofar gidansa ya tsaya suka gaisa Munkaila mai shago. Mal Bashir ya dauko naira dari ya mika masa. Gashi nagode sosai. Munkaila ya karba na meye kuma wannan Baban Yara? Darin da ka bawa Zuhra mana da safe. Ina shirin fita ta tambayeni kudi zata je karbo sakamakon jarabawarta. Lokacin bani da chanji shiyasa nace ta karba a wurinka. Munkaila ya mika masa kudin, ai yau ko sau daya banga fitowarta ba. Mal Bashir ya karba ya shiga gidansa da sallama.

Zuhra na yanka yakuwa taji muryar Babanta a soro. Hantar cikinta ce ta kada sosai ta tashi da gudu ta shiga bandaki. Garin sauri ta zubar da yakuwar da take yankawa. Ummanta ta soma fada ke lafiyarki kuwa. Mal Bashir ya karasa shigowa tsakar gidan. Ina ta sallama babu mai amsawa kamar babu kowa a gidan. Atine Umman Zuhra ta ce yi hakuri Baban Zuhra. Wallahi bari tayi min nake fada banji sallamar ba. Takalmansa ya cire ya zauna kan tabarmar dake shimfide a tsakar gidan. Fitsari ta bari ya matseta shine take wannan gudun ko. Umma tace anya kuwa? Hira mukeyi fa kana yin sallama ta tashi kamar wadda ta ga abin tsoro. Baban yara na jin haka yasha jinin jikinsa. Yace da Umma ta karbo sakamakon jarabawarta kuwa?Umma tana kwashe yakuwarta ta ce bana jin amma ga wasu takardu can akan taga wanda Hajara ta kawo mata dazu. Mal Bashir ya tashi ya dauko a sanyaye...ai tunda ta gudu yasan bana ma bata kitsa abin arziki a makaranta ba.

Ai kuwa yana budewa yaga abin haushin da yasa rai da gani. Ta 48 tayi cikin su 52. Ransa ne ya sosu. Ya rasa yadda zaiyi da yarinyar nan. A fusace ya tashi ya tafi kofar bandakin. Zuhra me kike yi ne ya tambaya da daga murya. Daga ciki ta ce ehem ehem! Ya sake bugawa idan ba so kike na bude ki ba gara ki fito tun wuri. Zuhra ta gwammace ta yini a bandaki da ta fito ta sha fadan Baba. Ta sake cewa ehem..... ya ce bari na fita tunda mun koma wasan buya da ke. Sai da ta kara kusan minti biyar sannan ta fito duk ta hada gumi. Ta dubi Ummanta, wai yau da Baba ya kamani bansan....saukar rankwashi taji a tsakar kanta ta durkushe a kasa tare da rike kan ta soma kuka.
[9/25, 2:38 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU🗿2

Batul Mamman(Mrs)💖

Baban Yara yace idan baki rufe min baki ba sai na kara miki. Da kuka Zuhra ta mike tsaye tana turo baki ko saboda rankwashin nan ba dole na kasa kokari ba. Idan kana taba min mandula oblongata dina haukacewa zanyi nan gaba kadan. Baban Yara yace kece mandular ai. Nan kika fi kauri dama. Kin iya haddace 'yan kalmonin turanci kizo kina barazana dasu kamar wata wadda tasan abinda take yi. Zuhra dai kuka ta cigaba da yi har sai da Umma tayi mata tsawa. Wallahi idan kika tara min makota yau jikinki sai yayi tsami. Jin haka ta soma tsalle tana kara kukan. Baban Yara yace bari na dauko wayar chaja na yi miki mai dalili. Ai kamar anyi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan.

Takardun jarabawarta da aka hada da report card din ya soma dubawa. Wasu har zero ta ci. Maths(lissafi) tace arbain da takwas, Arabic tace casa'in da hudu sai Hausa ta taci sabain da daya. Dama sune darrusan da suke dan taimakawa bata daukar ta karshe gaba daya. Sai ko rubutu da ta iya mai kyau idan ka gani zaka dauka na wata mai kokarin ne. Yana dubawa yana tsaki sai daga baya ya kula da yadda take rubuta suna. Kansa ya rinka girgizawa kawai don takaici. Ko shi da iyakarsa aji hudu a secondary ga shekaru sun mika amma yasan idan suka shiga aji shi da yar tasa sai yafi ta kokari. Zo nan ya yi mata tsawa. A hankali ta ja kafa ta je ta tsugunna a can gefe. Yanzu kin tabbatar duka takardun nan naki ne? Nawa ne Baba duba sunan da rubutun mana. Yace ai na duba. Wasu ki rubuta Zuhra Bashir wasu kuma Fatima Bashir don tsabar rainawa malamai hankali. Yana cigaba da dubawa yayi karo da wata. Takalminsa ya raruma ya kwada mata. Ya daga takardar yana nunawa Umma. Kinga wulakancin yar nan wai Fatima Basiru. Ya nuna kansa nine BASIRUN??? yadda yayi yasa ta soma dariya Umma tace Allah Zuhra zanci mutumcinki. Ana miki fada kina wa mutane dariya don shakiyanci. Zuhra ta kara matsawa gefe tana sharar hawaye to ba haka naji su Kawu Sabiu da Innar Ajingi suna kiranka ba. Baba ya cije lebe saboda takaici. Da kika ji sun fada ba sunan gida bane?. A nan wa kika taba ji ya kirani Basiru? Tace to yi hakuri wallahi daga yau na dena. Ki ma kara ya fada yana tattare takardun. Yana yi yana mita. Yarinya sau nawa ana miki repeating gashi kin kusa shekara ashirin. Amma kanki kamar kifi, nasan duk ajin kece mamansu ko. A'a Baba ga Hajara, ka manta ajinmu daya. Yace ina fa zan manta...an tara dakikai biyu a aji daya. Baku da aiki sai cin awara da wainar flawa. Zuhra da baki baya shiru tace to ba kai kake bani kudin ba. Umma tace kaga ka dena kula yarinyar nan sai jininka ya hau.

Takardun ya miko mata jeki ki ajiye min a dakina. Ni ina ta kokarin hada kudi na biya miki kudin WAEC saboda kada a rufe amma naga kamar asara zanyi. Sau biyu kina qualifying din nan amma kin kasa hada credit uku. Zuhra tasan yadda babanta ya damu tayi karatu amma duk yadda ta dage a cewarta ko kadan bata ganewa. Zama tayi kusa dashi kaga Baba kawai ka kaini makarantar koyon sakar nan. Har na tambayo matar tace a wata biyu zata koya min sau uku a sati zani. Kuma a dubu shida. Ai kaga yafi sauki akan WAEC din. Ta nuna kanta ni da ka ganni bani da abinci a boko. Kan baya dauka yadda kasan an zuba dusa a kwakwalwar haka nake. Shi din ma ya kusa dariya sai ya dan dake. Tashi ki bani wuri ni. Ko damuwa ba kya yi yan ajinku zasu tafi makarantun gaba ke kina son koyon saka. Ta dan tura baki to ya zanyi Baba. Suma fa duk harkar ta koma satar amsa. Idan sakar ma bazata yiwu ba kawai kayi min aure ka huta. Shi da Umma a tare suka yo kanta suna mata fada. Da gudu ta tashi tayi hanyar waje tana dariya tare da jan mayafin Umma a igiya.
[9/25, 2:39 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU🗿3

Batul Mamman(Mrs)💖

Mal Bashir Ibrahim mutumin Ajingi ne ta jihar Kano. Su biyar ne maza a gidansu shine na biyu. Mahaifinsu manomi ne kuma yana kiwon shanu da tumaki. Da farko sun fara karatu har ya kai aji hudu a makarantar gaba da firamare sai babansu ya matsa akan basa samun lokacin taimaka masa a gona. Shi a son ransa duk su hakura da karatun. Ko kadan Bashir baiji dadin hakan ba, sai da ya hakura shi da wansa da mai bi masa suka koma gona. Sauran biyun suka cigaba. Akayi rashin saa autanma ya dena zuwa don shi yafi son kiwo. Wanda ya karasa kuma kan nasa kamar na Zuhra. Ba wani sakamakon kirki ya samu ba. A halin yanzu ma masinja ne a wani company. Mal Bashir ya dawo birni shima aikin kafinta a nan ya hadu da Atine yar kwanar Diso ya aura.sun jima basu sami haihuwa ba gashi yana da son 'ya'ya ,sai daga baya aka haifi Fatima wadda taci sunan mahaifiyar Mal Bashir kuma sunan Atine shiyasa suke kiranta Zuhra.
Chapter 1 · 0% Book details