Sashe 2
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuhra na fita gidansu Hajara ta nufa tana ta mita ta jawo mata fada a gida. Da sallama ta shiga sai dai babu kowa a tsakar gidan. Daga dakinsu Hajara ta ji an amsa ta shiga. Kwalliya Hajara take yi anyi wankan yamma tana shirin fita unguwa, mudubi ne a hannunta tana zana gira. Zuhra ta sakar mata dundu a baya...shegiya kin hada min zafi a gida kin zauna kwalliya. Hajara na sosa bayanta suka ji muryar mamanta. Ta shigo dakin haba Zuhra sau nawa za'a hanaki zagi ne? Zuhra ta sunkuyar da kai tana hararar Hajara. Mama tace idan na sake ji Allah da yayanku Lawal zan hadaki. An kwana biyu ba kiji bulala ba shiyasa kika dawo da yi mana zagi. Zuhra tace don Allah kiyi hakuri na dena daga yau In sha Allah. Mama tace da kin kyautawa kanki sannan ta fita. Hajara ta cigaba da kwalliya suna hira tace ke ni fa Sahabi ya dage sai nayi karatu. Yace zai rinka yi min lesson kafin a fara WAEC don har ya biya min kudin a wata makarantar. Zuhra tayi dariya zaiyi asarar kudi da lokaci kenan. Baki fada masa kina sahunmu bane? Bana son wulakanci wallahi tunda na fahimci yana son nayi karatu na soma dagewa. Wannan karon mutum shida na doke harda ke. Zuhra ta daga hannu alamar jinjina kaga su Fropesa Hajara kenan. Hala irin su Ligan dinnan zai nema miki. Kanwar Hajara da ke tsakar gida sai dariya ta leko ta taga...Yaya Zuhra kin fiye abin dariya. Wai Ligan...Legal ake cewa. Zuhra ta hade fuska tace in ba tsoro ba ki shigo dakin nan ki fada mana kiga yadda zanyi dake. Marar kunya kawai. Hajara ma dai dariyar take ta dauko dankwali zata daura. Sai da ta daura wani dakal dakal din mayafi karami. Ta daure shi da ribbons har biyu manya sannan tayi dauri. Daga karshen daurin ta zaro wani ribbon din mai gashi dogo daga jikinsa ta makala taga ya zauna sosai sannan ta tura shi a jaka. Duk abinda take idanun Zuhra kyam a kanta. Tace Hajara gashin doki kika koyi sawa? Da sauri Hajara ta toshe mata baki. To sarkin karadi kada ki fada da karfi sai na fita zan saka. Zuhra tace wallahi babu kyau kuma kema kin sani. Ga acuci kin dora wannan wari ma ya isheki. Hajara tace ke ba yau zan saka ba fa. Yanzu ma gidan Anti Faiza zani tayata aikin abincin da zasuyi a makotansu. za'ayi party ne a gidan. To gobe zansa idan zaa wurin party din. Zuhra tace happy bazday tuyu zasu yi? Oho nima ban sani ba. Tace dai yan gayu ne a gidan. Zuhra tace duk da haka bani gashin na kona ko na fadawa Mama.
Da kyar Hajara ta bata ribbon din. Za ta fita Zuhra tace ke kamar kwailin kike ko, kinga fuskarki kuwa? Sai yanzu na lura. Hajara ta dora hannu a ka. So kike dai Mama taji tayi fada kike wani daga murya. Kuma bleaching ake cewa ba kwailing ba kalmar ko dadin ji babu. Tana murmuahi tace wani mai na samu mai dan kyau na gyaran fata. Kinsan tunda biki ya matso gara na shafa na dan washe. Zuhra dai tabe baki tayi...wallahi Hajara ki kiyaye sabon Allah. Ga acuci, ga bleaching ga karin gashi. Shi Sahabin zaki ha'inta da farin karya ko danginsa. Naga dai duk a unguwar nan kuka tashi to meye basu sani ba.
Karasa hada jakar tafiyarta tayi tace to malama zuhra idan kin gama waazin ki zo ki rakani bakin titi. Kuma wallahi kika fadawa su Mama sai munyi fada. Zuhra tace mun dade bamuyi ba...ni akan irin wannan ba sai dai aji kanmu ba. Lokaci guda kika tsiri irin wadannan abubuwan kawai don zakiyi aure. Hajara tace to in kinji haushi kema ki fitar da miji mana. Ran Zuhra ya soso ta dan yi murmushi miji dai Allah ke bayarwa. Kuma da yardarSa idan na tashi aure sai na sami miji na gani na fada. Daga nan tayi tsaki ta fita Hajara na kiranta tana bata hakuri. A tsakar gida suka tarar da Mama tace har anyi fadan ne kajin Mama? Ku zo nan...suna harare hararen juna suka durkusa gaban Mama. Tace duk naji abinda kuke fada. Ke Hajara akan an fada miki gaskiya kike gayawa yar uwarki magana ko? Duk canjin halin da kika koya yan kwanakin nan ina lura dake. Shiru nayi so nake farin naki yafi haka yawa sannan nasa yayyanki maza suci ubanki a gidan nan. Zuhra ta kwalo ido....lah Mama kema zagin kike yi. Mama tace ban kuma ce kiyi ba, nima kuskure ne. Ta cigaba da yiwa Hajara fada kije gidan Yayar taku ki dawo zanyi maganin rawar kan nan naki. Ita ma ba kyaleki zata yi ba kin sani sarai. Idan na sake jin kuna fada kuma ni daku ne. Ki wuce ki rakata ta hau adaidaita tace da Zuhra. Sum sum suka tashi suka fita. Zuhra ke rike da jakar kayan amma har suka je titi ko tari basuyi wa juna ba. Sai da adaidaita sahun ya fara tafiya Hajara ta leko tana dagawa Zuhra hannu. Itama dagawa take tana tambayarta yaushe zaki dawo. Hajara tace sai yanzu zaki tambaya? Kwana goma zanyi.....Zuhra harda dan hawaye ta koma gida. Irin wannan fadan sun saba yin shi da Hajara. Sai dai suna sake haduwa zancen ya wuce kenan.
[9/25, 2:39 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU🗿4
Batul Mamman(Mrs)💖
Hajara na sallama gidan yayarta ta hadu da babban dan Anti Faiza Abba zaune a bakin kofar gida. Hannunsa ta gani a nade alamun gyaran karaya ko gocewar kashi. Yana ganinta ya rungumeta A dan tsorace tace Babana me ya sami hannunka? Yace fadowa nayi daga kan babur din Baba. Ba dai hatsari kukayi ba ko ta tambayeshi suna shiga cikin gidan. Yace a'a jiya ne da daddare na hau sai na fado. Anti Faiza na jin muryarsu ta fito tana mata sannu da zuwa. Tace kafin ki fara korafi jiya abin ya faru ni kuma bana son tadawa Mama hankali sai ya dan ji sauki. Hajara tace ba komai Allah Ya sauwake. Sauran yaran uku suka zo suna mata sannu da zuwa. Mai bin Abba ce ta kalli Hajara da kyau sai tace Anti Hajara kinga fuskarki tayi fari, kafarki kuma baka. Ko kema mai bleaching ce irin ta fim dinnan....
Gaban Hajara ya fadi, Anti Faiza ta bar raba kayan wanki da take yi tace bazaki make mata baki ba kina jin abinda take fada. Nabila ta ce Allah ki kalli kafarta da fuskarta ki gani. Anti Faiza ta taso zata kaiwa Nabila duka sai taga Hajara na jan siket dinta tana kara rufe kafa. Anti Faiza tace su fita tana mata wani kallo. Gaba daya cikin Hajara ya duri ruwa. Tun kafin ta tambayeta tace wallahi Mama tayi min fada dazu kuma bazan kara yi ba. Anti Faiza tace da kina hauka ne kika fara shafe shafe. Ta fizge jakar kayan Hajara ta zazzageta a wurin tana duba kayan tana fada. Hajara a hankali ta gode Allah da Zuhra ta karbi ribbon din mai gashi a jiki. Anti Faiza kuwa ta kare mata tas sannan tace ke da Zuhra kuke yi ko? Hajara tana matsar kwalla tace a'a ni kadai ce. Ba wani nan, abokin barawo ai barawo ne kuna tare wata rana zata koya ne. Ta fara laluben wayarta. Zan kira Umma ince a turo min ita ko zuwa asabar ne in ja muku kunne da babban baki. Ba don hannun Abba ba ai gidan zani na hada ku. Wato kun girma zaku nunawa duniya baku da mafadi. Ita dai Hajara sai bada hakuri take.
Bayan kwana biyu Zuhra na zaune kan karamar kujera a kofar kitchen Umma na ciki tana duba miya da yar karamar fitilarta gwamnati ta gaza. Zuhra ta rike ciki ta fara waka.
Dan kanzo
Iya ko dan dago dago
Iya yunwa bata da hankali
Iya yunwa taci mutum tara
Iya.....
Umma tace Zuhra ko in miko miki kwano ne? Ta washe baki Umma kin gama girkin. Umma tace a'a wai da ki tafi makota bara. Baki Zuhra ta turo tana rike ciki ni shiyasa bana so kice zakiyi girki Umma musamman tuwo sai ki dade. Miyar nan tun kafin magariba kika dora gashi har an idar da isha. Umma tace ni kuma kinga bana son danyen girkin nan naku. Sai ayi tuwo da miya cikin rabin awa. Suna magana Baban Yara ya shigo. Zuhra tana matse ciki tana masa sannu da zuwa. So take yasa Umma ta kada miyar haka. Dariya yayi musu ya shige ciki. Ga mara juriyar yunwa , ga mai dadewa a girki.
A falo suka zauna suna ci. Da yake ba wuta Zuhra kasa jira tayi nata tuwon ya huce tasa mafici tana fifitawa tana ci. Ta cika baki da tuwo tace Ummana kin iya girki sosai sai dadewa. Umma tace bazaki yaba min ba sai kin hada da mita. Wannan mijinki sai yayi da gaske wurin noma. Baba yace to dai kada ki takurawa babata. Ya fito da wata leda daga aljihunsa. Ya danne ta da dungulmin hannunsa sannan ya bude da dayan ya dauko gasashshiyar kaza. Umma tace yau dadi zamu ci BabanZuhra. Yace Ya'u ne ya siya shine ya debar min yace na kawowa Zuhra. Dadi ya kamata taje ta durkusa a gabansa. Cinya ya dauko mata da fikafiki biyu. Ta karba da murna ta koma wurin zamanta.
Kamar ance ta daga kai ta hango hannuwan iyayenta a gefen kwano suna kokarin raba wuya su ci. Duk zumudin da take a lokacin wani daci taji a wuyanta. Hawaye ya sauko mata tayi saurin gogewa. Ta dan gutsiri naman kadan tace washhhh. Umma tace kin kone ko? Dama cin abinci kin kasa jira ya huce. Zuhra tace hakori na ne yake min ciwo daga nasa naman a baki. Baba yayi mata sannu. Ta tashi ta mayar da duka naman gashi ku cinye bakina zafi. Baba yace ki ajiye zuwa gobe mana. Idan ya lalace ai sai nayi kuka Baba. Ta dauki tuwon bari na kai kitchen bazan iya ci ba. Ta fice tana fifita baki.