Sashe 7
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Baba yace zo ki zauna kinji Fadimatu. Ta zauna bakin nan kamar ya zunguri kofa saboda yadda ta turo shi gaba. Yace yanzu don Allah idan ke namiji ce kika ga mace irinki zaki so ta? Tace eh to ya danganta da namijin. Baba yace ni bance sai mai kudi ba amma dai Zuhra a sami rufin asiri. Ke kadai fa Allah Ya bani dole na so ki da alkhairi. Dazu kina cin abinci lomarki har tafi tawa. Itama dariya maganar ta bata. Ta sunkuyar da kai. Baba yunwa naji sosai a lokacin. Yace to abinda zai faru nayi miki alkawarin waya mai kyau harda kemara indai zaki rinka tsafa. Alhamdulillah Zuhra tace da karfi tare da fadawa jikin Baba tana godiya. Yace dagani duk gidannan kinfi kowa nauyi saboda cin ki. Ta mike tsaye tana tsalle daga yau zaka ga canji Baba. A wurin ta cire hijab da dankwali ta kama zanin zata kwance Baba yace shiga daga ciki dai yana kawar da kai. Ta wuce da tsallenta kamar karamar yarinya. Baba yace da Umma kin kula da hannun rigar mamanta kuwa? Dandakuwa..... Umma tace Baban Zuhra ka fiye gane gane kaima. Allah Yasa canjin ya dore dai. Kusan minti goma sai gata ta fito da daurin kirji da gashinta buzu buzu. Ta dauko kwandon wankanta da yar robar shampoo ta wuce bakin rijiya ta debi ruwa bokiti biyu. Suna nan zaune ta fito bayan kusan rabin awa tayi wanka da wanke kai. Umma tace har kin danyi haske kuwa. Bata ce komai ba ta shige daki.
Tasha wahalar taje kanta sosai saboda tsabar cikarsa. Ta shafa mai a ko ina ta raba biyu tayi kitso manya. Ta shafa mai a jikinta da body spray din da Baba ya siyo mata. Ba wani abu ke sawa bata amfani dasu ba, ita a tunaninta idan basu kare ba Baba zai ajiye kudinsa yayi wani abin dashi. Tana matukar tausayinsa saboda lalurar hannu da ta same shi.
Sai da akayi laasar ta fito fes da ita. fuska tasha hoda da janbaki orange, har girarta ta gyara. Baba kuwa baki yaki rufuwa da ya ganta bayan ya dawo daga masallaci yace ko ke fa. Allah Yasa ayi gamon alheri a hanya. Umma tace iyayen zamani ba kunya. Dari biyu ya bata kudin mota tayi godiya ta fita. Tafiyar ma kokarin daidaita kafarta ta rinka yi kada Baba yace tayi ta maza. Sai da ta fita Umma tace ba naga ka siyo wayar ba. Yace eh kyaleta muga zuwa kwana biyu sai na bata. Ki rinka sa ido tana gyara kanta. Ga iya zuwa islamiyya daukar karatu amma bata damu da tsafta ba.
[9/25, 3:23 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿11
Batul Mamman(Mrs)💖
Su Anti Faiza sun sha dariya da Zuhra ta basu labarin dalilin shigowarta a guje. Anti Faiza tace lamarinki sai addua Zuhra. Yanzu meye na rashin kunya bayan an baki hakuri? Zuhra tace yana daga mota fa yake bani hakurin. Ni dariyar da suka yi min ita yafi bani haushi. Hajara tace to ba dole suyi ba kin kama fuska kinyi mata zane. Ji girarki kamar an miki fenti. Zuhra tace wai haka Anti? Yau baki ga yadda Baba yayi murna ba har alkawarin waya yayi min. Daga nan suka cigaba da hira. Anti Faiza ta sako zancen bleaching tana musu fada. Zuhra tace nima hanata nayi har malama Rabia na tambaya hukuncin mai yi. Ta zauna tayi musu bayanin yadda suka yi da malama. Anti Faiza tace ato ni dai nasan kuna tare naji tsoro kada ta koya miki hali kinsan ance zama da madaukin kanwa.....
Bayan kwana biyu suna cin danmalele a falon Anti Faiza suka ji sallama. Zuhra ta kwaye zaninta har ana ganin cinyoyinta. Anti Faiza sai fada take mata basu ji sallamar ba. Abba ne ya amsa sai ga Izzatu ta shigo. Da yake Zuhra na fuskantar kofa tana shigowa suka hada ido. Sai da ta kware don tsoro sannan ta tashi da gudu ta shige daki. Anti Faiza cikin mamaki tace sannu da zuwa Maman Khalifa. Ganin Izzatu na kallon kofar dakin tana dariya tace wata kanwata ce mai shirmen tsiya. Izzatu tace ai mun taba haduwa. Ta baki labarin an kusa kadeta da mota shekaranjiya ko? Zuhra daga daki tana lasar hannunta da ya sha manja tace na gama yawo yau.
A falo Anti Faiza tace ba dai Alh Hamza ta yiwa rashin kunya ba? Ke Zuhra fito. Izzatu tace ba kararta na kawo ba. Ni ta burgeni ne ma. Don baki ga idanunta ba da ya fito daga mota. Yadda kika san ta saki fitsari a wajen amma duk da haka bata dena magana ba. Anti Faiza tace ai indai Zuhra ce ta wuce nan. Sai ki fito ki bata hakuri ta kira Zuhra daga daki.
A sanyaye ta fito ta gaishe da Izzatu sannan tace ku yi hakuri. Hajara tana gefe tana musu dariya. Izzatu tace ba damuwa. Ai ranar baki ga yadda yaji haushi ba. Har muka je muka dawo yana mita. Ni da zaki bini gidana ma ai da saka ku zanyi a gaba ina samun abin nishadi. Zuhra ta kalleta da mamaki. Yanzu nufinki baki ji haushin duk abinda na fada masa ba? Izzatu tace not at all. Zuhra dai bata gane dangantakar turancin da tambayarta ba, sai tace da nice wallahi fitowa zanyi daga motar in saita bakin mara kunya. Hajara ta dan taba Anti Faiza sannan ta kallo Zuhra alamun ayi mata magana. Izzatu ta ce ni bana son hayaniya nasan he will handle everything shiyasa na kyale ku.
Maganar ta bawa Zuhra mamaki sosai. Ace wata tayiwa mijinki rashin kunya kice baki damu ba. Gaskiya ke a mata daban ce....anti Faiza tayi saurin toshe mata baki. To sarkin shirme ance abinda kika yi babu komai kin dage sai neman jawo magana kike. Maman Khalifa don Allah kiyi hakuri. Izzatu tayi dariya ke babu komai fa.
Haka suka cigaba da hira Zuhra tana basu labarin Baba na son yi mata aure amma yace yafi son miji mai ilimi. Ni kuwa indai gida da abinci bani da damuwa. Hajara tace amma kika ki maikifi? Baki taba tsayawa gabansa bane shiyasa kike magana. Banda karni babu abinda yake. Anti Faiza tace wai kura ce zata ce da kare maye. Ke da ba kya minti uku kin gama wanka ai bai kamata ki guji dan uwanki kazami ba. Zuhra tace baki ji na fada miki Baba zai bani waya bane..ai daga yanzu zan rinka wanka sosai. Ita dai Izzatu har ranta shirmen Zuhra yana bata shaawa. Dalilinta kenan na zuwa gidan ranar don idan tana neman Faiza waya take yi mata.
Kwana hudu Zuhra ta yi a gidan suka koma tare da Hajara. Baba ya bata dubu shida yace ta kaiwa mai koya mata sakar. Cikin dan kankanin lokaci ta fara kwarewa saboda abu ne da take so. Ga tsafta an dore da wanka. Kwalliyar ce dai har yanzu da sauki. Baba ya cika alkawari ya bata wayar. Ranar murna ba'a magana. Haka ta rinka shiga makota tana nuna musu. Mamansu Hajara ma tayi murna. Don duk makotansu sunfi shakuwa sosai tamkar yan uwa. Tecno ce second hand ya siya a wurin wani dan layinsu. Da yake suna ganin girman Baban Yara kamar yadda suke kiransa ba karamin sauki mai wayar yayi masa ba.
Arch Hamza na zaune yana duba wasu takardu a office dinsa Inuwa sakatarensa yayi sallama ya shigo. Bayan sun gaisa yace ranka ya dade naji baka ce komai ba game da text da wayar da nayi maka. Hamza yace yi hakuri wasu abubuwan ne suka dauke min hankali. Izzatu ta fada min komai. Babu matsala nagode. Har kunya yake ji ace matarsa karya tayi. Inuwa yace ranka ya dade babu matsala? Hamza ya ajiye takardun ko dai akwai wani abu ne Inuwa? Shi a tunaninsa Inuwa ya gano Junior lafiya yake. A'a babu komai, dama wannan maganar ce kawai. Daga nan ya fita. Tunda Oga bai damu da yanayin contract din ba gara ya dena damun kansa kawai. [9/25, 3:29 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿12