Sashe 11
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Su Zuhra sun kawo kwanar layin gidan Anti Faiza wasu mata uku suka tsayar da mai adaidaitan. Suka yi ciniki yaji kudi yace Zuhra ta sauka. Rai a bace tace haba malam ba haka mukayi da kai ba. Jakar nan nauyi gareta kuma gidan yayi dan nisa daga bakin titi. Naira hamsin ya miko mata gashi ki nemi wani ya karasa da ke. Ba yadda zatayi dole ta fito tana kunkuni. Ta kalli matan sunsha ado da gani biki zasu je ta dan murguda baki...ku ma Allah Yasa ku hadu da wanda zai muku abinda kuka yi min. Dankwalinta ta ciro daga kanta ta gyara hijab din sannan tayi gammo da dankwalin. Tana kicikicin dora ghana must go din taji horn din mota a gefenta. matsawa tayi tana tunanin ko ta tare hanya ne. Horn din ta sake ji sai ta dan juyo taga ko da ita ake. Ba karamin mamaki tayi ba da taga matar mutumin nan mai fadan tsiya.
[9/25, 3:35 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿 17
Batul Mamman(Mrs)💖
Zuhra ta washe baki tana murmushi tace ke ce? Izzatu itama murmushin take tace nice. Kingane ni ko? Zuhra ta gyara jakar kanta tace eh mana. To shigo na rage miki hanya Izzatu ta fada tana bude mata gaban motar. Allah Ya sani kayan da nauyi ba musu ta sauke tace ina zan saka jakar? Izzatu ta bude mata booth ta saka sannan ta dawo gaba ta zauna. Sai da ta zauna sannan ta gaishe da Izzatu. Sanyin AC yasa ta wani lumshe ido don har ta fara gumi. Izzatu ta ce gidan Faiza zaki je ko? Kai Zuhra ta daga don ji takeyi kamar tayi bacci. Ba karamin dadi take ji ba yadda sanyi ke busowa ta gaban motar. Ko da suka tsaya tace da mun saba dake cewa zanyi ki sake kunna min sanyin nan ko da na minti daya ne. Izzatu sai dariya tace ai mun saba idan kina so sai na kunna miki amma idan zaki bini gidana. Da sauri Zuhra ta bude kofa, wa ya aikeni naje na hadu da mijinki. Rufa min asiri.
Tare suka shiga gidan tana jan jakar kayan Izzatu na binta a baya. Anti Faiza tayi mata godiyar taimakon Zuhra da tayi. Izzatu tace ai ba komai. Kanwar taki ce akwai ban dariya. Ta dauko wayarta daga jaka, dan bani number dinki sai mu rinka gaisawa. Anti Faiza tayi saurin rike hannun Zuhra da take kokarin duba numbarta a cikin wayarta don bata haddace numbar ba. Tana dan yake tace rabu da lamarin Zuhra damunki zata rinka yi da flashing. Zuhra ta zumburo baki haba Anti Faiza nima fa yanzu ba zaman banza nake ba. Da sana'a ta, dan kudin gaisawa dai ina dashi. Izzatu tana dariya tana kallon kayan da Anti Faiza ke dubawa. Daya ta dauka ta bude daga cikin ledarta tace amma sakar nan tayi kyau. A ina kuka siya? Zuhra tayi caraf tace ni nayi. Da gaske Izzatu ta tambaya. Anti Faiza tace eh sanaarta kenan. Izzatu na jin haka tace lallai sai ta karbi numbar Zuhra. Kizo muje gidana ki gwada su Nana sai kiyi musu. Zuhra tana ta zumudi ta bada number sannan ta amince zata je gidan Izzatu tunda ta tabbatar mijinta baya gida.
Cikin daki Anti Faiza ta kira Zuhra. Naga kina ta rawar kai akan matar nan. Tunda nake da ita bata taba zuwa gidana ba sai kwanakin baya da suka kusa bige ki a mota. Daga ranar ban kara ganinta ba sai yau duk a dalilinki. Don Allah ki kama kanki nima ba wani sabawa mukayi ba. Aikin kayan flawa take bani tana biyana. Kuma kodayaushe ni nake zuwa gidanta. Zuhra tace to ko dai na fasa zuwa kawai. Nace ta kawo yaran nan. Anti Faiza tace ba haka nake nufi ba. Kije amma ki kula kinji ko.
A hanyarsu ta zuwa gidan Izzatu tana ta yiwa Zuhra tambayoyi ita kuma ta dena yar fara'ar da take yi saboda maganar Anti Faiza. Izzatu duk ta damu don ita tsakani da Allah shirmen Zuhra na burgeta. Tace ko dai nayi miki wani Zuhra? Eh to ba wai wani abu kika yi ba, Anti Faiza ce tace na kama kaina a gabanki itama bata saba dake sosai ba. Izzatu tace kuma a sirri ta fada miki ko? Zuhra tace eh....au tayi saurin rufe baki. Kuma wai sai na fada miki. Kai amma banji dadi ba. Izzatu tace bazan taba nuna mata kin fada ba. It's going to be a secret. Zuhra tace uhmmm tana dan murmushi. Turancin yayi tsauri kuma gashi kamar na yan TV ba'a ganewa sosai. Shiyasa tayi shiru kawai.
Gida ne mai kyau suka shiga sai dai ga kaya a kwaleye ko ta ina. A falon ma babu kujeru sai carpet kawai. Zuhra tana ta kalle kalle tace tashi kuke ko tarewa? Izzatu tace tashi zamuyi. Babyna ya gama gininsa. Zuhra ta rufe fuska da hijab tana dariya. Wai baby....Izzatu tace shine kike min dariya to ya kike kiran naki saurayin? Zuhra tace bani dashi amma ko na samu ni ban iya irin wannan abin ba. Kunya zanji wallahi. Izzatu tayi dariya sannan ta tashi ta kirawo yaranta daga dakinsu. Zuhra kallonsu kawai tayi tace ta gane yadda zata yi sakar. Suna tafiya tace 'ya'yanki kyawawa kema kyakkyawa. Ke kam kinji dadinki. Ga gidanku ma mai kyau. Yanzu idan kuka tashi wanda zaku koma ya kai girman wannan? Izzatu tace yafi wannan ma. Hira sosai suka yi har Zuhra ta fahimci Izzatu tana da kirki. Har kyautar turare tayi mata da zata tafi.
Bayan ta koma gida ne take bawa su Umma labarin Izzatu da kyautar da tayi mata. Sunji dadi amma anyi mata fadan karbar turaren.
A nata bangaren Izzatu ta bawa yayarta Zeenatu labarin Zuhra ta waya suna ta dariya. Zeenatu tace irinsu idan kika yi fooling dinsu bazasu gane da wuri ba. Izzatu tace kwarai kuwa. Ita da akayi sirri da ita shine ta fada min. Ina jin APRIL FOOL din shekarar nan da ita zanyi. Zeenatu tace ke da mijinki ya kafa miki doka. Mtsw rabo dashi wannan ai ba harkar kudi bace bazai damu ba. Ke ni har dashi ma zan hada ta fada tana dariya. Dama nace zan rama hanani party da yayi. Zeenatu tace zamu zo Kanon da su Mummy cikin next month kafin na koma Alaska.
[9/25, 3:36 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿18
Batul Mamman(Mrs)💖
Bayan kwana biyu Izzatu ta gama tsara yadda zata bullowa Zuhra. Murmushi keta tayi don ta tabbatar ba karamin shan dariya zasuyi ba.
Hamza ya dawo gida a gajiye 'yan kwanakin nan baya samun hutu sosai. Wani aiki ne ya sasu gaba, ga shirin tashi sunayi. Duk abin ya rincabe masa. Yana kwance necktie dinsa Izzatu ta shigo dakin ta rungume shi ta baya. Sannu da zuwa my darling. Murmushi yayi mata..kema sannu Izzy. Duk na barku da aiki ko. Ba komai, how was your day? Alhamdulillah ya bata amsa. Amma ina jin yunwa sosai. Me kika dafa mana yau? Ban fahimceka ba, ka manta yau thursday. Ga yara sun dawo daga school kowa yunwa muna ta jiranka. Naso kiranka na tuna maka a kawo na rana sai nayi bakuwa. Tun kafin ta gama magana ya rufe idanunsa saboda ransa da ya baci. Ba rashin girkin ne ya dame shi ba kamar yunwar yaran. A hankali ya kalleta Izzy ina ganin lokacin canja wannan tsarin yayi. Ga 'ya'ya Allah Ya bamu. Ki duba irin ayyukan da suke gabana kinsan dole na manta. Kuma su yaran ba kya jin tausayinsu ne. Ko indomie sai ki dafa musu. Ta harare shi wasa ma kake yi Hamza. Duk tsarin da muka yiwa rayuwarmu tun kafin aure yanzu a hankali kake soke komai. Don kawai kaga ina hakuri. Tana magana sai kuka ya kwace mata. Kada ka bari soyayyarmu ta ja baya saboda sabon ra'ayinka. Ni ba wannan Hamzan na aura ba. Wanda na aura ya damu da farincikina. Tausayi ta bashi ya rungumeta yana bata hakuri. A hankali yake magana. Izzy ya kamata mu fuskanci rayuwa a yadda take. Na daukar miki alqawura da dama ba tare da dogon tunani ba. Ba kullum ne zamu sami abinda muke so ba. Kinga saboda bana son tsegumi da kaina nake siyo mana abinci duk alhamis. Yau na gaji ga ayyuka. Ki daure ki rinka girkin ni kuma duk lokacin da nake da time sai na siyo a waje mu ci. Ta dago fuska sharbe da hawaye to naji amma sai ka amince ranar da zamu tare zamu danyi walima mutane su tayamu murna. Izzy na dauka mun rufe irin wadannan abubuwan. Tace walima nace ba party ba. Ko kida bazamu kunna ba I promise. To ba komai amma har yaushe zaki shirya wata walima. Tace ka bari sai nan da kwana tara mu koma. Jumaa ta sama kenan, mu sami albarkar Jumaa. Yayi dariya to naji amma please kafin nayi wanka abinci....tana tafiya tace Jumaa 1st April tayi kwafa.