← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 67

Sashe 6

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana tura ledar tsamiyar birin a jaka taga mota ta yo kanta. Hantar cikinta ta kada ta rasa ina zata yi ma. Gabadaya ta rude kafafunta sun kasa daukarta. Da kyar Hamza ya iya tsayar da motar bayan ya shigar da ita cikin wani ruwa da ya kwanta a gefen titi. Har fuska ruwan ya watso wa Zuhra sannan ta zame ta fadi a zaune cikin ruwan.

Karshen bacin rai kam taji shi a lokacin. Musamman da ta hango mai tukin da yaro suke kicikici da sitiyarin motar. Da sauri Hamza ya tura Khalifa wanda yake ta kuka cinyar Izzatu ya sauke glass din motar yana duban Zuhra. Leko da kansa yayi zai bata hakuri sai dai akayi rashin sa'a kwalliyar fuskarta ta bashi dariya. Izzatu da Tala ma da suke cikin motar sai da suka yi saboda yadda lebenta ke daukar ido. Ita kuwa Zuhra haushi ya kara kamata. Hamza ya dan daure amma fuskarsa dauke da murmushi yace don Allah kiyi hakuri kinji. Yaro ne ya rike sitiyarin Allah Ya kiyaye ban tabaki ba dai ko? Zuhra ta tsuke baki ban sani ba...don tsabar wulakanci kayi min wanka da kwatami sannan ka wani kame a mota kana tambayar ko ka tabani. Hamza ya dan sha kunu jin abinda ta fada yace to naji kiyi hakuri don Allah. Ya zaro kudi a aljihunsa ya mika mata dubu biyar. Gashi ki sayi sabulu. Ganin ya tayar da motar ta kama hannun gefen inda yake zaune ta soma masifa. Amma kai baka da mutumci wallahi...tana kallonsa tana kallon kudin. Kudinka me zasu min. Malam ka fito ka duba ko naji ciwo ka kaini asibiti. Izzatu ta dan leko kiyi hakuri kinji, kinga yaron da ya jawo, ta dungure Khalifa. Maganar Zuhra ta bawa Hamza haushi yace idan bazaki karbi kudin ba sauri nakeyi. Kin samu na tsaya zaki rinka yi kin rashin kunya. Zuhra tace anyi din, nace anyi din kuma Allah Ya isa abinda kayi min. Ka wani makale a mota kai mai kudi ko. Yadda take magana ya sake bawa Izzatu dariya. Haka kawai yarinyar ta burgeta. Hamza kuwa harararta yayi sannan cikin fushi ya fito daga motar. Tun kafin ya karaso tsoro ya cika mata zuciya. A gabanta ya tsaya ta daga kai ta kare masa kallo. Tabdijam...da kyar in kanta zai kai kafadarsa ma. Ta hadiyi yawu da kyar. Mutumin duk da bashi da kiba amma dai baya sahun masu rama, gashi da tsaho. Idanunta suka kawo ruwa don kallon da yake mata ba na wasa bane. Idan ya dake ta kuwa ya daki banza. Ya dan rage sautin muryarsa ke kinga nayi kama da sa'anki ne? Ta girgiza kai. Yace to ina baki hakuri sai ki rinka yimin rashin kunya. Izzatu ta dan bude kofa tace babyna ka taho mu tafi kawai. Zuhra ta zaro ido ta kara kallonsa....baby kuma? Katon gardi da kai a kiraka baby. Lallai an cuci kalmar nan al'quran. Ran Hamza ya sake baci ya daga hannu zai mareta. Tace kana tabani zanyi suman karya a wurin nan sai mazan can sun taru. Kuma in fada musu abinda kayi min. Daga kai yayi ya kalli kofar kantin da ta nuna yayi murmushi yace bismillah. Zuhra ta dan ja da baya da gaske nake fa...shima ya kara matsawa gabanta ai ban hanaki ba. Ta tabbatar dai ba wasa yake ba kawai sai tace Allah Ya isa da karfi ta kwasa da gudu.

Binta yayi da ido sannan yayi tsaki. Idan ya sake ganin yarinyar nan sai jikinta ya gaya mata. Shi zata yiwa Allah Ya isa har sau biyu. Yayi kwafa ya shiga mota. Izzatu sai dariya take. Yarinyar kamar wata clown. Ita fa gani take tayi kwalliya karshe ko? Hamza yayi tsaki yanzu duk abinda ta fada min bai dameki ba Izzy sai ki rinka dariya. Tace ai abin naku ne da ban dariya. tayar da motar yayi don idanun Izzatu suna ga yarinyar da ke gudu ba maganar da yake ba. Tana kallo har Zuhra ta fada gidan Faiza....
[9/25, 2:52 PM] ‪+234 803 040 6305‬: AL'ADUN WASU 🗿9

Batul Mamman(Mrs)💖

Tunani ne duk ya ishi Hamza har ya isa gida. Tabbas ko makaho yasan kasarmu tana cikin matsi a wannan yanayin da muke ciki. Sai fatan Allah Ya kawo mana sauki. Amma a haka duk shekara basa rasa dalilin yin taro a gidansu. Duk da hakan ba ra'ayinsa bane tun farko amma ya goyi bayan Izzatu akan duk abinda take yi. Dole ne kuma ya nuna mata kuskuren rayuwar da suka daukarwa kansu ko don inganta tarbiyar 'ya'yansu. Kila mutane suna ta zaginsa bai taba tunanin haka ba sai yau. A haka ya isa gida zuciyarsa duk ba dadi. Izzatu ta gama gyaran dakin yana ta kamshi ita kanta ta yi kyau sosai tace ya shiga yayi wanka.

Inuwa Sakatare ya karanta takardun gabansa yafi a kirga. Yana son sanar da ogansa amma yana tunanin kada ya zama ya nuna rashin damuwa akan lalurar Junior. Daga karshe dai text ya tura masa wanda ke dauke da cikakken bayani dangane da yarjejeniyar dake tsakaninsu da turawan. Kusan minti goma ba reply sai kawai ya kira wayarsa. A lokacin Hamza na wanka. Izzatu na kallo har wayar ta tsinke aka sake kira har sau hudu. Tayi tsaki ta dauka. Bata son abinda zai bata romantic night din da ta tsara musu ita da mijinta. Gashi baya yarda da kashe waya komai dare. Inuwa ya gaisheta ya tambayi jikin Junior tayi dariya kawai tace da sauki. Yace na turowa Oga sako ne nake son tambayarsa ko ya gani. Izzatu tace yana wanka amma zan sanar dashi. Inuwa yayi godiya yace sai da safe. Har ta ajiye wayar ta dawo ta dauka. Tasan halin Hamza kafin ya kwanta sai ya duba sakonnin wayoyinsa mai bukatar reply ya tura. Ita kuwa daren yau na tunawa da ranar aurensu ne. Bata bukatar duk abinda zai dauke masa hankali. Duba sakonnin mail dinsa tayi duk ta bude su a matsayin an karanta haka ma na whatsapp. Text kuwa banda na Inuwa duk sauran na etisalat ne da mtn. Gabadaya ta hada ta goge harda na Inuwan saboda daga farkonsa taga an rubut RANKA YA DADE YA JIKIN JUNIOR......iya nan ta gani ta goge ta saka masa wayoyin a chaji. A tunaninta text din dubiya ne. Da ya fito ya duba wayar babu wani abu mai mahimmanci sai kawai suka yi shirin kwanciya....

Zuhra ta dawo daga islamiyya tana ta zumbura baki. Sallamar ma a ciki ciki tayi. Umma tace waya taba uwar masu gida? Jakarta ta jefar a kan tabarma ta cire hijabin ta kwanta. Umma yunwa nake ji kamar naci babu. Baba ya fito daga bandaki da buta a hannu yace Allah Ya rabamu da babu. Shine zaki wani kwanta kina turo baki. Ji don Allah kamar ba mace ba. Kin wani kwanta a kasa. Ji gaban rigarki ma kamar manja. Ya taba kitsonta da tsagar har ta bace don tsufa...yanzu kan nan yaushe rabonsa da ki wanke shi? Wai wa zan samu ya aureki a haka? Ba kwakwalwar karatu ga rashin jure yunwa. Gaki ba wani kyan azo a gani ba. Da nayi kudi ne ma sai a aureki ko don nauyin aljihuna. Zuhra ta soma shura kafafu Umma kinji Baba ko? Ai dai kai na biyo wallahi. Yace wa? Ni? Haba yarinya don kinzo na fara tsufane. Tambayi Ummanki lokacin da nake matashi yadda mata ke bina. Umma tana wanke shinkafa tana musu dariya. Zuhra tace har tafiyarmu iri daya fa. Baba yasa dariya ai kuwa da kinji kunya ace budurwa kamarki tana tafiyar maza. Maganin farinjini zan nema miki. Tunda karatun yaki sai ayi auren. Maganarsa ta sake tunzura Zuhra har ta soma hawaye tace Umma ina kama dake ko? Umma ta rike baki tace ta ina? Ni duk gidanmu babu mai kyau na. Ke kuma da Babanki kike kama. Kaga Sima yar gidan Malam Basiru. Dariya sosai suke yi mata tana ta kuka. Ta tashi ta shige daki. Baba yace kinga kin batawa uwata rai ko. Umma tace don na tayaka?. Amma maganar gaskiya rashin saurayin Zuhra na damuna. Maikifin bakin layi ne kawai yake zuwa kuma tace bata son shi. Baba yace nima abin na damuna. Bata son kula da tsaftar jikinta ne kuma da laifinki. Umma tace akan ta tsefe kanta har dukanta nayi. Lokaci na bata zuwa wani satin tana bacci zan sa mata almakashi kowa ya huta. Baba yace wallahi ban yarda ba. Da nayi saa ta gado irin gashinki mai dan tsaho kuma sai ki aske. Ba gidan Faiza zata ba bayan azahar...Umma tace can zata je. Baba yace to kice ta tafi da kaya ko biyu ne ta kwana. Kinsan halin Faiza ko taki ko taso sai tayi tsifar nan. Zuhra na jinsu daga daki ta leko ta taga na fasa zuwa gidan Anti Faizar. Umma tace kunfi kusa ai.

Sai da ta gama cin abinci ta sha ruwa sannan ta dauko hijab ta saka da kullin kayanta a dankwali tace Umma zan tafi. Baba ya harareta a haka Zuhra... Islamiyya fa kika je ko wanka bakiyi ba ki ka saka kaya. Ji hijab din ko guga babu. Ke ko irin gayun mata baki iya ba. Ki dan saka kayanki a yar leda zaki kulle a dankwali. Yarinyar nan da a kauye muka tashi bana jin zaki taba wayewa. Gaskiya Umman Zuhra bakya kyauta min. Kin bar min yarinya ta zama borar karfi da yaji. Umma tace ai kana gidan kana ganin yadda nake fama da ita.
Chapter 6 · 0% Book details