← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 67

Sashe 5

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu yasa ya taba Hamza a kafada. Hakan yasa ya juyo da sauri. Muryarsa a raunane yace ashe kuma kunji. Ummahani tana gaishe shi yace mata shiga ciki Umma ai dukkanmu mukayi rashin. Ibrahim yace rashi kuma Yaya? Nifa tun jiya Izzatu tace muzo da yara yau. Nayi tunanin irin partyn da kuka saba ne na kawo su don kada ace ina raba zumunci. Amma wallahi barnar kudin naka tayi yawa. Hamza yace ina maganar party Ibrahim. Junior ne ya rasu. Baka ga mutane da yawa ba. Ummahani na kokarin bude gate Junior ya bude tare da wasu yaran. Sun sha sababbin kaya. Hamza ya kura masa ido sannan ya dubi Ibrahim. Ibrahim yace kai wa ya fada maka ya rasu? Hamza a rikice yace Izzatu tayi waya Office tace a fada min ya karye a hannu. To ina zuwa naga motoci nayi tunanin ya rasu ne. Ibrahim yayi tsaki cike da bacin rai yace Allah Ya kyauta ni na tafi. Zuciyarsa na kuna yaja motarsa yayi gaba. Ace babban mutum kamar Yaya dan shekara talatin da bakwai ya bari mace na karanta masa yadda zasuyi rayuwa. Kodayake ba laifinta bane. Tare suke yin komai. Daga nan Ibrahim gidansu ya tafi.

A hankali Hamza ya tura karamar kofar gate din ya shiga. Kawai sai ji yayi mutanen wurin sun ce SURPRISE!!! farfajiyar gidan ya gani ya sha kwalliya an jera kujeru da tebura. Ga fitilu suna ta haskawa an kunna inji. Kida aka kunna yana tashi a hankali. Bai gama tantance abinda ke faruwa ba Izzatu taja hannunsa suka shige cikin gida. Muje ciki ka canja kaya. Suna shiga daki ta rungume shi. ....HAPPY ANNIVERSARY MY BABY.
[9/25, 2:51 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿8

Batul Mamman(Mrs)💖

Hamza ya yiwa Izzatu kallon rashin fahimta. Izzy me yake faruwa ne? Kince Junior ya karye but it seems lafiyarsa kalau. Fari tayi masa da ido irin yadda tasan yana kara dauke masa hankali, sai a lokacin ya kula da kayan jikinta. Wani irin yadi ne mai matukar santsi aka yi mata doguwar riga wadda ta dameta daga sama har gwiwa sannan ta bude sosai. Ga wani abu kalar takalminta da sarka anyi mata dauri. Tamkar wata amarya ta fito. Jikinta mai kyau ne ba kace ta haifi 'ya'ya uku ba. Tana lura da yadda yake binta da kallo tayi murmushi. Dama nayi ne kawai don ka dawo gida akan lokaci. Na gama komai na shirya mana anniversary dinmu na shekara goma. Ya shafi gefen fuskarta amma Izzy ba kya ganin abin ya danyi yawa. Ki ce dana ya karye kinsan zan tsorata. Kiss tayi masa a kumatu to yi hakuri daddyn Junior. Kaga ana jiranmu a waje.

Tare suka fito rike da hannun juna. Sunyi matukar kyau sosai ga yaransu suma sun sha ado. Babban shekararsa biyar suna kiransa Khalifa mai sunan Alhaji Nasiru. Sai Junior mai shekara uku sunan baban Izzatu gareshi Sunusi sai kuma Nana(Halima) mai neman shekara ta biyu. Sunan Mama yaso saka mata sai dai Maman taki saboda Ibrahim da Mariya duk sunyi mata takwarori.

Hajara tana ta binsu da ido duk inda suka yi ana ta gaisawa da daukar hotuna. Ga masu rabon abinci suna ta yi su ma. Tace kai Anti Faiza ina ma Zuhra tazo muci son ran mu. Ji kaji kamar su suke kiwonsu. muma dai Allah Ya bamu kudin nan muji dadin rayuwa mu rinka party duk shekara. Mariya tace ba amin ba kanwata. Anti Faiza da Hajara suka juya suna kallonta. Hajara tace kinji min mata da bakinciki. Faiza ta kai mata duka to shashasha baki san mutum ba zakiyi rashin kunya, yi hakuri baiwar Allah. Ko ba'a fada ba daga shigar Mariya an san tana da kudi. Murmushi Mariya tayi ba komai ke dai kiyi adduar arziki mai albarka ba na party ba. Daga nan ta tashi ta hada kan 'ya'yanta sukayi waje.

Haka aka cigaba da taro har wurin karfe takwas na dare. Nura ne suna shirin tafiya dasu Adabiyya yazo ya fadawa Hamza sakon Mama kan cewa tana son ganinsa a yau. Sai bayan fitarsu ya duba agogonsa. Subhanallah ya fada da karfi tare da mikewa. Izzatu tace yaya akayi? Ya nuna mata lokaci. Kinga har lokacin isha yayi bamuyi magriba ba. Ta dan tura baki idan an watse ba sai muyi ba. Bana son a fara shiga ciki ne azo a bata min toilets. Hamza yace ni dai bani key please. Ta dan daure fuska Allah bazan bayar ba. Kana shiga mutane zasu fara bin bayanka. Ya girgiza kai yana murmushi Izzy baki da dama. Wani famfo ya zagaya a bayan gidan yayi alwala sannan ya fita masallaci. Duk lalacewar lamarinsa bai tashi da tarbiyar sakaci da sallah da gangan ba.

Ana gyaran wurin jamaa sun watse sauran kadan Hamza ya fito zuwa gidansu. Izzatu ta bashi manyan kuloli cike da abinci, nama da snacks. Ga katon din juice da na ruwa ya kaiwa su Hajiya.

Kula daya ya dauko maigadi ya biyoshi da sauran. Da sallama ya shiga babban falon. Mama da Hajiya ne a wurin sai Jidda da ta biyo su Nura tana jiran mijinta. Duk suka amsa sallamarsa sannan Mama tace maraba da Mungo Park. Turus Hamza yayi ya kasa furta gaisuwar da yake shirin yi musu. Hajiya tace Jidda tashi mu shiga ciki uwa da danta zasu gana. Dama zamanta a wurin ta kara tunzura mama da bayanin abinda ya faru a wurin partyn. Hamza yayi murmshi da wuya kaga fuskarsa a hade sai dai idan yana cikin tashin hankali. Mama nasan nayi laifi ko baki fada ba. Amma wallahi nima bani da masaniyar wannan party din. Surprising dina tayi nima. Mama tace ai naga alama. Zaka ce iyayenta basu da labari ne? Ka hado kuloli ka kawo wa mayunwatan iyayenka abinci ko. To duk ka kwashe abinka bama so. Yace Mama ita da kanta ta bani na taho dashi. Tace kaga ni ba wannan ke gabana ba kaji ko. Yanzu don Allah Yaya yaushe zaka san ka girma? Wace irin rayuwa ce kuka daukarwa kanku kai da iyalinka. Kanka aka fara zuwa kasar waje karatu ne da zaka dauko al'adun da ba naka ba kayi ado da su. Sau nawa muna yi maka fada ni da Hajiya akan birthday partyn da kuke wa yaranku duk shekara amma ka share. Irinsu valentine dinnan ma duk kuna yi ko? Shiru Hamza yayi don yau kam ya san ya batawa Mama rai. Tace ba tambayarka nake ba. Yace munayi. Ta cigaba da fada....duk wani dan iskan day da yahudu da nasara ke girmamawa kaima ka girmama. Ka iya kashe kudi mai tsoka ka shiryawa yara party kawai don suji dadi. Irin sadakar nan ta abinci ko kudi kuwa sai karshen ramadan. Baka tunanin halin kuncin rayuwa da mutane ke ciki yanzu.
Alhamdulillah muna da rufin asiri ci, da sha da sutura babu wanda Alhaji baya saukewa amma ai ihsani yana da dadi ko. Ko kasan duk wata sai Ibrahim ya kawo buhun shinkafa gidannan sannan ya bamu dubu biyar biyar ni da Hajiya. Ya san ba kudin ko abincin muka rasa ba. Amma yana neman albarkar iyaye. Mariya da Jidda suma suna nasu kokarin da dan abinda sukeyi. Duk cikinsu kafi kowa morar Alhaji kuma ka fisu kudi amma daga kai sai iyalinka. Kawaici kawai mahaifinka yake maka irin na bafillatani amma ko kadan baya jindadi. Shin ka taba zama ka tambayeshi a halin da kamfaninsa yake ciki? Ko ka tambayi Hajiya me take bukata ko da ba na kudi bane? Hamza ya girgiza kai a hankali. Mama bata san cewa tana fadan ma hawaye take yi ba. Tace to girma ya kama babanku. Ibrahim lecturer ne amma daga wurin aikinsa yana zuwa kamfanin taya shi aiki. Nura yanzu yake ajin karshe a jamia amma tun yana level one yake zuwa. Hamza yayi mamaki wai Nura har ya kai level four yanzu sai dai bai nuna ba kada fadan ya karu. Ita kuwa Mama cigaba tayi da fadanta. Yan uwanku na Kumo makusanta. Ina nufin yan uwan Hajiya da na Alhaji kasan halin da suke ciki? Ko kasan a rage maaikatan banki harda kanin Hajiya. Hamza ya dago kai wanne? Tace Nafiu. Gashi yana da mata biyu da 'ya'ya goma sha uku. Watansa kusan bakwai ba aiki. Akan Nafiu Hajiya ta soma kukan rashin taimakon da kake yi. Maganganun sun ratsa Hamza sosai. Ji yayi kamar wanda aka tasa daga bacci. Mama tace ni dai lahirarka nake duba maka Yaya. Rayuwarka nema take ta sauka daga turbar addini. Har yau ban manta yadda Izzatu tasha maganin hana haihuwa ba wai sai ta gama karatu. Allah ne ma Yaso kuna da rabon haihuwar daga baya. Ka tashi ka je ka bawa Hajiya hakuri ka tafi dare yayi. Hamza yayi godiya sosai tare da sake bata hakuri. Har ya kai bakin kofa tace Yaya....naam ya amsa. Nasan saura baifi sati biyu ba birthday din Nana. Kwana hudu kafin ranar ka dawo dasu nan. Wallahi ka sake celebrating birthday a gidanka zaka ga fushina sosai.. Allah Yayi muku albarka
[9/25, 2:51 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿10

Batul Mamman(Mrs)💖

Zuhra ta shigo layin gidan Anti Faiza sai ta hango mai tsamiyar biri yana turawa a baro. Tsallakawa tayi bangaren da yake zata siyo. Dama tana ta tunani yar tsarabar da zata kaiwa su Abba.

Hamza da Izzatu suna mota suna hira tana fada masa Inuwa sakatare ya kira yaji ya jikin Junior fa. Dariya sukayi yace kin mayar dani makaryaci dai. Khalifa ne ya hauro daga baya ya dawo gaba ya zauna kusa da Izzatu. Ta juya ta harari maiaikinta. Ke Tala garin yaya kika bari ya taso har ya dawo nan. Oya Khalifa koma wurin zamanka. Ko kulata baiyi ba yace daddy ka kawo na tayaka driving. Hamza yace not today Khalifa kaga anyi ruwa jiya titin babu kyau. Kuma akwai mutane a nan. Khalifa yace ko sau daya ka bari na dana. Izzatu ta kama shi zata mayar bayan mota yasa ihu tare ta riko wuyan Hamza. Iyakar karfinsa yasa yana jan babansa. Garin ya cire hannun Khalifan ya dan dauke ido daga kan hanya.
Chapter 5 · 0% Book details