← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 67

Sashe 31

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tashi yayi da sauri ya kamo wuyan rigarta ta baya ya dawo da ita...haba yar kauye daga magana sai ki dauke abincin. Ya dan yi mata kalar tausayi, nima ina son ci don Allah ki ajiye. Zuhra ta dan harare shi to Hajiyan fa? Flask din ya soma ja itama tana ja. Da taga yafi karfinta sai tace to bari na zuba maka kadan sai ka kai mata sauran. Kaga duk duniya ga namiji bashi da abinda yakai mahaifiyarsa daraja. Kafin na tafi in sha Allah idan kana so kullum duk abinda take ci ka fada min sai na dafa mata. Ummana tace idan nayi aure na taya mijina neman aljanna ta hanyar kyautatawa iyayensa da sauran ayyukan kirki. Kaga yanzu kafin ka sake ni ko dan yaya sai nayi abinda tace ko? Sai kuma ta rufe baki da hannu daya...ka ganni ko? Umma cewa tayi ba fada maka zanyi ba sai dai ka gani a aikace. Don Allah kada kace na fada. A shagwabe take masa maganar wadda tayi matukar tasiri a ransa. Har wani dan dukan bakinta take yi ita a dole tayi laifi. Allah kadai Yasan farincikin da Hamza yaji a wannan lokacin. Yau shine da matar da take nuna damuwa akan mahaifiyarsa fiye dashi. A wannan lokacin gani yake Zuhra tafi masa kowace mace. Bai yarda sonta yake ba amma a shirye yake ya kyautata mata iya karfinsa...a hankali take samun masauki mai daraja a zuciyarsa. Ido ya zuba mata kawai yana kallonta. Ita kuwa kuwa tana kare maganarta tayi gaba da flask din ba tare da ya tareta ba.

A dan plate ta zuba daidai yadda zaici ta hada sauran wuri daya. Takaici ma take bata sani da wuri ba ai da tayu mai yawa. Naman da ta soya ta diba ta zuba a kai saboda farfesun tayi shi da yaji tunda Hamza na mura.

Tunda Zuhra ta fita yake ta kai kawo....ya tsani ta tayar da maganar sakin. Shigowarta tasa ya sami wuri ya zauna ta mika masa plate din. Jan hannunta yayi ya zaunar da ita a gabansa. Nasan kin fini jin yunwa ki ci ni ga nawa abincin ya nuna mata farfesun....cikinta har wani kullewa yake ta yi murmushi da gaske ka bar min. Hamza yace eh...plate din ta janyo gabanta ta soma ci da sauri. Ya kama hannunta lesson two yar kauye, ki dena cin abinci da sauri kuma banda katuwar loma. Ta danji kunya sai tace to yaya zanyi? Dan madaidaici ya diba a spoon din ya nuna mata. Tace dama Babana yace kada nayi loma a gabanka...Allah Yasa na iya denawa dai. Amma meye kake cewa lesson one da two? Kallonta yake ya rasa me yake ji game da ita so nake ki zama yar gayu kafin lokacin rabuwarmu, yadda zan dena kiranki yar kauye. Washe baki tayi da gaske don Allah? To ai da ka fada min da wuri yadda zan kiyaye duk abinda ka gyara min. Rabin abincin taci ta ture plate din ni na koshi. Hamza yace don nace ki rage loma? Yamutsa fuska tayi a'a cikina ne ya kulle tea zan sake sha. Sannu yayi mata sannan yaja plate din ya ci sauran tare da shan farfesun. Kamar kullum yau ma abincin Zuhra yayi dadi. A zuciyarta kuwa dadi taji ta bashi dambun saboda tana ganin irin kallon da yake yiwa abincin tunda ta soma ci.

Yana gamawa ta hada masa wanda zai kaiwa Hajiya a wata yar jaka ta bashi. Yace to daga can zai biya office. Har ya isa gidansu ko na sakan daya bai dena tunanin Zuhran Baban yara ba.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 49

Batul Mamman(Mrs)

Da yake weekend ne a falo ya tarar da mutan gidan suna kallon wani shiri da akeyi a Sunna TV. Kannensa suka gaishe shi ys amsa da sakin fuska. Sannan ya gaishe da iyayensa. Mama tace Yaya yau ina office din? Zama ya fara yi sannan yace mura ke damuna amma tayi sauki. Yanzu ma can zan wuce, aiko ni aka yi wurin Hajiya. Hajiya tace ni kuma? Jakar hannunsa ya tura mata gabanta gashi inji Zuhra. Hajiya dai kunyar bude jakar tayi Mama tace kaga Yaya miko min nagani.

Kowa a falon zuba ido yayi yaga abinda ke jakar sai ga Mama ta fito da food flask mai kyau. Tana budewa dambun shinkafa ne ke kamshi mai dadi. Muryarta a shake kamar tayi kuka tace Adabiyya, Nura, Hamida ku shiga ciki. Ba musu suka tashi suka barsu su uku a falon. Mama ta turawa Hajiya flask. Kinga abinda ke ciki kice wani abu. Murmushi Hajiya tayi nagani Mama amma me zance? Ga mamakinsa duka su biyun hawaye sukeyi. Hankalin Hamza yayi matukar tashi ya fara basu hakuri. Mama tace Yaya ko kasan tunda kayi aure abincin gidanka bai taba shigowa gidan nan ba sai yau. Kasan gidan iyayenka babu yunwa amma a tamu al'adar lokaci zuwa lokaci mace takan yi girki na marmari ko da da sallah ne ta aika gidan surukanta. Irin haka yana sa iyayen miji su so matar musamman idan tana da tarbiyya. Shima mijin indai yasan kimar iyayensa dole matar ta sake samun wuri a zuciyarsa. Hannuwansa ta kama gam ta rike...Yaya yanzu kayi aure, nasan zaka ga kamar muna kin Izzatu amma ko kai shaida ne akan bambancinsu da Zuhra. Kwalla ce ta cika masa ido shima ya basu labarin yadda akayi ya kawo dambun. Hajiya dai kasa rike kukanta tayi ta tashi ta bar falon. Ashe tana da rabon ganin Hamza ya auri macen da zata saka shi a hanya..Allah Yayi mata albarka. Ko ba'a fada ba tasan shima ba karamin dadi yaji ba.

Tana tafiya Mama ta share hawayenta. Yaya ka rike Zuhra amana Alhaji bai maka zaben tumun dare ba. Idan ka cutar da 'yar mutane saboda dalilin da ya jawo aurenku Allah zai kamaka da hakkinta. Tana gama magana tace jirani ina zuwa. Kafin ta dawo Hamida tazo tace Yaya gobe bayan laasar zamu zo ni da Adabiyya muyi weekend. Yace to Allah Ya kaimu.....shikenan zasu zo su takura masa idan yana tare da Zuhra. Shima weekend din yake jira yini biyu a gida ba fita.

Mama dakinta ta tafi ta dauko dubu sababbin dari dari ta bawa Hamza ya kaiwa Zuhra tukwici. Tunda yake bai taba tunanin irin haka na faranta zuciyar iyaye ba sai yau. A hankali yace God bless the day I met you Fatima. Allah Yayi miki albarka. Ko flask din bai jira ba ya fita ya tafi office. Duk aikin baya masa dadi so yake yaji muryar Zuhra tana masa shirmenta ko shagwaba. Har mamakin kansa yake, ga babban abin kunya bashi da numbar wayarta ma. A lokacin ya tuna wayar tata tana da matsala, bayan sun gama cinikin filayensa da wani dillali ya tashi. Beirut road ya wuce ya siyo wata sabuwar waya kirar Samsung mai kyau. Nasa tukwicin kenan na abinda Zuhra tayi masa yau. Daga nan ya biya wani shago yayi yar siyayya ya tafi gidansa.

Yana ajiye mota ko gida bai shiga ba ya fita masallaci saboda a hanya yaji kira. Can ya zauna har aka yi sallar Isha sannan ya dawo ya shigo da kayan da ya siyo. Duhun da ya gani ya tuna masa bai nemi wani maigyaran injin ba gashi har dare yayi. Zuhra ce ta fado masa ita da ko wayar kirki bata da ita. Nemanta ya shiga yi daki daki baiji motsinta ba. Abin ya bashi mamaki ko bacci take yi ne? Yana hawa sama tana fitowa daga dakinsa da fitila a hannu daya, daya hannun kuma tsintsiya ce da abin kwasar shara. Har ajiyar zuciya yayi, ita ta fara magana tace sannu da zuwa. Murmushi yake yauwa yar kauye. Me kike yi da tsintsiya a duhun nan? Tsoro na rinka ji ni kadai sai kawai na fara shara da wankin bandaki. Amma dai ban bata maka rai ba da na shiga dakinka ko? Naga yanzu kana min kirki shine nace bari nima na gyara maka daki. Bai amsa mata ba sai da yazo gabanta...baki yi laifi ba yar kauye, nagode. Ki je kasa akwai kaya a falo ki kai kitchen dinki bari nayi wanka.

Bai shiga dakin ba sai da ta saukq kasa. Dadi yaji sosai har da turaren wuta ta saka. Ta gyara gadon tayi shara. Toilet din ma ta wanke shi tas har boxers dinsa da vests da suke cikin wani abin zuba kayan wanki duk ta wanke amma bata shanya ba saboda wurin shanyar yayi mata tsaho. Sau uku take niyar wankewa sai ta fasa wai kada yace bata da kunya. Sai daga baya ne ta daure zuciyarta ta wanke su harda kawar da fitilar gefe ita bata kalla ba bare ace mata 'yar iska.....

Ba jimawa ya sauko yace mata tayi girkin dare ne tace a'a amma zata dora yanzu. ki dafa mana indomie kawai akwai a cikin kayan da nazo dasu. Cikin 'yan mintuna ta gama ta kawo. A plates daban ta zuba musu. Maigadi kuwa dama ana magariba ta dafa masa taliya. Hamza na kallonta har ta zauna zata fara ci ya dauko nasa plate din ya dawo gabanta, tasa ya juye a cikin natan sannan ya soma ci batare da yace mata komai ba. Ido ta zuba masa ta kasa ci saboda tana gudun tsokanarsa. Ya dago kai suka hada ido....lesson three, yana da kyau mata da miji suci abinci tare. Yana kara musu shakuwa da son juna. Kyakkyawan murmushi tayi...Allah, to amma ba da kai ya kamata naci ba kada mu shaku gashi zamu rab....hannunsa yasa ya rufe mata baki ta daga ido tana kallonsa. Ki dena zancen rabuwarmu akwai sauran lokaci. Just eat. Babu abinda yaki jini yanzu kamar tayi zancen rabuwarsu, idan lokacin yayi sai asan abinyi amma for now so yake yayi enjoying moments dinsu tare.

Sai da Zuhra ta gyara kitchen sannan tace masa sai da safe Allah Ya kara sauki. Lokacin aiki yake da laptop a gabansa. Suma yan nepa kamar sunsan injinsu ya lalace suke kim basu wuta sosai.
Chapter 31 · 0% Book details