Sashe 38
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallo ta kare masa yana bacci. Tasan jiya ba wani baccin kirki ya samu ba shiyasa ta fita daga dakin a hankali ta rufe masa kofa. Wata mahaukaciyar yunwa take ji kamar anyi mata sata a ciki. A gaggauce tayi wanka ta shirya cikin riga da skirt na atampa ta sauka kasa. Banda breakfast hatta abincin rana su Hamida sun kusa gamawa. Shinkafa da miya suka yi, Adabiyya na gyara salad Zuhra ta shiga kitchen din suka yi mata sannu. Tace kuyi hakuri yau na barku da aiki. Adabiyya tace haba dai aiki, ai tun jiya na kula baki da lafiya sosai. Da asuba kuma Yaya yace baki dade da samun bacci ba. A kitchen din ta zauna cin abinci suna hira.
Har karfe daya babu motsin Hamza tace bari ta duba shi kada ya makara zuwa masallaci. Tana bude kofar dakin ya fito daga toilet da karamin tawul a hannunsa ya daura wani a kugunsa. Juya masa baya tayi tana bashi hakuri. Har inda take tsaye ya karasa ya rufe mata kanta da karamin tawul din. A bayanta ya tsaya ya rungumeta. Ko motsin kirki ta kasa, yayi kasa da kansa ya sauke akan kafadarta. Cutie ya jiki? Ta runtse ido tace da sauki Alhamdulillah. Rikon da yayi mata ne yasa ta tuna yadda ta rinka makale masa cikin dare. Dan murmushi kawai take yi tana jira ya saketa ta gudu. A hankali ya juyo da ita muje ki shafa min mai yana daga cikin lessons dinmu. Alamar kuka yaga tayi ta kasa daga ido ta kalle shi. Ya Hamza kayi hakuri banda shafa mai. Yadda nake jin kunyarka hannuna rawa zai rinka yi fa. Shiyasa nake so ki koya har ki saba ya fada yana jan hannunta. Idan baki shafa min ba kinsan dai zunubi za'a rubuta miki ni babu ruwana. Tawul din da ya dora mata taja ta sake rufe fuskarta sannan ta mika hannu bani man....yana jindadin kasancewa tare da Zuhra. Kamar gaske tasa hannu a cikin man sai yaga ta lakato shi da yawa kamar mai shirin wasan mai. Saurin yin baya yayi...Cutie me zakiyi da wannan man? Sai da tayi dariya sannan tace shafa maka zanyi. Haba ke kuwa, wannan ai man da zan shafa a wata biyu ne kika lakata. Dan kadan ta rage tace to wannan yayi? Yace kinga jeki kiyi wani abin kafin na shirya. Idan kika shafa min wannan man ai ko Takitse bazata gaya min narkewa ba. Dama haka take so ta cire tawul din ta ajiye sai ta rufe idonta wai kada ta ganshi ba kaya ta mika hannu ni dai sai na shafa maka ko a fuska ne saboda kada ladan ya wuce ni. Da gaske take matsowa kusa dashi yana yin baya yana bata hakuri. Kamar zugata yake kara yi tana ta binsa suna zagaye dakin tana dariya. Da ya gaji yace idan baki fita daga dakin nan ba Cutie zan daukeki muje mu sake yin wanka. Bata jira ya maimaita maganar ba ta fita tana dariya. Shima dariyar yayi ya soma shiryawa.
Karfe uku da kwata suka ji horn din mota alamun su Khalifa sun dawo. Murna a wurin Zuhra tamkar 'ya'yan cikinta ne. Yadda take son babansu haka suka shiga ranta su ma. Dreban kamfaninsa ne ya daukosu, yana tsayar da motar suka fito suna ta ihu suna kiran Daddy. Su biyu suka shigo a guje suka rungume shi tare da yi masa kiss a goshi shima yana yi musu. Junior ya rugo wurin Zuhra da ta fito daga kitchen da sauri. Dama tukin tuwo yasa bata fito da wuri ba. Kankameta yayi yace I miss you. Duk rashin turancinta tasan ma'anar wannan kalmar shiyasa taji dadi sosai. Bakinta kamar gonar auduga tace I miss you too Junior. Khalifa ya soma rigima Daddy kaji Zuhra bata yi missing dina ba. Kuma ni har nafi Junior missing dinki. Har sweet na rage miki fa. Zuhra tace yi hakuri kai babba ne shiyasa na fara fadawa kaninka. Hamza duk kunya ta isheshi da Khalifa yace mata Zuhra. Basu taba tunanin gyara musu ba da suke fada a da. Da dan borin kunya yace kada na sake jin kun kirata Zuhra. Junior yace to me zamu fada? Adabiyya ce ta bashi amsa, ku rinka kiranta Maama. Khalifa ya wani rungumeta don ace yafi sonta yace Maama I miss you. Tace nima haka tana dariya. Zuciyar Hamza kamar an masa albishir maidadi ganin yadda yaransa suke son Zuhra.
Tala ce ta shigo da Nana a hannunta tana jan jakar kayansu. Har wani tsalle ta soma yi da ta hango Hamza. Ajiyeta Tala tayi da dan gudunta ta taho zata rungume Hamza sai ta kula da Zuhra mai bata abinci. Kwana tayi ta barshi da hannu a bude ta tafi wurin Zuhra ta rike mata kafa. Fuskar nan babu alamun wasa tace zanci tuwo. Hamza ya soma salati ana dariya. Yanzu duk gidanmu ki rasa wanda zaki gada sai Hamida mai cikin zani da babarki Zuhra. Hamida tace haba Yaya don Allah a gaban yara kake fadan wannan sunan. Adabiyya da Zuhra sai dariya suke yi. Hamza yace gashi nan ta gado ki a cin abinci da kiba. Ji yadda take gudu duk jikinta na juyawa kamar wata 'yar shekara hudu. Zuhra ta dauki Nana tace kai dai kawai kaji haushi 'yata tafi sona shine kake hucewa a kanmu. Tala ta gaishe su sannan ta wuce ciki da kayan.
Ana la'asar Hamza ya fito zai tafi masallaci su Junior suna ta wasa a falo. Zuhra tace Junior, Khalifa Daddy zai tafi masallaci fa. Khalifa yace mun gani Daddy bye bye. Cigaba da wasan suka yi Zuhra tace kuzo muje kuyi alwala kada ya tafi ya barku. Maza a masallaci ake so su rinka sallolinsu. Junior yace Zuhra sai kuma ya rike baki... au Maama yau sallah babba ce ko sallah karama da zamu je masallaci? Allah Yasa su Hamida sun tafi yin alwala da kunyar da Hamza zaiji sai tafi wannan. Shi yasan bai taba damuwa da nunawa yaransa zuwa masallaci ba sai lokacin Idi. Zuhra ta kalle shi bari muyi sauri suyi alwala sai ku tafi. Ai dolensa ma ya jirasu tunda kanwar bayansa ce take fada masa abinda ya kamata. Yaran kuwa sai murna suka shirya suka bi babansu.
Tala ce ta gama ware kayansu ta shiga kitchen din Izzatu zata dora abinci. Hamza na falon yaji motsin kwanuka ya tura Khalifa ya kirawota. Me kike yi a kitchen? Sai da ta durkusa daga gefe sannan tace abinci zan dora. Yace abinci wane iri? Tana dan susar kai tace Maman Khalifa tace idan mun dawo na rinka yi muku girki kai da yaran. Ransa a bace yace kada ma ki soma. A wane dalilin zaki yi mana girki bayan Zuhra na nan? Kema idan ta dafa zata baki so kada ki yi wani girki indai ba ta nemi ki tayata ba. Kuma ki rinka yi mata wanke wanke da sauran ayyuka idan ta bukata. Tala bata iya boye mamakin fuskarta ba. Hamza yace ko akwai wani abu ne? Tayi saurin mikewa a'a.
Dayake Hamza yace ana magariba zasu je mayar dasu Hamida gida shiyasa Zuhra tayi girki da wuri. Tuwon shinkafa tayi da miyar agushi. Tala ta shigo kitchen din yana ta kamshi tana tambayarta ko akwai abinda zata tayata Zuhra tace babu komai. Bata manta kashedin da Izzatu tayi mata ba akan Tala. Khalifa ya shigo yace Tala ina sabon takalmi na zan nunawa Maama. Zuhra tace Khalifa kaga Tala babba ce ku rinka ce mata Anti Tala ko. Yace dama Mummy ce tace maiaiki ce ita ba sai mun ce Anti ba. Zuhra tace idan kana fada har aljanna zaka shiga. Da murnarsa yace bari na fadawa Junior ya fita. Tala tace nagode sosai saboda taji dadin yadda Zuhra ta darajata. Murmushi tayi ta dauki abincin maigadi zata mika masa Tala ta karba tace bari na kai masa.
Tana zuwa inda yake zaune kan benci yace yau kun kusa saka min hawan jini. Tala tace saboda me? Ya gyara zama, wato ina ganin motarku gabana ya fadi nace Hajiyar ta dawo zamu koma gidan jiya..yunwa salamu alaikum. Tala tayi dariya sannan tace ai ni gidan mamaki ya bani. Dan bani labari meya faru bayan tafiyarmu. Maigadi ya bata labarin yadda Zuhra ke kyautata masa ga abinci a wadace. Tala ta bude flask dinsa taga tuwon yadda zaici ya koshi. Nan ta bashi labarin yadda suka yi da Izzatu kafin ta taho. Maigadi yace bar marowaciya....sai ya rufe baki kada wani yaji. Ai ki kyaleta kawai ni nan kullum addua nake yiwa Hajiya amarya Allah Ya kawo kazantar daki. Tala tace amin amin ai yanzu yallabai yayi aure. Wai har Anti tace su Khalifa su kirani.
Gabadayansu suka shirya suka mayar dasu Hamida gida. Yaran sai murna sunga kakanninsu. Zuhra ta tafi gaisawa da Hajiya a dakinta ta bar Hamza a dakin Mama. Hamida ta dauko kudi ta nunawa Maman tace kinga Yaya ya bamu dubu bibbiyu ita kuma Anti Zuhra ta bamu kayan kwalliya. Mama tace Allah Ya saka da alkhairi Yaya mungode. Mamaki ne ya kamashi domin kuwa bashi ya bawa Zuhra kudin ba. Bayan fitar Hamida kasa shiru yayi ya fadawa Mama. Mama tayi murmushi tace Yaya Allah ne Ya hadaka da yarinyar nan domin ta tayaka gyara dukkan abinda ka bata. Har abada tsakaninmu da ita sai addua da fatan alkhairi. Abinda take yi maka shi ake bukata daga duk matar kwarai mai neman rahmar Allah. Cike da farinciki Hamza yake kara jin son amaryarsa. Mama tace idan Izzatu ta dawo sai kayi kokari ku zauna kayi mata nasiha. Idan da tarbiyar gidansu a halayyarta harda sakaci irin naka. Baka taba kokarin hanata ba a da sai ma biye mata da kake yi. Yanzu sai sauke nauyin dake kanka na yiwa iyalinka tarbiya irin ta addini.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: [10/4, 12:59 PM] +234 806 970 6638: AL'ADUN WASU 59
Batul Mamman(Mrs)
A gajiye Izzatu ta isa gidan iyayenta a cikin garin Abuja. Bayan ta sallami mai motar da tayi shata tun daga Kaduna maigadinsu ya biyota ciki da jakar kayanta.