Sashe 49
Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kujera ya tura mata ta zauna sannan ya hada mata tea. Bayan ya gama ya dauko kwai guda uku a fridge Zuhra tace biyu zata ci. Yace shima zai ci. Tana kallo ya dora mai ya dauko maggi da cokali. Tana jira ya dauko roba ya fasa a ciki sai kawai taga ya fasa a cikin frying pan din. Da sauri ta taso Ya Hamza wace irin suya ce wannan? Bai kula ta ba ya barbada maggi kadan a saman ya dauko plate. Zuhra sai girgiza kai take yi taga ya juya kwan daya barin ma ya soyu sannan ya juye a plate. Kinga suya ba irin taki ba, muje falo kici ki ji.
Bata yarda zata ji dadin suyar tasa ba sai da ya tura mata a baki. Sai da cinye na bakinta tayi murmushi tace da dadi....Hamza ya dauke plate din to kinci rabonki. Rokonsa ta fara yi taga yaki kawo mata, wuri ya samu ya zauna yana ci. Ta zauna ta soma kukan karya sai ya kawo mata. Tare suka karasa ci suna hira. Suna gamawa ya kulle gidan yace to sai bacci.
A kofar dakinta tace masa zata je tayi wanka. Yace ke da kika gaji, muje ki dauko kayanki a dakina zaki kwana. Duk abinda zata bukata shi ya dauko mata sannan suka tafi dakinsa.
Kai tsaye ta shige toilet zata yi wanka. Ta gama tara ruwa mai zafi saboda hannuwant da kafada duk sunyi tsami tana son gasa su taji an bude kofar. Wani irin ihu ta saka ganin Hamza a tsaye daga shi sai dogon wando. Da sauri yaje ya toshe mata baki da nasa. A haka ya karasa cire mata riga. Kuka take masa kamar wadda zai yanka yayi murmushi kin fiye tsoro Cutie. Ni taimakonki nazo yi kike min kuka.
Hannunta ya kama tana ta harararsa ya sakata a cikin bahon sannan ya dauko karami tawul ya saka a ruwan zafin ya danna mata a kafada. Wani ihun tayi ta mike zata gudu ya riketa sosai. Kinga idan baki zauna ba matseki zanyi. Ki cigaba da hararata sai idanunki sun fado.
Kunya taji ta dena harararsa. Kamar mai rada tace Ya Hamza ka dan rufe ido mana.
Ki dena magana ba'a son surutu a toilet. Daga nan duk kauce kaucenta haka ya gasa mata jiki sosai sannan yayi mata wanka. A katon tawul ya nadota ido duk sunyi ja saboda kuka. Da kansa ya shiryata sannan ya dauko wata katuwar shirt dinsa ya saka mata. A bakin gado ya zaunar da ita shima yaje yayi wankan ya fito. Har ya gama shiryawa Zuhra na tura baki. Cak ya dauketa suka kwanta ta janye jikinta can gefe.
Haka kawai kayi min wanka kamar wata yarinya karama. Ni bazan sake wanka a dakinka ba.
Yana ji tana mita yayi dariya...zo na baki hakuri kinji my cute baby.
Matsawa tayi gefe yasa hannu ya janyota ta fado jikinsa. Fuskarta yake shafawa da hannunsa daya yace duk abinda nayi miki kiyi hakuri harda wanda zanyi miki ma.
Tace wanne kuma.....bai barta ta karasa maganar ba ya katseta ta hanyar kissing dinta da nuna mata soyayya irin wadda ya jima yana fatan zuwan ranar da zai nuna mata. AL'ADUN WASU 68
Batul Mamman(Mrs)
Babu irin yadda Hamza baiyi ba domin ya tashi Zuhra da asuba taki tashi. Ganin yana neman rasa sallah yasa ya rabu da ita yaje yayi wanka ya tafi masallaci. Niyarsa idan ya dawo sai ya sake tashinta.
Tana jin sautin rufe kofar ta yaye bargon jikinta ta tashi jiki babu kwari. Abinda Ya Hamza yayi mata ne yasa ta tashi da wata irin kunyarsa, da wane ido zata sake kallonsa ma. Shiyasa tayi shiru tamkar bata jinsa lokacin da yake ta kokarin tashinta.
Dama ita bata iya jin ciwo ba ta rinka raki da koke koke kenan to yau an sami maidalili. Da kyar ta iya zama cikin ruwan zafi sannan daga baya tayi wanka ta fito. Don kokari harda dan fesa turare tunda an zama 'yan gayu sannan tayi sallah. Zama ta cigaba tana azkar bayan ta idar taji har taji alamun antaba kofa.
Jiki na rawa ta tashi ta jefar da hijab dinta ta haye gado. Har kanta ta rufe ta koma ta kwanta ko numfashin kirki bata yi.
Dariya ta bawa Hamza da ya kula tabbas tayi sallah bayan fitarsa. A gefenta ya zauna yana mata magana a hankali.
Cutie bazaki tashi mu gaisa ba?
Shiru tayi babu amsa sai alamun tana kuka da yaji.
Da kyar ya iya budeta ya kwantar da ita a jikinsa. Yace dama matsalar irinku kenan wadanda suke tashi babu wa babu kani. Kunfi kowa iya shagwaba. Yanzu duk kukan da kika yi jiya bai isheki ba shine zaki tashi da wani sabon.
Tashi tayi suka hada ido tayi saurin juyar da kanta, to ba kai bane ina ta......
Yace na fa baki hakuri tunda wuri kuma me ya rage? Hmmm ko baki gane lesson din bane da kyau. Ya fada yana kashe mata ido.
Murguda baki tayi ni bance ka koya min irin wannan ba.
Eyye, Cutie ashe baki dena tsiwa ba. Lallai ya kamata a maimaita karatun ko zaki fi dauka. Irin wannan juya baki kamar idan na fara kissing kada na saki.
Ido ta rufe ta kwanta a jikinsa...ai nasan Ya Hamza yana da kirki bazai kara sani kuka ba ko. Don Allah kayi hakuri na dena yi maka tsiwa.
A hankali yace gaskiya banyi miki alkawari ba. Ke ko irin addu'ar da maza ke yiwa matansu da safe irin haka baki bari nayi miki ba sai korafi. Tashi zaune kiji wannan kwanciyar da kike yi a jikina sake kashe min jiki kike yi.
Yadda yake magana yasa da saurinta ta tashi harda matsawa gefe. Hamza ya rinka dariya...matsoraciya kawai. Sannan ya kama hannunta...nagode miki Allah Yayi miki albarka Ya bamu zuri'a dayyiba. In sha Allah Zuhra zan rike ki amana kuma zan so ki fisabilillah. Idan har nayi miki wani abu ba daidai ba ina so ki rinka fada ba ki barshi a ranki ba muzo muna samun rashin fahimtar juna. Naso ace kinyi wanka a gabana dazu domin nasani ko akwai gyara duk da nasan matar tawa tana da ilimi. Amma kamar yadda naji wata malama Ummi Aisha tana fada yana da kyau duk miji ya san ko matarsa ta iya tsarki.
Zuhra dai kunya duk ta isheta ta sunkuyar da kanta kasa. Hamza yace ina jinki fada min yadda kika yi ko muje nayi miki da kaina. Sanin ba karamin aikinsa bane yin hakan yasa ta soma yi masa bayani a hankali kamar wadda aka kamawa baki. Ya gamsu sosai da amsar da ta bashi yace to yanzu me ya rage?
Zuhra tace naje kitchen nayi girki ko don asibiti...tana magana ta tashi da sauri saboda su Junior da ta tuna.. .Ya Hamza su Khalifa yau bazasu school ba? Tashi ka kaisu gashi har bakwai da kwata.
Murmushi yayi...kinsa miji a daki kina masa dadin baki ba dole ki manta da yaranki ba. Ta tura baki ta fara jan hannunsa, don Allah ka tashi kada su makara yau. Yace to laifin waye? Ko kadan bai damu ba harda kishingida akan pillow Zuhra tana ta kokarin tayar dashi.
Gajiya tayi ta hakura bari naje kasa nasan Tala tayi musu wanka. Don Allah ka taso kaji Ya Hamzana. Har wani fari take masa da ido duk don ya tashi. Sai da ya bari taje kofa sannan ya kirata. Da sauri ta dawo amma hankalinta yana kan yaran da tasan tun waccan alhamis din bayan dawowarsu daga Kaduna suka fara jarabawa.
A gabansa ta dan durkusa tana jiran taji dalilin kiran. Bakinsa ya nuna mata...yau bamu gaisa ba. Idan kina so na tashi kizo mu gaisa. Kuma ki dena tafiya da sauri sauri kafin kizo kina min raki anjima.
Kallonsa kawai take yi yadda yayi kwanciyarsa kamar bai damu da zuwan nasu makaranta ba. Bakinsa ya sake nuna mata tace jiya fa kaji min ciwo har ya kumbura ko ka manta? Dariya yayi ....you are not serious, duk abinda kika yi da bakin nan jiya sai yanzu zaki tuna da ciwo. Ko dai kiyi abinda nake so ko yaranki su zauna a gida yau.
Da sauri ta fada jikinsa saboda tana hangowa su Khalifa makara sannan ta hada bakinta da nasa. A hankali Hamza ya rinka janta har ta saki jiki. Da kyar ta iya tuna masa su Khalifa...yace don't worry sun gama exams jiya so bazasu school ba sai ranar friday da zasuyi class party. Ta dan daki kirjinsa amma shine....bata sami damar karasa maganar ba ya katseta da wani salon soyayyar tasa.
****
Sai shadaya saura ta samu Hamza ya kyaleta ta fito. Wanka ta sake yi ta saka wani lace dinta mara nauyi. Dinkin yayi mata kyau riga da zani tayi kwalliya sai kamshi take yi. Dakinsa ta fara shiga ta same shi zaune akan gado da laptop bashi da niyyar tashi. Ya dago mata hannu alamun ta je wurinsa...Cutie kinyi kyau. Har nan nake jin kamshink mai dadi. Murmushi tayi a kunyace tace ina daga nan Ya Hamza. Ni yanzu ko hannunka tsoron tabawa nake yi. Yana daga zaune ya rinka dariyar maganarta. Ka fada min me zaka ci ni yunwa nake ji. Kansa ya kada irin ya zama abin tausayi tunda taki zuwa. Zaki kawo kanki ne yarinya. Yanzu dai ki hada min tea kuma idan akwai sauran tuwon jiya ki dumama min.
Bata jima ba ta kawo tea din falonsa da tuwon suka ci sannan tace zata dora abincin rana. Rabin cin abincin duk Hamza ke tsokanarta tana ta sunkuyar da kai. Can tace ni har kunya nake ji ba'a kai abincin safe ba asibiti kuma duk laifinka ne. Ya dauke kai su Mama sun aika shiyasa kika ga ban damu ba. Abincin ranan ma kiyi wake da shinkafa amma da manja shi nake sha'awa yau. Zuhra tace to abincin asibitin fa. Ya dan sha kunu, suma shi zasu ci ko akwai matsala ne? Zuhra tace babu, sannan ta kwashe kwanukan ta sauka kasa. Amma a zuciyarta tana tunanin yadda mara lafiya zata ci wake da shinkafa da mai duk da Izzatun ta fara cin abinci.