Sashe 51
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kwanan Izzatu tara a asibitin sannan aka sallameta. Duk irin nasiha tagari Raliya tayi kokarin yi mata domin ta samu ta rike igiyar aurenta dake lilo a iska. Itama ta danyi karatun ta nutsu saboda bata taba tsammanin zai iya shareta haka ko waya babu ba. Tun safe akayi sallamar ta kira shi a waya yana can jikin Zuhra bai bi ta kai ba. Sai daga baya yaga missed call ya kira tace an sallameta ne tun safe. Hamza yace to sai ki tari adaidaita sahu ki taho gida ni motata jiya da kyar ta kawoni gida. Anjima kadan makanike zai zo ya dauka. Kamar ya kwada mata guduma haka taji maganar tasa. Adaidaita sahu kuma??? Ita ba don kada tayi karya ba sai ta iya cewa bata taba shigarsa ba. Motoci uku ne a gidansu kuma duk inda zata indai ba aiki ne yayi masa yawa ba Hamza da kansa yake kaita. Gashi ko zancen motarta da ta bari a Kaduna baya yi. A sanyaye tace Baby ko daga gidanku kasa azo a daukeni mana. Saboda yadda ta bashi haushi ko amsa bai bata ba ya ajiye wayar.
Zuhra na falo tana biyewa yara suna shirmensu Hamza ya fada mata an sallami Izzatu tayi abinci da ita. Tace Mamanta fa? Gidan kanwarta zata wuce, kisa Tala ta gyara mata daki kafin ta karaso. Yana gama magana ya shige falonsa. Sakonsa ta fadawa Tala sannan tabi bayansa dama ta riga tayi girkinta kuma zai isa indai cikin Izzatu ne ita kadai.
Kwance ta same shi akan doguwar kujera ya dafe kansa da hannu daya idonsa a rufe. A hankali ta rinka tafiya har tazo gabansa ta durkusa. Gashinta ta janyo daga cikin dankwali ta matso kusa dashi sosai sannan ta zira masa gashin a kunne tana wasa dashi. Da sauri ya bude ido ya dagota ta fado jikinsa. Kinci bashi Cutie ya fada yana karkade kunnensa. Tayi dariya kai dai kaji tsoro kawai zaka wayance. Hancinsa ya goga a jikin nata yana murmushi...Cutie I love you so much. Ganinki yana sa na manta damuwata. Mayar masa da murmushin tayi tace I love you too. Amma yanzu ka tashi muyi magana kaji. Ba haka yaso ba a yadda ta kwanta a jikinsa so yayi su zauna a haka. Yace idan na tashi kin min alkawarin zan sami duk abinda nake so. A kunyace tayi hada bakinta da nasa tace harma da kari.
Zama ya gyara ya dorata akan cinyarsa. Ina jinki Cutie. Har wani dan gyaran murya tayi sannan tace Ya Hamza nasan bani da wani iko akan duk matsalarka da mamansu Khalifa. To amma abinda yake faruwa yanzu yana iya shafarsu. Idan har iyaye na fushi da juna yara su kan gane idan sun fara wayo. Jiya Khalifa cewa yayi yanzu baka zuwa wurin Mummy dinsu saboda tayi maka laifi. Nayi kokarin yi masa wayo nace kana zuwa. Daga baya yazo yace yanzu nice mamansu ko, ita kuma zata koma Abuja su dena ganinta. Bansan ya akayi yake irin wannan tunanin ba amma ya kamata ka nuna masa ba haka bane. Yanzu yaro ne bazai kawo komai ba, amma nan gaba idan ya kara wayo zai ga kamar baka sonta ne. Daga nan ko kai ko ita zai goyi bayan daya ya bar dayan wanda hakan bai dace ba.
Hamza kallonta kawai yake yi har ta gama bayaninta. Fuskarsa dauke da murmushin jindadi, shi kam yaga ranar biyayya ga iyaye. Iska ta busa masa a ido da taga baya kiftawa. Ya shafa fuskarta, Zuhra ke dabance a mata. Lokacin da ya dace kiyi farinciki hankalin miji ya dawo gareki gabadaya sai kike tunanin kyautatawa wadda tayi sanadiyar jefaki cikin kunci.
Zuhra tayi saurin dora yatsanta a bakinsa...Ya Hamza ni bana cikin kunci. Na aureka ba don ina so ba amma yanzu bana fatan ganin ranar da zamu rabu. Yayi murmushi Allah Cutie? Kice karatun da na koya miki yayi aiki kenan. Kunya taji ta sunkuyar da kai, ni ba haka nake nufi ba. Yayi murmushi ni haka nake nufi. In Sha Allah zanyi kokarin gyarawa kuma. Sai dai sai kinyi min hakuri da kunnenki kika ji abinda tayi. Zuhra tace babu komai indai zaka gyara itama zatayi da yardar Allah. Hamza ya jinjina kai, Cutie fada min gaskiya ke bakya jin haushin duk abinda tayu miki? Zuhra tace tabdi, ya za'ayi naji haushi ta hadani da mijin da babu kamarsa. Tana fadar haka ta tashi ta gudu tana masa dariya.
******
Mai adaidaita sahu ga gaji da ihun da Izzatu take yi ko yaya suka shiga gargada. Dama da ganinsa ko ba'a buge yake ba to yana dan tabawa ya kallota ta mudubi idanunta wuri wuri. Ke Hajiya ya zaki rinka min ihu kamar yau kika fara shiga adaidaita? Izzatu ta kankame karfen gefen da take tana mai nadamar kin bin mamanta a wanda ta tafi...ban taba shiga ba wannan ne shigata ta farko. Dan matashin yayi dariya yace shegiyar karya kice daga turai jirginki ya sauka kawai. Kallon yadda yake kurdawa tsakanin motoci take yi baki na rawa tace wallahi ba karya nake yi ba a Canada na girma. Dreban ya kwashe da dariya yace bari na dan shillaki kiji kamar a jirgin Canadan kike.
Ai bata kara samun nutsuwa ba sai da ya tsaya a bakin gate din gidanta. Gudu yake yi da ita sosai har wani abokinsa na tambayarsa ina zuwa haka da suka tsaya a danja yace yau Canada ya nufa. Izzatu taga tashin hankali duk jikinta ya bugu. Kafarta kamar bazata dauketa ba da suka tsaya a kofar gida.
Maigadi ne ya kwaso mata kayanta ta shiga ciki tana jan kafa. Tana shiga falon idonta ya dire akan Zuhra zaune a kan ledar cin abinci ta dora Nana a cinyarta ga Junior da Khalifa duk sun zagaye tray suna cin abinci. Zuhra ta dago kanta a dan tsorace tace mata sannu da zuwa. Ko bi ta kanta bata yi ba tace where are your table manners kids? Yaushe kuka fara cin abinci a kasa kuma a tray? Khalifa yace zumunci yake karawa. Izzatu ta dakawa Tala tsawa, daukesu ki zubawa kowa plate dinsa su koma dinning table. Tala ta ruga kitchen a ranta tana cewa shikenan mun shiga uku.
Sai a lokacin Izzatu ta karewa abincin kallo tace meye wannan kuke ci a wulakance. Zuhra taji babu dadi. Farar shinkafa ta dafa sannan tayi miyar alaiyahu. Jajjagen attaru da albasa tayi sai tumatir kadan ta soya da manja ta zuba alaiyahu wanda ya tsane ruwansa sannan ta dafa kwai ta sakawa kowa. Tala na zuwa da plate din Hamza ya fito yace ta mayar ko kallon Izzatu baiyi ba ya koma falonsa rai a bace. Zamansa kenan wayarsa tayi kara ya dauka.
Mutumin yace shine sakataren ministan tsara birane. An turowa Hamza sakon email ana bukatar ya karanta ya turo reply kafin gobe. AL'ADUN WASU 70
Batul Mamman(Mrs)
Hamza.
Hamza..
Hamza....
Shigowar Izzatu falon nasa tana kwala masa kira yayi daidai da faduwar wayarsa daga hannunsa saboda yadda kiran nata ya dan razana shi. Ya fuskanci kamar da gayya Izzy ke zuwa a lokacin wani abu mai mahimmanci ta wargaza komai. Sunkuyawa yayi ya dauki wayar ya mayar da batir zai kunna tazo ta tsaya rai a bace. Yanzu Baby don kayi aure shikenan ni ban isa ba a gidan nan? Menene dalilin da zaisa ka hana Tala rabawa yara plates kamar yadda na saka ta?
Hamza ya fasa kunna wayar kada ya bude email din Izzatu tayi abinda zai kasa fahimta ya bayarda amsar da bata dace ba. Sai da ya zauna sannan yace...daga yanzu da kika shigo gidannan zaki ga changes wadanda suka sha bamban da abinda kika saba dasu. Duk wanda baiyi miki ba ki fara magana dani kafin kice zaki gyara shi. Maganar yara na cin abinci a tray nima jiya haka muka yi dasu duka. Once in a while dai family suyi sharing plate yana kara saka shakuwa a tsakaninsu. Yanzu ki taimaka ki tafi daki kiyi wanka ko abinda ranki yake so kafin nazo na sameki. Yana kaiwa nan ya fita ya wuce dakinsa.
Wayarsa ya kunna ya duba email din. Gayyatarsa akeyi zuwa workshop da za'ayi a Lagos na kwana hudu. Daga litinin zuwa alhamis, a ranar juma'a kuma za'ayi musu gwaji a fitar da mutum biyar da suka yi nasara a turasu Korea course na wata biyu. Jin abin yayi kamar a mafarki ya sake karantawa. Su goma aka zaba su halarci workshop din. Idan ya amince zashi akwai inda zai danna alamar ya amince sai su turo masa da kudin jirgi. Hatta hotel din da za'a sauke su a kwanakin da zasuyi duk an tanada. Hamza dai ya rasa bakin magana sai cewa yaje IKON ALLAH. Shi bazai iya tuna lokacin da ya tura application na halartar workshop din ba. Inuwa sakatare ne ya fado masa yayi saurin kiransa. Bayan sun gaisa yake sanar dashi abinda ke faruwa. Inuwa yace Alhamdulillah, ranka ya dade ai kusan wata biyu kenan da naga tallan abin a labaran NTA sai kawai na bude website dinsu na cike maka tunda naga abin na architects ne. Banyi tsammanin zamu sami nasara ba shiyasa nayi shiru da zancen.
Hamza yace Allah Mai iko da daukaka ni bansan me zance maka ba Inuwa. Allah Ya saka maka da mafificin alkhairi.
Inuwa yayi dariya ranka ya dade ai bazan taba biyanka alkhairin da kayi min ba a rayuwata. Ban gama karatu ba ka bani aiki kuma ka cigaba da biya min kudin makaranta har na kammala. Allah dai Ya sanya mana alkhairi a wannan aikin Ya bamu sa'a.