← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 67

Sashe 44

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

******
Da wata irin tafiyar jan hankali Izzatu ta shigo falon Hamza. Da tayi niyar kiran sunansa sai ta fasa kada ta bata surprise dinta. A hankali ta bude kofar dakin ko bacci yake yi kada ya tashi sai ta kwanta a kusa dashi. Labulen ta daga ta dan tura kai......tamkar wadda taga wani mugun dodo haka tayi saurin sakin labulen ta koma da baya a hankali. Dakinta ta tafi kai tsaye ta wuce bandaki ta wanke fuskarta da sabulu. Ta fito ta tsaya a gaban mudubi tana mayar da numfashi a wahale. Lallai Izzatu, yau da abinda kika gani gaske ne kila sai kin shiga coma. Shine abinda ta fada a zuciyarta sannan ta sake sabuwar kwalliya ta fita. Tasan ba wani abu bane dama ance abinda kafi so ko kafi tsana wani lokacin sai kaga yana maka gizo. In ba haka ba me zaisa taga hannuwan mace sun rungume mijinta Hamza suna kissing juna irin haka.

*******
Zuhra ke kokawa da Hamza ya dage sai ta cire rigarta tasha iska. Kamar tayi kuka tace Ya Hamza, bama Yaya ba, Baba Hamza kayi hakuri mana. Yace ni gaskiya Inna Fatima bazan hakura ba. A haka kike son nan da wata taran na kaiki asibiti haihuwa. Yana jan rigarta itama tana ja suna ta dariya.

*****
Sake komawa dakin nasa Izzatu tayi sai dai wannan karon tun daga falon take jin dariyar Hamza da wata mace. Zuciyarta ce tayi wani mugun bugu kamar zata ballo kirjinta. A fusace ta banka kofar dakin ta ga wace karuwar Hamza ya kawo gidansa.

Karar kofar ya mayar da hankalin Hamza da Zuhra kofar dakin. Izzatu ce ta shigo tamkar wata zakanya idanunta sun kankance babu abinda ake gani sai tsantsan bacin rai.

Shima Hamzan a fusace ya tashi da ya ganta. Shaf ya manta tace yau zata dawo amma duk da haka hakan bai zama dalilin da zata shigo masa daki babu sallama ba. Ita kuwa Zuhra bargo taja ta suturta jikinta saboda rigarta ba mai kauri bace. Cikin masifa Izzatu tace Hamza me zan gani haka? Karuwa har cikin gidan aure, har kan matrimonial bed(gadon aure)din mu. Daurw fuska yayi shima yana fadan...Izzy a wane dalili zaki shigo min daki babu sallama.

Heyyyy! aa'a! maza har abada bakwa rabo da abin mamaki. Na kamaka da karuwar kace zaka min wa'azin sallama. To ban karba ba sai ka kama wata hanyar borin kunyar ba wannan ba.

Kallonta ta mayar ga Zuhra ta daka mata tsawa ke kuma tsohuwar 'yar bariki wallahi ni da kike gani bani da mutumci akan mijina. Sai kinyi nadamar hada jiki dashi. Zaki sakko daga kan gadon nan ko sai nazo na babballaki?

A gigice Zuhra tayi yunkurin sauka daga gadon tana lullube da bargo hakan ya jawo ta bige gwiwarta da gefen gadon, tana tashi ta soma dingisa kafa. Hamza yayi saurin tareta, Cutie koma kiyi zamanki let me handle this issue. Ya nuna kofa Izzy wuce muje dakinki we need to talk.

Ko sauraronsa bata yi ba ta taho gaban gadon ta kwaye bargon da Zuhra ke ta rufe jikinta dashi. Idonta cike da hawaye tace Hamza buduwar ka samo shiyasa naga har wani jan kafa take yi. Zuhra ta rasa inda zata saka kanta saboda wannan tozarci da Izzatu tayi mata. Bayan Hamza taje ta tsaya saboda tasan ko kadan bai kamata Izzatu ta ganta da wannan shigar ba. Gadon Izzatu ta rinka dubawa Hamza yana mata fada ko daga kai bata yi ba. Ka barni na duba shaidar cin amanar da kayi min da wannan 'yar isakar da take son nuna min ita budurwa ce. Hamza yace Izzy idan baki nutsu kin fita daga dakin nan ba wallahi zaki ga baccin rai.

Jajayen idanunta ta dago tana kallonsa, bacin rai har ya wuce wannan munafukar karuwar da ka dauko daga bakin titi. Hannu ta kai zata janyo Zuhra dake zubar da hawaye a bayan Hamza ya rike hannun tare da zagba mata mari. Shima nasa idon bacin rai yasa sunyi ja yace kada ki sake kira min mata karuwa wallahi.

Izzatu ta dafe kunci ni ka mara Hamza??? To na fada din karuwa matsiyaci....wani wawan marin ya bata wanda yafi na farko. I am warning you Izzy ki kiyaye bakinki. Zuhra matata ce ba karuwa ba. Magana Izzatu taso yi sai dai kalmarsa ta karshe tasa ta hadiye maganar tare da kukan da take yi.

Kunnenta ta dan buga sannan tace me kace Hamza, Zuhra matarka ce? Wannan karuwar ce Zuhra? Ta fada tana nuna ta.

Hamza yace idan ba ita ba ina da wata matar ne bayan ke? Haka kawai kin shigo kina ta bala'i kamar wata mahaukaciya. Ki fice daga dakin nan kafin na saba miki.

Sai a lokacin Izzatu ta karewa Zuhra kallo. Ko da wasa bata ganeta ba da farko saboda ba haka tasan Zuhra ba. Jikinta a sanyaye tayi zaman 'yan bori akan gadon. Ta dago kai a hankali tana kallon Zuhra dake labe a bayan Hamza. Tsakanina da kai Hamza bazan taba yafe maka ba. Ni Izzatu Sunusi zaka yiwa irin wannan cin fuskar? Ka kasheni kuma bazan yafe maka ba. Har gara ace sophisticated prostitute( hadaddiyar karuwa) ka dauko sai nasan cewa gazawa nayi shiyasa ka nemi wadda ta fini amma ZUHRA, HAMZA KWANA DA ZUHRA yana nufin mummunan kaskanci gareni a matsayin mace.

Maganar Izzy ta batawa Hamza rai sosai yace kinga for the last time ki fita daga dakin nan. Kina iya daukan tarayyata da Zuhra duk abinda yazo ranki amma ki sani matata ce ta sunnah wadda all thanks to your stupidity na aureta, kuma nake alfahari da auren. Now GET OUT.

Cikin sanyin jiki Izzatu ta tashi jiri na dibarta ta kalli Zuhra da gabanta ke faduwa. Nayi miki alkawarin barin gidan nan kamar yadda nayi sanadin shigowarki cikinsa. Sai kinyi dana sanin cin amanata kika kawo kanka ga mijina. Nasan ba laifinsa bane Hamza baya iya dadewa babu mace shine kika yi amfani da wannan kika bashi kanki. Bakiyi nasara ba Zuhra sai kin koma inda kika fito domin ni ban daukeki a matsayin mace ba ma.

Hannun Izzatu Hamza ya kama zai fitar da ita ta doke hannun, kada kayi tunanin zan sake bari ka tabani bayan ka taba waccan kazantar. Fita tayi daga dakin babu ko digon hawaye a idonta. Bakin cikin da take ji yafi karfin kuka.

Hamza ya juyo ga Zuhra ya rungumeta, sai a lokacin ta soma kuka da sauti. Bayanta yake shafawa kiyi hakuri Cutie. Duk laifina ne da sakaci har ya janyo haka. In sha Allah Izzatu sai ta koyi mutuntaki a matsayin matata. I love you so much. Rabon Zuhra da ganin wulakanci tun ranar da aka mata April fool. Tayi kusan minti goma tana kuka Hamza na aikin rarrashi. Daga baya ta sake shi ta nemi zaninta ta daura. Hannunta ya riko Cutie ina zaki kuma. Muryarta a dashe tace dakina. Zama yayi ya dorata a cinyarsa. Ki zauna anan kema kinsan bazan iya barinki ki fita a haka ba. Tashi nayi miki wanka....murmushi tayi ta dora kanta a kafadarsa ni bazan yarda kayi min wanka ba. Shima murmushi yayi zaki zo da kanki ne kuma lokacin nima yanga zanyi miki. Rungumeta yayi a jikinsa yana ji tana ajiyar zuciya. A hankali ta tashi bari naje nayi wanka. Ya dan ja hancinta please Cutie na kada kisa komai a ranki kinji ko. Komai zai daidaita in sha Allah zanyiwa Izzy magana. Murmushin yake kawai Zuhra tayi ta fita.

Tana zuwa falo Hamza ya tashi shima wankan yake shirin yi ya jiyo ihunta da salati. A guje ya fito ya ganta a tsaye jiki na bari. Ya Hamza kaga jini.....jini ne digo digo a falon har bakin kofa. Da hanzari suka bi jinin har kofar dakin Izzatu. A kulle Hamza yaji kofar ya soma bugawa yana kiranta amma shiru. Duk ya rude ga Zuhra tana kuka. Sai da ya gaji da bugun ga kofar da karfin tsiya ya tuna yana da spare key. Daukowa yaje yayi ya bude kofar dakin nata. Kwance suka tarar da ita a sume ga jini yana bin kafarta.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 65

Batul Mamman(Mrs)

Gabadayansu ba karamin tashin hankali suka shiga ba. Da sauri Hamza ya koma dakinsa ya dauko wata doguwar riga ya sakata gaba a baya ya dauko Izzatu. Zuhra ma hijab ta burma ta bi bayanshi da gudu da wani mayafi da ta gani a dakin Izzatun domin a suturta mata jiki. A kasa suka tarar da Tala da Nana zata hada mata tea. Idanunta ne suka bi Hamza dauke da Izzatu ga jini a jikinta. Zuhra tace mata ta kula da gidan da yara zasu je asibiti.

Gudu Hamza ya rinka yi cikin dan lokaci suka isa asibitin. Maaikatan asibitin suka yi masa jagora zuwa emergency inda aka bukaci su tsaya a waje shi da Zuhra. Haka suka rinka kai kawo a wurin sai gashi an turo Izzatu akan gado an wuce dakin operation da ita. Hamza ya tambayi wani cikin likitocin menene ya sameta. Likitan yace bari mu fito zamu yi maka bayani. Ku dai kuci gaba da addu'a.

Sun kusa awa biyu a corridor din babu wanda yake iya yiwa wani magana. Kowa da abinda yake sakawa da warwarewa a zuciyarsa. Zuhra ce tayi karfin halin cewa Hamza ko zai yi waya gida ya sanar dasu Hajiya, jikinsa duk a sanyaye yace ya barota a gida. Itama Zuhra tace bata dauko tata wayar ba. Suna magana likitan ya fito yace Hamza ya biyoshi office. Ga mamakin Zuhra sai taji ya kamo hannunta suka tafi tare.

Ko zama basu yi ba Hamza yace don Allah ka fada min halin da take ciki. Likitan yace to ka zauna mana, Zuhra ya zaunar tare da rike mata hannu gam. Likita yace kaine mijinta ko? Hamza ya gyada kai. Ya cigaba da cewa to sai dai kuyi hakuri bamu iya saving din abinda ke cikinta ba.

Bangane ba doctor? Kana nufin tana da ciki ne.

Kwarai kuwa don har ya kusa wata biyu. To matsalar da aka samu shine mahaifar bata da kwari kwata kwata. Don ita da abinda ke cikin tare suka fara fitowa.

A gigice Hamza yace fitowa kamar yaya?
Chapter 44 · 0% Book details