← Book details Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 67

Sashe 40

Al'adun Wasu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake matsowa tayi ta dora masa littafin Khalifa akan cinyarsa. Na kusa minti shabiyar na kasa gano kan aikin nan. Ina tsoron fada masa ba daidai ba yaje yaci zero. Hamza yayi dariya ai kuwa da ya bazaki a duniya yace Maama bata iya homework dinsa ba. Littafin ya duba verbal reasoning na 'yan nursery three. A wata takarda duk ya rubuta amsoshin ya bawa Zuhra taje ta koyawa Khalifa kamar ita tayi. Suna gamawa tasa suka yi shirin bacci kowa yayi fitsari suka kwanta. Ba jimawa suka yi bacci. Kasa ta sauko dibar ruwa saboda Nana sai ta kula Hamza na cikin falonsa har lokacin bai kwanta ba.

Sallama tayi ta shiga yasa computer da takardu a gaba yana ta aiki. Da yaji motsinta ya dago kai suka hada ido ta sakar masa murmushi. Doguwar rigar bacci ce a jikinta mara kauri ta daura zani a sama har kirjinta , sai hula a kanta. Hamza yace maman yara me ya sauko dake? Tace ruwa na manta ban daukarwa Nana ba. Da hannun yayi mata alama ta karaso gabansa. Tana zuwa yasa hannu ya kwance zanin dake daure a kirjinta. Cutie bana son daurin kirji. Kunya ce ta kamata saboda rigar bata da kauri ta fara shirin fita ya rike hannunta ya zaunar da ita a kusa dashi. Tun yanzu kin dena damuwa dani saboda yara sun dawo ko? Irinku ne masu mayar da miji dan kallo da kun haihu. A haka ma kina shareni ina ga kin haifi naki. Zuhra ta sha kunu Ya Hamza nufinka ni ba 'ya'yana bane. Ai ko baka fada ba na sani amma a yadda na daukeka dan uwana dole naso 'ya'yanka, ko kara ai kayi min naji dadi. Sarkin kuka tana magana ta soma hawaye. Hamza duk ya rude, ba haka nake nufi ba Cutie ki dena kuka 'ya'yanki ne mana. Ta share hawaye ba wani nan, don kaga ina kuka ne kace nawa ne. Rungumeta yayi sosai a jikinsa, duk abinda kika yi yana sani farinciki da jindadi Cutie amma bazan juri kukanki ba sai ya kara min damuwa.

Idanu sharbe da hawaye ta dago kai tana kallonsa. Ya Hamza indai kana so na dena kuka sai ka karbi shawarar da zan baka yanzu. Lallai ma yarinyar nan dama kika samu shine kike kuka mara dalili don ki fake ki fadi abinda ke ranki. Dariya tayi tana share hawayen, ya akayi kayi saurin ganewa don Allah? Amma da gaske banji dadi ba sosai don nasan dai wasa kake yi ne. To ina jinki mecece shawarar taki? Zuhra tace dazu na kula kamar kana cikin damuwa. Hamza ya girgiza kai anya Cutie baki da alaka da sarkin mayu. Yarinya duk yadda na boye abu sai kin gane. Dariya tayi sosai sannan tace to Ya Hamza idan ban gane kana da damuwa ba ai babu amfani a zan tare. Kasan ina yin saka ko? Yace Baba ya fada min. Zuhra tace to idan na hau sama zan dauko kaga irin rigunan da nake yi. Mijin Anti Faiza ya taba samar min nayiwa 'yan wata makaranta. Duk da ba babba bace amma akwai riba. Idan zaka iya ka nemo mana makarantu pravate masu dan tsada ko zasu bani kwangilar sakar rigunan sanyi na makaranta. Idan nayi kaga zamu sami wata hanyar ta shigowar kudi kafin ka gama aikin kwangilarka a biya ka. Zuhra bata san yadda take raunanawa Hamza zuciya da kalamanta da kaifin tunani ba. Yace Cutie ban fada miki matsalata don ki tausaya min ki taya ni neman kudi ba. Tayi dan murmushi Ya Hamza na tabbatar ba fada min kayi ba saboda naji dadin labari. Kullum ina tayaka addua Allah Ya saukaka maka halin da kake ciki, to tunda Allah Ya bani iko sai na taimaka maka da abinda na iya kafin lokacin rabuwarmu. Ya Hamza nima fa ka taimakeni, da taimakonka na san na kula da jikina kamar kowace mace batare da ka nuna min kyama ba. Don Allah ka bani wannan damar nayi maka wani abu. Nan gaba kila ko zumunci bazamu sami damar yi ba idan nayi aure.

Tashi Hamza yayi ya tasheta tsaye yana kallonta cike da tsantsar kauna. Cutie nima kin taimakeni da abubuwa da dama ciki harda gyaran tarbiyar su Khalifa. Kada ki wahalar da kanki a kaina. Hawaye ne yake wanke mata fuska tace don Allah ka bincika ko za'a sami masu bani aikin. Wallahi na iya sakar sosai. Hannu Hamza ya mika zai janyota jinkinsa sai ya fasa, yanzu ina tabaki zaki ce wayon tabaki nake yi. Kinyi min izini na rungumeki?

Rigar jikinta ta kalla sai taji kunya ta sunkuyar da kai. Ya dan leka fuskarta please Cutie. Kai ta gyada tare da rufe fuskarta da hannuwanta. Hamza ya rage tazarar dake tsakaninsu ta hanyar rungumeta a jikinsa sosai yana mayar da numfashi. Bai san inda zaisa son Zuhra a ransa ba. A hankali yace kin yarda bayi kissing dinki please? Don kunya ji take wani abu na yawo a cikinta ta kara sunne kai a kirjinsa. Ya Hamza kunyarka nake ji. Ya dago kanta a hankali da hannunsa daya. Ko na minti daya kawai Fatima. Bai bari ta sake sauke kanta ba ya hada bakinsa da nata. Ita dai sai yadda yayi da ita kawai. Dukkansu a bakuwar duniya suka tsinci kawunansu. Ko da ya saketa bai dena kallonta ba yace Cutie ko ban sami school din ba bazan taba mantawa da wannar ranar ba. You hold a special place in my heart. Hamza yana godiya da dukkan abinda kike masa na kyautatawa. Ita dai bata iya magana ba ta dauki jug din ruwa ta haye sama ta barshi yana murmushi.

**********

Kwayoyin guda hudu ne a hannunta da kofin ruwa. Zuciyarta tana dan yi mata wasiwasi sai dai gaskiya bazata iya yarda ta kara haihuwa ba. Wadannan ukun sun ishesu. Tun kafin ta hadu da Hamza take da ra'ayin 'ya'ya biyu kawai. Rufe ido tayi ta watsasu gabadaya daya. Idan cikin ya zube sai ta fadawa Hamza da iyayenta bata ma san dashi ba. Tana sha ta dauki waya ta kira shi. Lokacin Zuhra bata dade da barin falon ba. Hira sosai suka yi yana fada mata yadda yayi missing dinta. Har zuciyarta Izzatu tasan bata kyauta masa ba amma tasan idan ya gane da cikin nan tilasta mata zaiyi sai ta haifa. Sai da suka gama hirarsu ta masoya ta gyara kwanciya tayi bacci. Karfe biyar da rabi wani matsanancin ciwon ciki ya tasheta. Tana kunna fitila taji danshi a inda take kwance. Hannu na rawa ta bude bargon taga jini ne sosai a wurin. A razane ta kwalla ihu MUMMMMM.
[10/11, 2:27 PM] Mariya u madara: AL'ADUN WASU 61

Batul Mamman(Mrs)

Kamar daga sama Raliya da Dad dinsu Izzatu suka ji ihunta. Kafin su karasa dakin kaninta Walid ya rigasu. Kokarin dagata suka tarar yana yi ga jini ya jika zanin gadon. Kuka Raliya ta saka ta soma jijjiga Izzatu sai dai ta suma bata san waye a kanta ba. Dad dinsu yayi saurin dauko makullin mota shi kuma Walid ya ciccibota ya sakata a ciki. Hankalinsu a tashe suka tafi asibiti mafi kusa dasu. Raliya sai kuka takeyi tana kiran sunan Izzatu.

A yanayin da likitoci suka ganta theatre akayi gaggawar kaita ana kokarin ceto ranta. Sai kai kawo suke yi a kofar theatre din har gari ya karasa wayewa. Suna kallo nurse zata fito da gudu wata ta shiga. Tsahon lokacin nan babu irin tunanin da iyayenta basuyi ba. Suna nan tsaye jugum jugum Raliya tace idan ka taho da waya ya kamata a sanar da Hamza. Alh Sunusi yace haba Raliya, ya za'ayi mu kirashi a wannan lokacin bayan muma bamu san aininhin abinda ke damunta ba. Ko kin sani? Cike da damuwa Raliya tace ni bansani ba kuma banga wata alama ta rashin lafiya a tare da ita ba. Likitoci biyun dake kan Izzatu ne suka fito a tare bayan fiye da awa daya da sukayi a ciki. Daya daga cikinsu ya dubi Alh Sunusi yace ku biyo ni office. Raliya tace Doctor kawai ka fada mana a nan idan ta cika. Yayi murmushi noooo Madam, ki kwantar da hankalinki. She is stable now.

Duk su biyun sun tsirawa liktan ido suna jiran bayaninsa. Glass din idonsa ya cire ya goge fuskarsa da hankice....duk motsinsa Raliya kamar ana tsikarinta take ji. So take kawai tasan abinda ya sami Izzatu. Likita yace "yallabai menene matsayin patient dinnan a wurin ka?"

" 'Yata ce" Alh Sunusi ya amsa masa.

"Tana da aure ko budurwa ce?"

Raliya ta kagu ya fadi abinda ke faruwa tace "matar aure ce harda 'ya'ya uku. Mijinta yana Kano".

Sai da yayi 'yan rubuce rubuce sannan yace "patient dinnan tasha maganin zubar da ciki overdose. A ka'idar wanda tasha ma guda daya ake sha amma da kyar ta iya fada mana hudu tasha a lokaci daya".

Cikin rashin fahimta Alh Sunusi yake tambayar Raliya dama Izzatu nada ciki tace itama bata da labari.

Likita yace to a gaskiya ba karamin ganganci tayi da rayuwarta ba domin da kyar muka iya ceto rayuwarta da ta abinda ke cikinta. Tunda yana da lafiya bamu ga dalilin zubar dashi ba. Sai dai ya zama dole a kula da ita sosai har ta haihu domin mahaifar a yanzu bata da kwari. A takaice ma dai sai dai ayi mata aiki a cire baby din idan ya cika watannin haihuwa sannan ita kanta mahaifar dole a cireta. Dalilin haka yasa muka tabbatar munyi kokari wurin ceto abinda ke cikin."

Raliya ta dora hannu a ka tana kuka tunda taji yace za'a cire mahaifa. Alh Sunusi rai duk babu dadi yace muna iya ganinta? Doctor yace su bari ta huta domin ta wahala.
Chapter 40 · 0% Book details